NNPCL zai karɓi rancen dala biliyan uku cikin gaggawa

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Adadin mutanen da suka mutu a gobarar dajin Hawaii ya kai 106

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Adadin wadanda suka mutu sanadin mummunar gobarar daji a jihar Hawaii, ya kai 106 inda kusan mutum 1,300 suka ɓata ba a gan su ba.

    Jami’ai sun su ce, sun gano wadanda gobarar dajin da ta mamaye tsibirin Maui a makon jiya, ta fara shafa inda aka bayyana sunayen mutanen biyu na farko da suka mutu sakamakon gobarar, Robert Dyckman, mai shekaru 74, da Buddy Jantoc, mai shekaru 79, dukkansu daga garin Lahaina.

    Gwamnan Hawaii, Josh Green ya ce bisa dukkan alamu za a iya kwashe kwanaki da yawa kafin hukumomi su kai ga tantance adadin wadanda suka mutu sanadin gobarar.

    Ya kuma ce hukumomi sun sake gano gawawwakin mutum uku, kuma za a sanar da danginsu nan ba da dadewa ba.

    • Wutar daji ta ƙone wani gari ƙurmus a Amurka
    • Jiya da yau: Bala'in gobarar dajin da ke addabar duniya
  2. Gwamnatin tarayya za ta sake gurfanar da Emefiele a gaban kotu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake gurfanar da gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele da abokan ƙawancensa da aka dakatar da su, a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis bisa zargin almundahanar kuɗi har naira biliyan 6.9.

    Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa za a gurfanar Emefiele ne tare da wata ma’aikaciyar CBN, Sa’adatu Yaro da kamfaninta mai suna 'April1616 Investment Limited' a kan laifuka guda 20 da suka hadar da damfara, da haɗin baki wajen aikata laifi da kuma bayar da cin hanci da rashawa ga abokan huldarsa.

    Ba a ji wani bahasi daga jami'an da ake zargin ba, kan sabbin tuhume-tuhumen da ake yi musu.

    Emefiele wanda ke tsare tun lokacin da aka dakatar da shi daga aiki a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, an zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa ga Yaro.

    Laifin ya saba wa sashe 19 na dokokin cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi doka ta 2000.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
    • DSS ta gurfanar da Emefile a kotu
  3. 'Yan sandan Zimbabwe sun kama 'yan jam'iyyar adawa 40

    ...

    Asalin hoton, @advocatemahere

    Bayanan hoto, ...

    'Yan sanda a Zimbabwe sun kame wasu 'yan jam'iyyar adawa ta CCC 40 a lokacin wani gangamin yakin neman zabe da suke gudanarwa, mako guda gabanin babban zaben kasar da ke tafe.

    An tsare su ne a unguwar Glenview da ke Harare, babban birnin kasar a ranar Talata.

    Kakakin jam'iyyar, Fadzayi Mahere, ya ce Gladmore Hakata, dan takarar majalisar wakilai na Glen view South, yana cikin wadanda aka kama.

    Sanarwar da 'yan sanda suka fitar a shafukan sada zumunta ta ce jam'iyyar CCC ta gudanar da wasu abubuwa da ba ta ambata a sanarwar gangamin da ta aike a 'yan sandan kafin gudanar da shi.

    Sun gudanar da jerin gwanon motocin, tare da hana ababen hawa da kuma rera taken jam’iyyar a kan tituna, lamarin da ya sa ‘yan sandan mayar da martani bayan wani mazaunin garin ya kai rahoton lamarin, in ji ‘yan sandan.

    A watan da ya gabata ne 'yan adawar kasar suka yi kira ga hukumar zaben Zimbabwe ta dauki mataki kan yadda ake amfani da 'yan sanda wajen dakile tarukansu.

    Jam'iyyar CCC ta ce 'yan sanda sun haramta tarukanta da dama tun ranar 9 ga watan Yuli.

    Shugaba Emmerson Mnangagwa da shugaban jam'iyyar CCC Nelson Chamisa ne manyan 'yan takara na gaba-gaba a zaben.

    • Yadda kulle-kulle da kashe-kashen siyasa suke ci gaba da barazana ga zabukan Zimbabwe
    • Zimbabwe za ta kirkiro dokar hukunta 'marasa kishin ƙasa'
  4. An samu arangama tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Libya

    a

    Asalin hoton, Reuters

    Majiyar likitoci a Libya ta rawaito cewa an samu arangama tsakanin wasu manyan kungiyoyin masu ɗauke da makamai a birnin Tripoli da ba sa ga-maciji da juna, inda akalla mutum 27 suka mutu, tare da jikkata sama da 100.

    Rikicin ya ɓarke tsakaninsu a daren Laraba, bayan jami'an tsaro sun yi awon gaba da kwamandan ɗaya daga cikin ƙungiyoyi, ko da ya ke an sake shi a jiya Talata.

    Barkewar sabon rikicin ya sake ta da zaune-tsaye a Tripoli babban birnin Libya, bayan watannin da aka ɗauka cikin kwanciyar hankali.

    A shekarar 2020 aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ,amma hakan ba ta dore ba.

    • An sace makamashin uranium da ake haɗa makamin nukiliya da shi a Libya – MDD
    • Amurka ta kama ɗan Libya da ake zargi da tarwatsa jirgi a Lockerbie
  5. Google zai horas da mata da matasan Najeriya 20,000 fasahohin Intanet

    e

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Google ya sanar da shirin bai wa mata da matasan Najeriya 20,000 horo don ƙwarewa a fasahohin dijital iri daban-daban.

    Matakin wani yunƙuri ne na tallafa wa aniyar gwamnatin ƙasar wajen samar da ayyukan yi miliyan ɗaya a fannonin fasahohin dijital na zamani.

    Kamfanin na Amurka ya kuma ce zai ba da tallafin dala miliyan ɗaya ga Najeriyar.

    Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar da daraktan Google a Afirka ta Yamma Olumide Balogun da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima a Abuja.

    Kashim Shettima ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirya tallafa wa matasa domin su baje kolin fasaharsu domin ci gaban wannan fanni a kasar.

    A wani jawabin da shugaban kasar ya gabatar wa 'yan Najeriya mako biyu da ya wuce, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa matasa miliyan ɗaya ayyukan yi musamman a ɓangaren fasahohin zamani.

    • Zaman kashe wando tsakanin matasan China ya kai matuƙa
    • Me ya sa matasan Koriya ba sa son shiga cikin jama'a?
  6. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Aisha Babangida da Abdullahi Bello

    Ku biyo mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da sauran sassan duniya.