Sai da safenku
Masu bibiyarmu ƙarshen rahotannin ke nan a yau Asbar. Mu haɗu da ku gobe Lahadi don samun wasu sababbi.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Masu bibiyarmu ƙarshen rahotannin ke nan a yau Asbar. Mu haɗu da ku gobe Lahadi don samun wasu sababbi.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan ya umarci magoya bayansa su gudanar da zanga-zangar lumana bayan yanke masa hukuncin zaman kurkuku.
Mista Khan ya kara da cewa yana fafutuka ne domin magoya bayansa su ji dadi.
An kama shi a ranar Asabar bayan Kotu ta same shi da laifin rashin bayyana kudaden da ya samu ta hanyar sayar da kyautukan da ya samu a lokacin yana kan mulki.
Mista Khan ya musanta zargin da aka yi masa yayin da lauyoyinsa suka ce za su daukaka kara.
Kakakin jam`iyyar PTI, Rauf Hassan, ya ce muna neman babbar kotun Islamabad ta saurari korafinmu gobe (Lahadi), kuma ta dakatar da hukuncin.
Masana shari`a sun bayyana cewar idan alkalai ba su yi watsi ko kuma dakatar da hukuncin ba, za a hana shi fitowa takara nan da shekara biyar.

Asalin hoton, Nigeria Police
Ɗaya daga cikin 'yan daba da rundunar 'yan sandan jihar Kano ke nema ruwa a jallo, Nasiru Abdullahi da aka fi sani da Chile Maidoki, ya miƙa kansa ga rundunar yana "mai tuba da neman afuwa".
Mutumin mazaunin Layin Falwaya, Kurna ya yi saranda ne bayan ya samu labarin ware naira 100,000 a matsayin tukwici ga duk wanda ya nuna ko ya ba da bayanin inda yake, a cewar 'yan sanda.
"Maidoki ya faɗa wa 'yan sanda cewa a maƙabarta yake kwana saboda kada jami'an tsaro su kama shi," in ji wata sanarwa.
"Yanzu yana neman gafarar 'yan sanda da Kanawa, ya tuba kuma a shirye yake ya yi aiki tare da 'yan sanda don ɗorewar zaman lafiya da cigaba a Kano."
Rundunar ta ce tana ci gaba da neman wasu mutum biyu - Abba Burakita da Hantar Daba - kuma za ta ba da tukwicin N100,000 ga duk wanda ya nuna inda suke.

Asalin hoton, Nigerian Senate
Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗage zaman tantance mutanen da Tinubu zai naɗa a matsayin ministoci zuwa ranar Litinin.
'Yan Majalisar sun ɗage zaman ne bayan tantance mutum biyar a yau Asabar. Waɗanda aka tantance su ne:
Tun farko an tsara tantance Festus Keyamo daga jihar Delta da kuma Mariya Bunkure daga Kano, amma sai aka ɗaga.

Asalin hoton, Channels TV
'Yan Majalisar Dattawa a Najeriya sun tilasta wa Dr. Bosun Tijani neman afuwarsu da kuma 'yan Najeriya game da wasu kalamai da ya yi a shafukan zumunta a baya.
Dr. Tijani na cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa, wanda ɗan jihar Ogun ne da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Sanatocin sun karanto irin saƙonnin da ya wallafa a Twitter, cikinsu har da na 2019, inda ya ce "ba na alfahari da riƙe fasfo ɗin Najeriya da kuma Najeriya a matsayinta na ƙasa".
Haka nan, an karanto wani saƙon da ya kira 'yan Majalisar "shashashai" game da yadda suke tantance ministoci.
Mista Tijani bai musanta zarge-zargen ba.
Bayan sanatoci da dama sun yi magana, masu goyon bayansa da masu neman ƙarin bayani, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya umarce shi da ya nemi afuwarsu kafin su ƙyale shi ya tafi.
"Ina neman afuwarku 'yan Majalisa da ma sauran Najeriya kan waɗannan abubuwan da na faɗa," in ji shi. "Ina so ku lura da dalilan da suka sa na yi su, ban yi su don na ɓata sunan wani ba."
Daga nan ya rusuna kuma ya sauka daga kan dandamali.

Asalin hoton, Channels TV
Ɗaya daga cikin mutanen da ake tantancewa don zama minista a Najeriya, Bosun Tijani daga jihar Ogun, na shan tambayoyi game da wani saƙon Twitter da ya taɓa wallafawa a 2019.
Sanata Abdulfataye Buhari ya faɗa wa Bosun cewa a 2019 ya faɗa cikin wani saƙon Twitter cewa "ba ya ganin mutuncin fasfo ɗin Najeriya da kuma Najeriya a matsayinta na ƙasa".
Sannan ya tambaye shi; "Shin har yanzu kana da wannan ra'ayin ko kuwa ka sauya?".
Shi ma Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya umarci Mista Bosun ya bayyana musu ko ɗan Najeriya ne shi har yanzu.
Haka nan, an zarge shi da ɗiga ayar tambaya game da yadda Majalisar take tantance mutanen da za a naɗa a matsayin minista, yana mai cewa "ban san wane irin bincike suke yi ba kan mutanen nan".

Asalin hoton, Senate
Majalisar Dattawan Najeriya ta ci gaba da tantance ministocin da shugaban ƙasar ya aike mata.
A ranar Juma'a ne majalisar ta ɗage zaman tantance ministocin zuwa ranar Asabar, domin samun damar kammala aikin tantance ministocin.
A cikin makon ne dai majalisar ta kammala tantance rukunin farko na sunayen ministocin da shugabna ƙasar ya aike mata.
To sai dai a tsakiyar makon ne, shugaban ƙasar ya sake aike wa majalisar da ƙarin sunayen kutum 19, da wasu ƙarin mutum biyu ranar Juma'a.

Asalin hoton, Reuters
An yanke wa tsohon firaministan Pakisatan Imran Khan hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan yari, kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Kotu ta samu Mista Khan da laifin rashin bayyana kuɗin da ya samu bayan sayar da kyaututtukan da aka ba shi a lokacin da yake matsayin firaminista.
Mista Khan ya musanta zarge-zargen tare da cewa zai ɗaukaka ƙara game da hukuncin.
Cikin wani sakon Tuwita da ya wallafa Mista Khan ya gaya wa magoya bayansa cewa ''zaɓi guda ya rage min, don haka kada ku zauna shiru a gida.''
An zaɓi Khan mai shekara 70 a matsayin firaministan Pakistan a shekarar 2018, to sai dai a shekarar da ta gabata aka tsige shi bayan kaɗa masa ƙuri'ar yankan ƙauna kan gazawarsa a fannin sojin ƙasar.
Tun bayan tsige shi Mista Khan ke fuskantar zarge-zarge sama da 100, waɗanda ya ce bi-ta-da-ƙullin siyasa ce.
Rahotonni na cewa Mista Khan ya sayar da kyautukan kan kudin kusan dala 500,000, ciki har da manyan agogunan alfarma da zobuna.
Yayin da yake yanke hukuncin, alƙalin kotun mai shari'a Humayun Dilawar ya ce rashin gaskiyar mista Khan ta bayyana ƙarara a fili.
Lauyan mista Khan Intazar Hussain Panjutha ya shaida wa BBC cewa an kammala shari'ar ne a wata ''kotun da ba za ta iya amsa sunata ba, inda ba a bai wa wanda ake zargi dama don kare kansa ba''.

Asalin hoton, others
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta fara aiwatar da tsarin 'Ba aiki, ba albashi' ga mambobin ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasar da ke gudanar da yaji aikin sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da darakta kula da ayyukan asibitocin ƙasar Dakta Andrew Noah ya aike wa manyan daraktocin asibitocin gwamnatin tarayya, kamar yadda jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito.
Wasiƙar ta ce “Ina mai sanar da ku cewa ku riƙa ɗaukar sunayen likitocin da suka zo aiki, tare da tuura sunayen zuwa ma'aikatar lafiya a kowanne wata''.
Ya kuma ce ma'aikatar lafiyar kasar tare da hukumar ƙwadago ta ƙasar da sakataren gwamnatin tarayya da majalisar dokoki ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a gwamnati sun sha yin zama da ƙungiyar likitocin don jan hankalinsu cewa su jingine yajin aikin da take yi a fadin ƙasar.
A ranar 26 ga watan Yuli ne dai ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta sanar da tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar samakon kasa biya musu buƙatunsu daga ɓangaren gwamnatin tarayya.

Asalin hoton, AFP
Shugabannin mulkin sojin Nijar sun gudanar da sabbin naɗe-naɗe a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar ranar Juma'a da daddare, sun sanar da naɗin Janar Moussa Salau Barmou a matsayin babban hafsan hafsoshin soji na kasar.
Sai kuma Kanal Amirou Kader a matsayin mataimakinsa.
Manjor Kanal Sani Kiaou shi ne sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, in ji sanarwar.
Sai kuma Kanal Abdoutahamane Zataka a matsayin mataimakinsa.
Sanarwar ta kuma ce Janar Sani Kache ne sabon sakaren ofishin ministan tsaro na ƙasar.
Sojojin na Nijar dai sun ce a shirye suke su mayar da martani idan ƙungiyar Ecowas ta kai musu farmaki cikin ƙasarsu.

Asalin hoton, FACEBOOK/MARYAM SHETTY
Matar nan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya cire sunanta daga cikin jerin sunayen da ya aike wa Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa Dakta Maryam Shetty ta ce ƙaddara ce ta sa a ka cire sunanta.
Cikin wani dogon saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook Maryam Shetty, ta ce ba za ta iya bayyana irin farin cikin da ta ji ba a lokacin da ta ga sunanta cikin jerin mutanen da ake son naɗawa a matsayin ministocin ƙasar.
Kuma hakan a cewarta wata alama ce da ke nuna cewa a shirye Najeriya take wajen tabbatar da kyakkyawar makomar mata musamman matasa kamarta.
To sai dai Dakta Shetty ta ce ƙaddara wadda ta riga fata, ta yi tasiri wajen cire sunanta daga jerin sunayen.
Ta ce ''wasu na ganin hakan tamkar wani koma-baya ne a gareni, amma ni a matsayina na musulma na yadda da ƙaddara, na ɗauki hakan a matsayin ƙaddara daga Allah, wanda shi ke bayar da mulki ga wanda ya so, kuma a lokacin da ya so''.
Ta kuma ƙara da cewa duk, da wannan abin da ya faru, tana miƙa godiyarta ga shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu kan sanya sunanta da ya yi tun da farko.
Dakta Maryam ta kuma ce hakan bai karya mata gwiwa ba, domin kuwa a cewarta tana cike da ƙwarin gwiwar bauta wa ƙasarta.
''Ina son tabbatar wa magoya baya na cewa wannan ba shi ne ƙarshe ba, yanzu ma aka fara, don haka ku ci gaba da yi wa ƙasarmu addu'a tare da goya wa shugaban ƙasarmu baya''.
A ranar Laraba ne shugaban ƙasar ya aike da sunayen mutum 19 ciki har da Dakta Maryam Shetti ga Majalisar Dattawan kasar domin tantance su a matsayin ministoci.
Sanya sunan Shetty cikin jerin sunayen ya janyo zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta a arewacin ƙasar, kasancewar sunan nata ya zo wa mutane da dama da mamaki.
To sai dai kuma a ranar Juma'a ana tsaka da tantance ministocin, sai shugaban kasar ya sake aika sunan mutum biyu zuwa majalisar, inda a ciki ya bayyana janye sunan Dakta Maryam Shetty, inda ya maye gurbinta da Dakta Mariya Mairiga Mahmud.

Asalin hoton, Boyu onanuga/Twitter
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na gudanar da gagarumin bincike kan yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya a ƙasar.
Mista Tinubu ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da shugaban Bankin Duniya Mr. Ajay Banga da ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce ''za mu gudanar da gagarumin bincike, tare da nazarin tsarin albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya''.
''Ban amince da adadin mutanen da ke kan rajistar albashin ma'aikatan gwamnatin tarayyara ba, a baya lokacin da nake gwamna na fuskanci irin wannan matsala''.
Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take don toshe duk wata kafa da kuɗaɗen gwamnati ke zurarewa.
Sanarawar ta ce za a gudanar da binciken ne domin gyara tsarin aikin gwamnati a ƙasar, tare da sauya dabi'un 'yan ƙasar da kuma wayar da kan jama'a.
Haka kuma shugaban ya ce a yanzu haka gwamnatinsa na gudanar da wani binciken ƙwaƙaf a babban bankin ƙasar CBN.
Makonni bayan rantsar Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, bisa zargin aikata ba daidai ba.