Ba mu amince sojojin Nijar su ci gaba da mulki har shekara uku ba - Ecowas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Yankunan da ake tafka yaƙi a Sudan sun ƙara yawa

    Khartoum

    Asalin hoton, Reuters

    Wuraren da dakarun sojan Sudan da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) ke fafatawa sun ƙaru a garuruwan Yammacin Kordofan, da Khartoum, da kuma Darfur.

    Sahaidu sun faɗa wa BBC Arabic cewa an ƙara jibge dakarun sojan Sudan a birnin Al-Fula na jihar ta Kordofan, suna masu cewa ƙazamar fafatawar da ɓangarorin suka yi ta lalata sassan birnin da yawa.

    A Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, shaidun sun ce faɗa ya ɗan lafa, amma ana ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe.

    Mazauna yankin sun ce arangamar da aka shafe kwana uku ana yi ta ɗaiɗaita yankin, yayin da ake ci gaba da kashe fararen hula.

    A gefe guda kuma, jami'an sojan Sudan sun tabbatar da cewa sun yi ruwan wuta kan wasu sansanonin RSF a kudancin birnin Khartoum.

    Wata majiya ta ce hare-haren sun fi ƙamari a unguwannin Jabra, da Abu Adam, da kuma Kalakia.

  2. Wutar daji: An umarci mutum 30,000 su fice daga British Colombia na Kanada

    British Colombia

    Asalin hoton, Reuters

    Kusan mutum 30,000 aka umarta su bar gidajensu a yammacin lardin British Colombia da ke kasar Kanada a yayin da gagarumar wutar daji ke ci gaba da mamaye lardin.

    Jami'ai sun ce akwai wurare da dama da wutar ke barazanar kai wa gare su.

    Wakilin BBC ya ce mahukunta sun ce wutar dajin na ɓarna cikin gaggawa, inda ta mamaye yankuna da dama ciki har da Kelowna, wani mashahurin wajen yawon bude idanu.

    Birnin Yellowknife da ke arewa maso yammacin kasar ma ya zamo kufai bayan an kwashe mazaunansa.

  3. 'Yan bindiga sun kashe mutum 21 a Mali

    'Yan bindiga

    Asalin hoton, AFP

    Wani hari da 'yan bindiga suka kai a tsakiyar yankin Mopti da ke Mali ya yi sanadin mutuwar fararen hula aƙalla 21 da kuma raunata wasu da dama.

    Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wasu 'yan bindiga ne suka afka kauyen Yarou, sannan suka bude wuta.

    Babu wata kungiya da kawo yanzu ta ɗauki alhakin harin.

    Rashin tsaro da tashe-tashen hankali sun addabi arewaci da kuma tsakiyar Mali, inda ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Alƙa'ida da ISIS ke yawan kai hare-hare.

  4. Assalamu Alaikum

    Barkanmmu da sake saduwa a shafin kabarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku kasance da ni Umar Mikail don samun rahotannin da suka shafi rayuwarku.