Bankwana
Masu bibiyarmu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen rahotannin na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu sababbi. Rabiatu Kabir Runka ce ke fatan mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Rabiatu Kabir Runka
Masu bibiyarmu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen rahotannin na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu sababbi. Rabiatu Kabir Runka ce ke fatan mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu maza biyar, bayan da kotu ta same su da laifin yi wa wata mata fyade na gungu a yankin arewa maso yammacin kasar.
A bara ne aka kama su kwana huɗu da aikata laifin a birnin Marand. A makon da ya gabata ma hukumomin Iran din sun rataye wasu maza uku, bayan da su ma aka same su da laifin yi wa mata fyade.
Mutanen suna yi wa mata allurar hana jin zafi, bayan sun yaudare su zuwa wani asibitin mai-da-tsohuwa yarinya, ko gyaran jiki na bogi.
Ƙungiyar kare hakkin dan'Adam ta duniya, Amnesty International, ta ce, zuwa yanzu Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan mutum akalla 282, a wannan shekarar kadai, fiye da kowa ce ƙasa a duniya bayan China.

Rahotanni daga yankin Amhara na Habasha na cewa dakarun tarayya sun kori mayaƙan sa-kai daga manyan garuruwa biyu na yankin, a babbar galabar da suka samu a fagen daga tun bayan da faɗa ya ɓarke a makon da ya gabata.
Gwamnatin ta ce an ƴanto Gondar da Lalibela daga abin da ta kira barazanar 'yan baranda, wato mayaƙan sa-kai na ƙungiyar Fano.
Rikicin shi ne babban kalubalen tsaro na Habasha tun, bayan da aka kawo ƙarshen yaƙin basasa na shekara biyu a yankin Tigray.
Zaman tankiya na ta ƙaruwa tun watan Afirilu, lokacin da gwamnati ta ce za ta rushe dukkanin dakarun yanki a faɗin ƙasar, abin da ya harzuƙa ƴan kishin ƙasa na Amhara, waɗanda suka ce matakin zai rage ƙarfin yankinsu.

Wutar daji da mahaukaciyar guguwa sun tilasta kwashe jama'a a sassan jihar Hawaii ta Amurka, inda wasu mazauna suka riƙa faɗawa teku domin tsira daga wutar.
Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun bayyana yanayi a tsibirin Mawe (Maui), wanda shi ne na biyu mafi girma kuma na uku mafi yawan jama'a, a jihar ta Amurka, da "tashin duniya".
Wakiliyar BBC ta ce mmasu aikin agajin gaggawa a Maui na cewa asibitoci sun cika da mutanen da suka ji rauni.'
Garin Lahaina na daga cikin wadanda suka fi gamuwa da ɓarna, inda gomman gidaje da harkokin kasuwanci suka lalace.

Asalin hoton, Reuters
Faransa ta musanta zargin karya dokar sararin samaniya da sojojin mulki a Nijar suka zarge ta da yi.
Sojin Nijar sun zargi Faransa da karya dokar ƙasar ta rufe sararin samaniyarta.
Sojojin Nijar sun zargi Faransa da ƙawayen ta da ƙoƙarin kuɓutar da ƴan ta'adda da ke tsare, waɗanda ake zargi da haifar da rashin tsaro tsawon shekaru takwas.
Amadou Abdraman ne ya bayyana zargin cikin wata sanarwa da ya karanta a talabijin, sai dai babu wata shaidar da ya gabatar game da zargin.
Hakan na zuwa ne lokacin da ake zaman ɗar-ɗar kan zaman da ƙungiyar Ecowas za ta yi a gobe Alhamis, inda za ta tattauna matakan da za ta ɗauka nan gaba, ciki har da matakin soji.
Gwamnatin Faransa ta musanta zargin na sojojin Nijar kan kuɓutar da "ƴan ta'adda" da kuma karya dokar keta sararin samaniyarta.
Lamarin na zuwa ne ƴan sa'o'i bayan da wani tsohon jagoran ƴan tawaye ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Yau Laraba ma an kama ɗan jakadiyar Nijar a Faransa, Idrissa Kané, wadda tsohuwar shugabar gidan waya ne na Nijar, inda ake zargin sa da almubazzaranci da dukiyar al'umma.
Majalisar malaman addinin Musulunci a Najeriya ta gana da Shugaba Bola Tinubu a yammacin Laraba, inda suka shaida masa rashin goyon bayansu wajen amfani da ƙrfin soja kan rikcin siyasar Jamhuriyar Nijar.
Sakataren ƙungiyar Jamaatu Nasrul Islam (JNI), Farfesa Khalid Abubakar, ya bayyana cewa sun nemi shugaban ya ci gaba da lalubo hanyoyin sasanta lamarin ta hanyar difilomasiyya maimakon ƙarfin soja.
"Mun faɗa masa cewa ɗaukar matakin soja ba zai warware komai ba, kuma mun faɗa cewa ba mu goyon baya," kamar yadda ya faɗa wa manema labarai bayan ganawar tasu.
"Najeriya da Nijar kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. 'Yan uwa muke, addininmu ɗaya, al'adunmu ɗaya. Dole a bi a hankali don a samu zaman lafiya."
Wata tawagar ta malaman na ci gaba da tattaunawa da Shugaba Tinubu ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Asalin hoton, AFP
A jamhuriyar Nijar rahotanni na cewa dakarun ƙasar da dama ne suka rasa rayukansu ta dalilin wani hari da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba.
Maharan sun afka wa rundunar Garde Nationale ne da ke Bourke Boukey a yankin Dargol da ke jihar Tillabery.
Sai dai wata sanarwa da sojojin ƙasar suka fitar na cewa sojojin Faransa ne suka kai harin, inda suka kuɓutar da wasu da suka kira yan ta'adda 16 tare da kashe mata sojojin da yanzu haka ba su san adadinsu ba.
Majalisar sojojin mulkin ƙasar ta sanar da 'yan ƙasa da na ƙetare cewa "wasu lamurra marasa daɗi, masu kuma munin gaske na kan hanyar faruwa a Nijar ta dalilin halayen sojojin Faransa da waɗanda suka haɗa baki da su bayan sun kai hari kan sojinmu".
"Waɗannan jagororin ƴan ta'adda da aka saki su16, an yi nasarar kama su ne yayin wasu hare-hare uku." in ji sanarwar.
"A ƙoƙarinsu na aiwatar da aniyarsu ta hargitsa Nijar, sojojin Faransa sun tura wani jirgin yaƙin soja samfurin A400M daga N'Djamena na kasar Chadi da safiyar yau [Laraba]".
Latsa hoton da ke ƙasa domin sauraron rahoton Tchima Illa Issoufou

Asalin hoton, EPA
Hukumomin Italiya sun fara gudanar da bincike a kan bayanan waɗanda suka ga yadda ruwa ya ci 'yan ci-rani 41, a tsibirin Sicily da ke Lampedusa.
Mutum 45 ne ciki har da ƙananan yara uku ke cikin jirgin ruwan, wanda ya tashi daga birnin Sfax na ƙasar Tunisiya, ranar Alhamis da ta wuce kafin ya nutse a cikin teku.
Mutum hudu kawai da suka kuɓuta a hatsarin, 'yan kasashen Ivory Coast da Guinea, su ne suka bayar da bayanai ga jami'an tsaron teku na Italiya, bayan ceto su.
Wakiliyar BBC ta ce, ''wadanda suka tsiran sun ce mutum 15 ne kawai suke sanye da rigar-fito." Sun ce wata babbar igiyar ruwa ce ta nutsar da jirgin nasu 'yan sa'o'i da fara tafiyarsu.
Wani jirgin ruwan dakon kaya ne ya fara ceto mutanen, maza uku da mace ɗaya, waɗanda ke cikin 'yan kaɗan masu sanye da rigar-fito.

Asalin hoton, Khalifa Sanusi

Asalin hoton, Khalifa Sanusi

Asalin hoton, Khalifa Sanusi

Asalin hoton, Khalifa Sanusi

Asalin hoton, Facebook/ Sheikh Ibrahim H Musa Albani
Gwamnan Gombe da ke arewacin Najeriya, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ci alwashin zaƙulo mutanen da suka kashe malamin addini Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta ce wasu ɓarayi ne suka kashe malamin ranar Talata da dare yayin da suka shiga gidansa a Tabra da ke birnin Gombe.
"Muna tabbatar wa mazauna Gombe cewa za mu ci gaba da kare dukiya da rayukansu, da kuma zaƙulo waɗanda suka aikata wa malamin wannan mummunan abu," a cewar gwamnan lokacin da ya halarci jana'izarsa a masallacin Bolari.
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta ce maharan sun kashe shehin malamin ne yayin da suka yi yunƙurin yi masa fashi.
Gwamnan ya miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar Gombe da kuma ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Iqamatissunnah (JIBWIS), wanda mamba ne a cikinta.

Asalin hoton, Getty Images
Fitaccen mawaƙin Mali, Salif Keita ya yi murabus daga gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar, wadda ke gudanar da mulki tare da gwamnatin soji.
A wani bidiyo da aka yaɗa, an nuna wani jami'i yana karanta sanarwar ajiye aiki a madadin Keita inda yake cewa ya yi murabus ne saboda dalilai na raɗin kai.
Ya ce "zan ci gaba da zama aboki ga dakarun sojin ƙasarmu,"
Tun a watan Disambar 2020 Salif Keita ke cikin majalisar mulkin Mali ta riƙon ƙwarya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2020, wanda ya kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita.
Sai dai wasu kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce kofar Keita aka yi saboda aikata ba daidai ba.

Asalin hoton, GODSWILL OBOT AKPABIO
Shugaban Majalisar Datawan Najeriya, Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka, inda ya sanar da cewa majalisar ta tura wa mambobinta 'kuɗin more hutu'
A lokacin zaman majalisar na ƙarshe kafin tafiya hutu, Akpabio ya ce “Da zarar an rantsar da Sanata Umahi a matsayin minista, za mu sake tsara shugabancin majalisar.”
Sai ya ce “Domin more hutunmu, Akawun majalisa ya tura ɗan wani abu a asusun ajiyar kowannenmu.”
Bayan ya yi furucin ne ɗaya daga cikin ƴan majalisar ya matsa kusa da shi, don fargar da shi cewa ana nuna zaman nasu kai-tsaye ta talabijin.
Daga nan ne sai Akpabio ya yi saurin warware maganar tasa, inda ya ce “Na janye kalaman da na yi. Ina nufin shugaban majalisa ya tura maku addu'ar fatan shan hutu lafiya da kuma fatan yin tafiya lafiya a dawo lafiya.”
Babu dai tabbacin game da adadin abin da aka tura wa ƴan majalisar, musamman ma yadda albashinsu da kuma sauran kuɗaɗen alawus ɗinsu duk abubuwa ne da babu hakiƙanin bayani a kai.
Jaridar Daily Trust ta wallafa bidiyon a shafin Tuwaita, wanda ke nuna shugaban majalisar yana bayani game da alawus ɗin hutun, da ta ce Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka wajen furtawa a daidai lokacin da 'yan ƙasar ke fama da matsin rayuwa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, CBN
Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emiefele ya nemi wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta hana gwamnati da hukumar DSS ci gaba da tuhumar sa kan mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba.
Ya kuma nemi kotun ta wanke shi daga duka zarge-zargen da hukumar DSS ke yi masa.
Emefiele wanda kotu ta bayar da belin sa a ranar 25 ga watan Yulin 2023, amma har yanzu hukumomi na ci gaba da tsare shi.
Lauyan Emiefele, Joseph Daudu, wanda ya shigar da buƙatar a madadin wanda ake zargi ya nemi mai shari'a Nicholas Oweibo ya tabbatar da belin dakataccen gwamnan babban bankin da kotu ta bayar tun da farko.
Ya yi fatan kotun ta haramta duk wani yunƙuri na ci gaba da gurfanar da Mista Emiefele har sai an yi biyayya ga hukuncin da kotu ta bayar game da belinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Mutum biyar sun mutu, ciki harda wani ɗan Birtaniya mai shekara 40 da kuma ɗan sanda bayan rikicin da ya mamaye yajin aikin direbobin motar haya a birni Cape Town na Afrika ta kudu.
Wannan na zuwa ne bayan shafe mako guda ƙungiyar direbobin motar haya ta Santaco tana yajin aiki a ƙasar.
Direbobin sun shiga yajin aikin ne saboda abin da suka kira 'muzgunawa' daga hukumomin tsaro.
Birtaniya ta gargaɗi ƴan ƙasarta game da shiga Afrika ta Kudu bayan yajin aikin ya fara rikiɗewa zuwa tashin hankali.
Da alama yajin aikin zai ci gaba, bayan gaza cimma matsaya tsakanin Santaco da gwamnati.
Tuni dai Ministar sufurin ƙasar, Sindisiwe Chikunga ta bayar da umarnin fitar da ƙananan motoci don sauƙaƙa wa jama'a wahalar sufuri.