Laberiya ta miƙa wa Saliyo tsohon shugaban ƴan sandanta

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Laberiya sun kama tsohon shugaban ƴan sanda Saliyo da ake zargi da shirya kifar da gwamnatin shugaba Julius Maada Bio, tare da miƙa shi ga ƙasar.
Ministan yaɗa labaran Laberiya, Ledgerhood Rennie ya ce an kama Mohammed Y Toure ne “bayan buƙatar hakan da hukumomin Saliyo suka gabatar, inda suke zargin sa da yunƙurin juyin mulki.”
Ya ce Laberiya ta yanke shawarar miƙa shi ga Saliyo ne bayan kammala bincike a kan batun.
Ya kuma yi bayanin cewa sun samu tabbacin cewa za a kare ƴancinsa da duk wani haƙƙi da ya kamata a lokacin sauraron ƙarar a Saliyo.
Tun a shekarar da ta gabata tsohon jami'in ƴan sandan yake zaune a Laberiya.
Mista Toure na daga cikin ƴan sandan da Saliyo ta kora daga aiki a 2020, ta kuma tilasta wa wasu da dama yin murabus.







