Ba mu amince sojojin Nijar su ci gaba da mulki har shekara uku ba - Ecowas
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu binmu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshe labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Abdullahi Dello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Kotunan ƙorafin zaɓe: Kungiyoyin fararen hula na nuna damuwa kan zargin bai wa alƙalai cin hanci
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare fararen hula da ke sanya ido kan ci gaban dimokaraɗiya a Najeriya ta 'Transition Monitoring Group'(TMG)tan bayyana damuwarta kan yadda wasu da ta bayyana da 'marasa kishin ƙasa' ke son amfani da kuɗi don kawo tarnaƙi ga shari’un da ke gaban kotunan sauraron ƙararakin zaɓe a wasu daga cikin jihohin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce faruwar wannan al'amari abin takaici ne, adaidai lokacin da dimokradiyya ke fuskantar barazana a yankin yammacin Afirka, sakamakon ƙaruwar cin hanci da rashawa da wasu 'yan siyasa ke aiwatarwa.
Kungiyar ta kuma ƙara da cewa akwai buƙatar mayar da hankali domin tabbatar da cewa an kammala gudanar da shari'o'in ƙorafe-ƙorafen zaɓe cikin gaskiya da adalci.
A makon da ya gabata ne, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen 'yan majalisun tarayya da ta jihar Kano, Mai shari'a Flora Ngozi Azinge, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.
Ƙungiyar ta TMG ta ce iƙirarin Mai shari'a Azinge babbar damuwa ce ga duk wani mai kishin ƙasa.
Sanna kuma ƙungiyar ta yaba wa alkaliyar dangane da fitowa fili da ta yi tare da bayyana hakan.
Rahotanni dai sun ambato Mai shari'a Flora Azinge na cewa karo na biyu kenan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.
Zargin na babbar alƙaliyar, na nuna tsananin rufewar idon 'yan siyasa, ta yadda wasu ke ƙoƙarin sayen nasarar da suka kasa samu ta halastacciyar hanya daga jama'ar da za su mulka.
Klopp na fatan a soke jan katin da aka bai wa Mac Allister
An sake yin zanga-zangar goyon bayan mulkin soji a Nijar
Asalin hoton, Getty Images
Daruruwan magoya bayan juyin mulkin Nijar ne suka taru a birnin Yamai ranar Lahadi da yamma, domin sake jaddada goyon bayansu ga sojojin ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ƙasar Janar Abdurahmane Tchiani ya gargaɗi ƙungiyar Ecowas kan shirin da take na afka wa ƙasar.
A ranar Asabar ne shugaban ƙasar ya bayyana cewa suna shirin miƙa mulki nan da shekara uku masu zuwa.
Asalin hoton, AFP
Masu zanga-zangar galibinsu matasa ɗauke da tutar Rasha da ta Nijar, sun nuna goyon bayansu ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula, ta Mohamed Bazoum cikin watan da ya gabata.
A ranar Asabar ne tawagar - wakilan Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar - ta ziyarci hamɓararren shugaban ƙasar a inda ake tsare da shi tare da iyalinsa da kuma ɗansa, a fadar shugaban ƙasar tun bayan hamɓarar da shi.
Haɗakar ƙabilun Nijar mazauna Ghana sun gudanar da taron addu'o'i ga ƙasarsu
Hadakar Kabilun Nijar a Ghana sun gudanar da taron shekara-shekara na hawan Daba da suka saba gudanarwa a kowace shekara a ƙasar.
Bayanan hoto, An gabatar da jawabai tare da yi wa ƙasarsu fatan alkairi game da halin da take ciki
Bayanan hoto, Jagororin ƙalibun Nijar mazauna Ghana sun halarci bikin na bana
Bayanan hoto, Sun yi addu'ar Allah ya kawo wa ƙasarsu zaman lafiya mai ɗorewa
Bayanan hoto, Nijar ta faɗa cikin rikici da kungiyar Ecowas ne tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli
Bayanan hoto, A wannan shekarar maimaikon hawan Daba an gudanar da addu'o'i don neman Allah ya kawo zaman lafiya a ƙasar Nijar
Bayanan hoto, Ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar afka wa Nijar da yaƙi matuƙar sojojin ba su mayar da Bazoum kan mulki ba.
Bayanan hoto, Cikin makon da ya gabata ne manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas suka ce sun saka ranar kai wa Nijar hari, idan tattaunawar lalama ta ci-tura
Messi ya daukar wa Inter Miami kofin farko a tarihi
Ba mu amince sojojin Nijar su ci gaba da mulki har shekara uku ba - Ecowas
Asalin hoton, ECOWAS/FACEBOOK
Kungiyar Ecowas ta ce ba za ta amince da maganar da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi ba, cewa zai mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyayya cikin shekara uku masu zuwa.
Cikin wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya fitar da maraicen ranar Asabar ya ce zai miƙa mulki hannun farar hula cikin shekara uku.
A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan harkokin siyasa da tsaro da tabbatar zaman lafiya na Ecowas, Abdel-Fatau Musa, ya ce yana ganin sanarwar da Janar Tchiani ya fitar dabara ce ta buƙatar tattaunawa.
Ya ƙara da cewa ya kamata a ce jagororin sojin Nijar sun mayar da hankali wajen yaƙar 'yan ta'adda, maimakon harkokin mulkin ƙasar.
Ƙungiyar dai na buƙatar sojojin su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba.
Ecowas ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
To sai dai cikin sanarwar da ya fitar, ranar Asabar, Janar Tchiani ya yi gargaɗin cewar amfani da ƙarfin soji ka iya wargaza zaman lafiyar ilahirin yankin yammacin Afirka.
Amfanin Mongoro ga lafiyar ɗan'adam
Mongoro nau'in kayan marmari ne da ke ƙunshe da tarin abubuwan amfani ga lafiyar jikin ɗan'adam.
Usman Bashir wani likita ne a Najeriya ya kuma yi bayanin cewa mongoro na ƙunshe da sinadaran gin jiki da ƙarin ƙuzari.
Ya shawarci mutane su riƙa ci har ɓawon idan za su mongoro, kasancewar ɓawon da ɗauke da sinadarai masu amfani ciki har da na ƙara lafiyar idanu
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Kotu za ta sake duba zargin lalata da ƙananan yara da ake yi wa Michael Jackson
NDLEA ta kama dala miliyan 20 da take zargin na boge ne
Asalin hoton, NDLEA
Jami'an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA), sun kama dala miliyan 20 da take zargin na boge ne a Abuja.
Wata sanarwa daga hukumar a yau Lahadi ta ce jami'n sun kama kuɗin ne ranar Juma'a yayin aikin duba ababen hawa a kan hanyar Abaji zuwa Lokoja bayan ta taso daga jihar Legas.
Hukumar ta ce an kama direban motar, Onyebuchi Nlededin, mai shekara 53.
Kazalika, an kama tarin ƙwayoyi ranar Alhamis yayin wani samame a yankunan Kabusa da Dei Dei da Tora-Bora da ke ciki da kuma kewayen birnin na Abuja, a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.
Rasha ta ce harin Ukraine ya raunata mutum biyar
Asalin hoton, Reuters
Rasha ta ce wani hari da Ukraine ta kai da jirage marasa matuƙa kan tashar jirgin ƙasa a yankin Kursk ya raunata mutum biyar.
An ce wani jirgin ya faɗo a yankin Rostov - wanda shi ma yake da iyaka da Ukraine ɗin - amma babu wanda ya jikkata.
Rasha ta kuma ce ta kakkaɓo wani jirgin da ya nufi birnin Moscow, inda ya faɗo a wurin da babu kowa.
Wani bidiyo da BBC ta tantance ya nuna yadda aka lalata gilasa na tagogi da kuma wuta tana ci a tashar ta Kursk mai nisan kilomita 150 daga iyakar Ukraine.
A kwanan nan ana yawan zargin kai hare-hare da jiragen cikin Rasha.
Duk da cewa Ukraine ba ta ɗaukar alhakin kai hare-haren, Shugaba Volodymyr Zelensky ya taɓa cewa "hari kan Rasha abu ne da ya zama dole kuma wanda ya dace".
Sifaniya na murnar lashe Kofin Duniya
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
An karya bajintar Ingila ta wasa 29
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Lamarin babu daɗi amma an yi ƙoƙari.
Rashin nasarar da Ingila ta yi a wannan wasa, shi ne karo na farko cikin wasa 29 da ta buga a dukkan gasa.
Rabon da a ci tawagar tun watan Maris na 2020 a wasa tsakaninta da Sifaniya - ita ɗin dai - a gasar SheBeleives.
Ta yi nasara cikin wasa 25, ta yi canjaras 4.
Kafin Sifaniya ta lashe Kofin Duniya...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya ba ta lashe gasar Kofin Duniya a banza ba.
Kafin wannan gasar, wasa ɗaya kacal ta taɓa ci a Kofin Duniya.
Yanzu ta zama ƙasa ta biyar da ta ci kofin bayan Amurka (4), da Jamus (2), da Norway (1), da kuma Japan (1).
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, 'Yan matan Sifaniya sun lashe Kofin Duniya
Asalin hoton, PA Media
Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Sifaniya ta lashe gasar Kofin Duniya bayan doke Ingila a wasan ƙarshe na gasar ta 2023 da aka buga a Ausraliya.
Carmona ce ta ci ƙwallo ɗaya tilo a minti na 29 bayan ta ɗaɗa ta daga ɓangaren hagu da ƙafarta ta hagu.
Wannan ne karon farko da Sifaniya ta lashe gasar.
Fafaroma Francis ya yi kiran a sasanta rikicin Nijar cikin lumana
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Fafaroma Francis ya yi kiran a sasanta rikicin siyasar Nijar ta laluma biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
"Ina lura cikin damuwa da abin da ke faruwa a Nijar," a cewarsa yayin da yake jawabi yayin ibada a Dandalin St Peter's a yau Lahadi.
"Na bi sawun bishop-bishop wajen neman zaman lafiya a ƙasar da kuma yankin Sahel.
"Ina taya ƙasashen duniya da addu'a a yunƙurinsu na lalubo bakin tsaren cikin kwanciyar hankali don zaman lafiyar kowa da kowa."
Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi barazanar yin amfani da ƙarfin soja wajen tilasta wa sojojin mulkin mayar da mulki ga farar hula.
Shugaban Gambiya ya hana jami'an gwamnati tafiye-tafiye don rage kashe kuɗi
Shugaban Gambiya Adama Barrow ya dakatar da kansa da dukkan jami'an gwamnatinsa yin balaguro zuwa ƙasashen waje don rage kashe kudin gwamnati.
A cewar mai magana da yawunsa, Shugaba Barrow "ya saka hannu kan umarnin shugaban ƙasa na dakatar da shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa, ministoci, manyan jami'an gwamnati, da ma'aikata daga tafiye-tafiye a shekarar kasafi ta bana".
Sai dai kamfanin labarai na AFP ya ruwaito Mista Ebrima Sankareh na cewa ganawar da ta zama dole a ƙasashen waje kuma wadda ba gwamnati ce za ta ɗauki nauyinta ba, babu laifi.
Gambiya da ke da mutum ƙasa da miliyan biyu, ita ce ta 174 cikin ƙasashe 191 da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bayyana a matsayin masu arziki.
Sakamakon kuɗin shiga da ke raguwa a ƙasar da kuma maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a kan tallafin man fetur, da kuma na takin zamani da hatsi, kasafin kuɗin ƙasar ya samu giɓi a shekarar da ta gabata.
Labarai da dumi-dumi, Kofin Duniya na Mata: Spain 1-0 England
Spain ta zira ƙwallo a ragar England.
Carmona ce ta ci ƙwallon bayan ɗaɗa ta daga ɓangaren hagu da ƙafarta ta hagu.
Me ya sa ake yawan juyin mulki a ƙasashe renon Faransa?
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku:
Filin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi biyu kan rikicin siyasar Nijar.
Tambayar farko ta nemi tarihin shugaban mulkin soja na Nijar ɗin Janar Abdourahmane Tchiani.
Ta biyun kuma ta nemi sanin dalilin da ya sa ake yawan juyin yin mulki a ƙasashe renon Faransa.
Ƙungiyar manoma ta ƙasa a Najeriya, AFAAN, ta bayyana jin daɗi da goyon bayanta kan matakin gwamnatin tarayya na raba wa gwamnatocin jihohi buhunan kayan abinci da na noma.
A watan da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a raba wa jihohin buhunan shinkafa da masara 100,000, da takin zamani 100,000 a matsayin tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin mai.
Sai dai mai magana da yawun kungiyar manoman ta Najeriya, Muhammad Magaji, ya ce suna fargabar hakan ka iya haifar da ƙaranci da tsadar abinci a kasuwa.
A cewarsa, a yanzu babu wadataccen abincin a hannun manoma. "Idan gwamnati ta saye wanda ya rage a kasuwa hakan zai kawo ƙarancin abincin wanda zai sa ya yi tsada."
Latsa hoton ƙasa ku saurari hira da Muhammad Magaji:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari hira da Muhammad Magaji