Ministocin Tinubu: Majalisa ta tilasta wa Bosun Tijani neman afuwar 'yan Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Ba ma goyon bayan amfani da ƙarfin soji a Nijar - Sanatocin Arewa

    a

    Asalin hoton, others

    Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta ce ba ta goyon bayan amfani da karfin soji don tilasta wa sojojin Nijar mayar da mulki ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

    Mai magana da yawun ƙungiyar, Sanata Abdurrahman Kawu sumaila ya shaida wa BBC cewa, duk da cewa sanatocin ba su goyi bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi ba, to amma kuma ba su goyi bayan amfani da karfin soji da ƙungiyar Ecowas ke shirin ɗauka kan Nijar din ba.

    ''Muna so ne a yi amfani da hanyoyin diplomasiyya wajen warware wannan matsala, amma ba ƙarfin soji ba'', in Sanata Kawu Sumaila.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu tana la'akari da kusancin Nijar da Arewacin Najeriya

    "'jihohin Najeriya kusan guda bakwai duk sun yi iyaka da Nijar kuma kusan duka waɗannan jihohi, akwai matsalolin tsaro, kama daga na Boko-Haram zuwa na 'yan fashin daji''.

    ''Idan muka bari aka fara yaƙi tsakanin Najeriya da Nijar to masifar da Najeriya za ta shiga, ita kanta Nijar dinma ba za ta shiga wanna masifa ba'', in ji Sanatan da ke wakilar Kano ta Kudu.

    Sanata Kawu Sumaila ya ce hakan zai sa 'yan ta'addan take waɗannan yankuna su ƙara samun dama wajen ci gaba da ɓarnar da suke gudanarwa.

    Ya ƙara da cewa ''kuma yanzu halin da talakawan ƙasar nan ke ciki na matsin rayuwa da sauran matsaloli, idan aka fara yaƙin gaskiya yankunan Najeriya da ke iyaka da Nijar za su sake shiga cikin wata masifa''.

    A ranar Juma'a ne shugaban Najeriya Bola Tinubu, kuma shugaban Ecowas, ya aike wa Majalisar Dattawan Najeriya buƙatar amincewarta domin tura sojojin ƙasar zuwa Jamhuriyar Nijar.

    • An garƙame iyakar Najeriya da Nijar
    • Tasirin yarjejeniyar tsaro da Nijar ta soke da Faransa
  2. An kashe sojojin Indiya uku a yankin Kashmir

    d

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Indiya ta ce aƙalla sojojinta uku aka kashe a wata arangama tsakaninsu da masu auke da makamai a lardin Gulgam da ke yankin Kashmir.

    A cikin wani sakon tuwita da ta wallafa rundunar sojin ƙasar ta ce jami'anta sunkaddamar da auikin neman waanda suka aikata kisan a dajin haland da ake kyautata zaton maɓoya ce ta masu dauke da makamai.

    Masu dauke da makaman sun bude wa sojojin wuta ne a lokacin wata arangama a yankin.

    Yankin Kashmir ya yi ƙaurin suna wajen fuskantar hare-haren masu ɗauke da makamai a Indiya

  3. Amurka za ta ci gaba da bai wa Nijar tallafin Abinci

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurka za ta ci gaba da bayar da taimakon kayan agaji da tallafin abinci ga Jamhuriyar Nijar.

    To sai dai Mista Blinken ya ce Amurka za ta dakatar da wasu tallafin da za su taimaka wa ƙasar da ke yammacin Afirka.

    Ya ce Amurka za ta ci gaba da samar da tsaro don kare jami'anta da ke ƙasar.

    Kalaman Mista Blinken na zuwa ne a daidai lokacin ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka amince da amfani da ƙarfin soji a Nijar ɗin, matuƙar sojojin ba su mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki ba.

    Tuni dai Nijar din ta sanar da janye jakadunta da ke wasu ƙasashen duniya ciki har da Amurka da faransa da kuma Najeriya.

    A ranar Juma'a ne dai Najeriya ta sanar da rufe kan iyakokin ƙasar da Jamhuriyar ta Nijar, bayan katse wutar lantarki da take bai wa ƙasar, a wani mataki na tilasta wa sojojin mayar da Bazoum kan mulki.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Asabar

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki, za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da kuma makwabtan ƙasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.