Wutar daji: Hukumomi a Kanada sun umarci mazauna Kelwona su gudu

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da Kanada ke ci gaba da fuskantar wutar daji mafi muni a duniya, an ƙaddamar da dokar ta-ɓaci a birnin Kelwona da ke kudancin British Colombia.
Birnin mai mutum 150,000 na fuskantar barazanar gobara daga ɓangaren yammaci mai makwabtaka, wanda ke cikin barazanar wutar tun kwana biyu da suka wuce.
Wakilin BBC ya ce mahukunta sun umarci kowa ya bar inda yake saboda irin haɗarin da wutar ke da shi wadda ake gani za ta iya kai wa ga birnin cikin sa'oi.
Iska mai karfi da ke kadawa na ƙara rura wutar.
Wani jami'in kashe gobara ya ce yadda suke kashe wutar kamar suna kashe wutar da ta yi shekara 100 tana ci.