'Kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kaiwa naira miliyan biyar'
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza
Indiya ta gayyaci Tarayyar Afrika ta zama mamba a G20
Asalin hoton, Getty Images
Yayin buɗe taro Firaiministan Indiya Modi ya gayyaci Tarayyar Afrika ta zama mamba ta dindindin a ƙungiyar G20.
Mambobi da dama sun amince da sanya AU a wannan ƙungiya tun gabanin taron.
Wannan wani mataki da Modi ya ɗauka wani ƙoƙari ne na mayar da Indiya muryar kudancin duniya.
'Za a gudanar da zaɓe a Gabon nan da shekara biyu'
Asalin hoton, Getty Images
Sabon Firai Ministan Gabon, Raymond Ndong Sima, ya shaida wa BBC ya na fatan za a gudanar da zaɓe nan da shekaru biyu masu zuwa a ƙasar.
Sojojin da suka hamɓarar da mulkin shugaba Ali Bongo sun yi alƙawarin gudanar da sahihin zabe, amma ba su ƙayyade lokaci ba.
Mista Sima ya ƙara da cewa nan da kwanaki masu zuwa ne za a sanar da takamaimai lokacin da za a gudanar da zaben, bayan kammala taron da za su yi da jam'iyyun siyasar Gabon.
Ya kara da cewa za a ɗauki lokacin kafin karfin fada ajin iyalan Bongo ya kau a Gabon, amma ya ce za a gurfanar da Mista Bongo gaban shari'a wanda a yanzu sojin da sukai juyin mulkin suka sake shi tare da ba shi damar barin ƙasar idan ya na muradi.
Yadda shugabannin duniya suka isa taron G20
Tun gabanin fara taron shugabanni daban-daban na duniya suka fara isa.
Shugabannin Amurka da Burtaniya da Canada da Masar duka sun isa taron.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Shugaban Amurka Joe Biden tare da Modi
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak a taron G20 tare da Modi na Indiya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Shugaban Majalsar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres tare da Modi jim kaɗan bayan isar sa wajen taron G20.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Hoton farko na Yarima bin Salman na Saudiyya lokacin da ya isa India. Bayan taron Yariman zai yi wata ziyara a India ta musamman da zai fara a ranar 11 ga watan Satumba
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Modi na gaisawa da Ministan harkokin wajen China Wang Yi
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Firaiministan Canada Justin Trudeau tare da Modi a taron G20
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Modi lokacin da ya ke yi wa Firaiministan Bangladesh Sheikh Hasina Wazed barka da zuwa
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Modi lokacin da ya ke yi wa sugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi barka da zuwa
An fara taron G20 a India
Asalin hoton, MEA/X
A yau ake buɗe taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G20, wanda a bana kasar Indiya ke karɓar baƙunci, sai dai biyu daga cikin ƙasashen da ke sahun gaba wato Rasha da China ba su halarci taron ba.
Tuni shugabannin ƙasashen suka fara taruwa a sabon ɗakin taron da aka gina a birnin Delhi.
Shugabannin za su tattauna kan batutuwa masu muhimmanci ciki har da matsalar sauyin yanayi, da matsalolin da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta, sai dai ana sa ran yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine ya mamaye taron.
Da alama akwai kyakkyawan fata, ganin yawancin shugabannin kasashen sun amince da buƙatar Firai Ministan Narendra Modina ta gayyatar ƙungiyar Tarayyar Afirka domin shiga cikinsu su tashi daga G20 zuwa G21.
Barka da safiya
Ma su bibiyar wannan shafin barka da hantsi.
Buhari Muhammad Fagge ke fatan an tashi kalau.
Ni zan kasance da ku a tsawon wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.