'Yan bindiga sun kashe mutum biyar a masallaci a Kaduna

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Gane Mini Hanya: 'Ba ƙasashen Yamma ne ke bai wa Najeriya umarni ba kan Nijar'

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Gane Mini Hanya:

    Filin Gane Mini Hanya na wannnan makon ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tuggar.

    Ministan ya bayyana shirin da suke yi na dawo da dimokuraɗiyya a Nijar maƙabciya, yana mai musanta batun cewa ƙasashen Yamma ne ke bai wa Najeriya umarni a yunƙurin.

  2. Tinubu zai nemi zuba jari daga shugabannin ƙasashe huɗu a taron G20

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, APC

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gana da shugabannin wasu ƙasashe a gefen taron ƙungiyar G20 ta ƙasashe 20 mafiya girman tattalin arziƙi da za a yi a Indiya a watan Satumba.

    Duk da cewa Najeriya ba ta cikin G20, maƙasudin tafiyar shi ne jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen zuwa Najeriya, wadda ita ce mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.

    Tinubu zai gana da shugabannin Brazil da Indiya da Koriya ta Kudu da Jamus a gefen taron da za a fara daga 9 zuwa 10 na watan Satumba.

    Kazalika, Tinubu zai gana da wasu manyan 'yan kasuwa na Indiya.

    Kamfanin sadarwa na Airtel, wanda kamfanin Indiya Bharti Airtel ya mallaka, shi ne na uku mafi girma a Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na Reuters.

    Ministan kuɗin ƙasar ya faɗa a ranar Litinin cewa gwamnatin Bola Tinubu na neman hanyoyin ƙarfafa zuba jari fiye da dogaro kan bashi don samun damar ƙirƙirar ayyukan yi ga miliyoyin matasa.

  3. Juyin mulkin da muka yi na taƙaitaccen lokaci ne - Sojin Gabon

    Janar Brice Oligwe Ngwema

    Asalin hoton, Reuters

    Jagoran juyin mulki a Gabon, Janar Brice Oligwe Ngwema, ya ce za su mayar da hankali wajen ƙarfafa mulkin dimukuradiyya a ma'aikatun kasar.

    Ngwema ya ce za a sake gyara su da kyakkyawan tsari da inganci, sannan juyin mulkin da suka yi wa gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba na wucin-gadi ne.

    Tun da fari a jiya Juma'a, 'yan adawa a Gabon sun zargi sojoji da ƙin nuna alamar shirin miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.

    Mai magana da yawun haɗakar jam'iyyun, Alexandra Pangha, ya ce "rashin ta-ido ne a ce an rantsar da Janar Ngwema a matsayin shugaban Gabon a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda take-taken sojojin ke nuna wa".

    Har yanzu sojojin na tsare da Shugaba Ali Bongo da iyalansa a fadar gwamnati, kuma babu wani karin bayani kan halin da yake ciki ko matakin da za su ɗauka a kansa.

  4. Assalamu Alaikum

    Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sassan duniya.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan hantsi na Asabar.

    Da fatan an fara hutun ƙarshen mako lafiya. Ku biyo ni.