Alƙaliya ta sanya ranar fara shari'ar tsohon shugaban Amurka, Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and A'isha Babangida
Mu kasance lafiya
To a nan za mu dakatar da kawo muku labarai da rahotanni a wannan shafi na kai tsaye daga sassan duniya.
Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu. Sai gobe idan Allah ya kai mu za mu dawo.
Amma dai kuna iya gangarawa cikin wannan shafi, don ci gaba da karanta rahotannin da muka wallafa muku.
Aisha Babangida ke cewa Allah ta tashe mu lafiya.
An zane likitocin ba da agaji bayan harin ƴan bindiga a Khartoum
Asalin hoton, MSF/REUTERS
Bayanan hoto, ....
Kungiyar ba da agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce wasu masu ɗauke da makamai sun zane likitocinsu bayan sun kai wa ayarin motocinsu hari a Khartoum babban birnin Sudan.
Ayarin likitocin na hanyar kai kaya zuwa asibitin Turkiyya da ke kudancin birnin Khartoum lokacin da ƴan bindigan suka kai musu hari ranar Alhamis inda kuma suka sace ɗaya daga cikin motocinsu.
Mummunan faɗan ƙwatar iko tsakanin sojoji Sudan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) tsawon wata uku da suka gabata sun lalata cibiyoyin kula da lafiya da dama a birnin.
Yayin da sama da mutane miliyan uku a fadin ƙasar suka tsere daga gidajensu tun daga watan Afrilu, har yanzu wasu miliyoyi na makale a birnin Khartoum, inda suke fafutukar samun magunguna da taimakon jinya.
MSF na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin agaji na duniya da ke ci gaba da tallafawa asibitoci a Khartoum da birnin Omdurman, suna taimakawa wajen ci gaba da ganin harkokin kula da lafiya wanda ya kasance cikin matsala shekaru da yawa bai durƙushe ba.
Ukraine da ƙasashen yamma sun ji kunya - Putin
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ...
Shugaba Putin ya ce har yanzu yunkurin Ukraine na mayar da martanin hari a kan dakarun Rasha bai samar da wata nasara ba, duk da abin da ya kira dimbin tallafin da kasar ta samu daga kasashen yamma.
Da yake magana wajen taron majalisar tsaron Rasha, Putin ya ce kawayen Ukraine sun ji kunya sakamakon da suke samu daga fagen dagar, yana mai ikirarin cewa ra'ayin jama'a ya fara canzawa kan batun a Turai.
Shugaba Putin ya ce babu shakka kasashen yamma suna iya kara kai wani tallafin kayan yakin, amma hakan zai kara tunzura rikicin ne kawai.
Ukraine dai ta yi ikirarin cewa tana samun nasara a hare-haren martani da take kaiwa dakarun Rasha.
Kotu ta ba da umarni a ƙwace dala miliyan 130 daga hannun James Ibori
Asalin hoton, METROPOLITAN POLICE
Bayanan hoto, ...
Wani alƙali a birnin London ya ba da umarnin ƙwace dala miliyan 130 a hannun tsohon gwamnan Najeriya James Ibori, kuɗaɗen da ake zargin sato su ya yi har aka ɗaure shi a gidan yari.
Lauyan ya ba da umarnin ne a ranar Juma’ar da ta gabata.
Umarnin yana ɗaya daga cikin manyan matakan ƙwace kuɗi da aka yi wa wani mutum a tarihin shari'a na Birtaniya baya-bayan nan.
Mista Ibori ya yi gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur tsawon shekara takwas inda rahotanni suka ce ya saci kudaden da aka tanada domin gudanar da ayyukan ci gaban jihar.
A shekarar 2011 ne aka tasa ƙeyar sa daga Dubai zuwa Birtaniya, kuma an tuhume shi da laifin halarta kuɗin haram da suka kai miliyoyin daloli a wata kotun Birtaniya.
A 2012 ne, tsohon gwamnan ya amsa laifuka 10 da suka hada da zamba da halarta kuɗin haram sannan kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 13 a gidan yari.
Yanzu dai, an umarci Mista Ibori ya yafe kudin nan take ko kuma a ɗaure shi na tsawon shekara takwas.
A halin yanzu dai, tsohon gwamnan yana Najeriya. Rahotanni sun ce ya sha alwashin ɗaukaka ƙara a kan umarnin ƙwace kuɗaɗe..
Babu tabbas ko gwamnatin Najeriya za ta ba da haɗin kai wajen aiwatar da wannan oda. Tsohon gwamnan dai yana da kusanci da Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya a yanzu. Tun hawansa mulki a watan Mayu, ya karbi bakuncin Ibori sau biyu a fadarsa, tare da wasu tsoffin gwamnoni.
Hukuncin Mista Ibori a 2012 ya samu lambar yabo sosai lokacin a matsayin wani abin tarihi a yaƙi da cin hanci da rashawa a Biritaniya da Najeriya.
Akwai tsammanin cewa kudaden da za a kwace za a mayar da su Najeriya idan har shari'a ta yi nasara.
Mura ce ta hana ni zuwa wurin zanga-zanga - Raila Odinga
Asalin hoton, Reuters
Jagoran 'yan adawar Kenya Raila Odinga ya ce "mura mai tsanani" ce ta hana shi shiga zanga-zangar da aka shafe kwanaki uku ana yi kan tituna da ake yi akan tsadar rayuwa da ƙarin haraji.
"Ba lallai ba ne ganin shugabannin 'yan adawa a kan tituna," Mr Odinga ya shaida wa wani gidan talabijin na Kenya game da zanga-zangar da za a kawo karshen shi a yau.
Gogaggen dan siyasar, wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka yi ta ce-ce-ku-ce a bara, ya ce zanga-zangar neman canji ta al'umma ce ba tasa ba shi kadai.
Ya musanta rade-radin rashinsa wata dabara ce ta kulla yarjejeniya da shugaba William Ruto, inda ya kara da cewa ba ya neman shiga wani bangare na gwamnati.
"Ba mu yi ba, kuma ba za mu nemi 'tsarin musafaha' ba," in ji jagoran 'yan adawar yayin da yake magana kan sunan yarjejeniyar da ya kulla da tsohon shugaban kasar, Uhuru Kenyatta.
A nasa bangaren shugaba Ruto ya dage kan cewa ba zai shiga tattaunawa da Mr Odinga domin warware rikicin da ke faruwa a yanzu ba.
A ranar Alhamis din da ta gabata, ya yaba da martanin da ‘yan sandan suka yi – Shugaban ‘yan sandan ya ce zanga-zangar barazana ce ga tsaron kasa tare da tura jami’an kwantar da tarzoma a fadin kasar.
Sai dai wasu da dama sun soki yadda jami'an tsaro ke fuskantar masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Mutane kalilan ne suka shiga zanga-zangar adawa da gwamnati a wannan makon idan aka kwatanta da zanga-zangar da aka yi a baya. Mutane da yawa sun zauna a gida a ranakun Laraba da Alhamis, saboda fargabar tashin hankali.
Amma da alama abubuwa sun dawo daidai ranar Juma'a tare da sake buɗe makarantu da kasuwanci.
Manyan tashoshin mota a babban birnin kasar, Nairobi, da sauran garuruwa na ci gaba da aiki a hankali.
Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya N2m ga mutanen da aka yi yunƙurin rusawa gidaje
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta umurci gwamnatin jihar da sauran wadanda aka yi ƙara, su biya wasu mazauna unguwar Salanta, kudi naira miliyan ɗaya kowannensu akan yunƙurin rusa musu kadarori ba bisa ƙa'ida ba.
Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin cewa yunƙurin gwamnatin Kano da jami’anta na sanya wa gidan Saminu Shehu Muhd da na Tasiu Shehu Muhd cikin jerin gidajen da za a iya rushewa bayan an buga musu lambar jan fenti ba tare da bin ƙa’ida ba, tauye ƴancinsu ne na mallakar kadara kamar yadda sashe na 43 da 44 na tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tabbatar musu.
Jaridar Daily Trust ta ambato Barista Bashir Ibrahim, wanda ya shigar da karar a madadin Saminu da Tasiu, bayan yanke hukuncin yana yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta kare haƙƙi da martaba ƙimar ɗan'adam.
A nasa bangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano da sauran waɗanda aka yi ƙara a shari’ar, Barista Musa Dahuru Muhd daraktan shari’a a ma’aikatar shari’a ta Kano ya ce za su yi nazari a kan hukuncin tare da bai wa gwamnati shawara game da mataki na gaba.
Matan Indiya sun cinna wuta a gidan wanda ake zargi da cin zarafin mata
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Wata tawagar mata a jihar Manipur ta India sun banka wuta a gidan wani da ke kan gaba cikin wadanda ake zargi da cin zarafin mata a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan hukumomi sun kama wasu maza hudu bisa zargin hannu a garkuwa da kuma cin zarafin wasu mata biyu yan kabilar Kuki.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda matan suka kai hari kan gidan daya daga cikin mutanen da suka ci zarafin matan.
An ci zarafin matan ne a cikin watan Mayu lokacin da aka yi fama da rikici tsakanin kabilar Meitei da kuma ta Kuki a India.
Alƙaliya ta sanya ranar fara shari'ar tsohon shugaban Amurka, Trump
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Wata kotu ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump zai gurfana gaban shari'a a shekara mai zuwa bisa zargin riƙe takardun sirrin ƙasa.
Alkaliyar kotun Aileen Cannon ta sanya 20 ga watan Mayun 2024 don fara shari'ar, amma Mista Trump ya so a gudanar da ita bayan zaben watan Nuwamban baɗi.
Tsohon shugaban Amurkan mai shekara 77, yana fuskantar manyan tuhume-tuhume kan taskance takardun sirrin ƙasa a gidansa na Florida.
Masu gabatar da ƙara sun ce ya ajiye takardun sirrin ba bisa ƙa'ida ba, bayan ya bar kujerar shugabancin Amurka kuma ya kawo cikas ga ƙoƙarin hukumomi na karɓo su.
Donald Trump dai ya musanta aikata wani laifi, inda ya ce batun wani yunƙuri ne na ɓata masa harkokin yaƙin neman zaɓe.
A ranar Juma'a, Mai shari'a Cannon, wadda Trump ya naɗa, ta ce za a yi shari'ar ce tsawon mako biyu a Fort Pierce cikin jihar Florida.
Za a zaɓi masu taya alkali yanke hukunci daga kewayen yankin Fort Pierce, wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi da dama da Mista Trump ya lashe a zaɓen 2020.
Tsohon shugaban Amurkan ya ƙi amsa laifi kan tuhuma 37 da gwamnatin tarayya ta yi masa a lokacin da aka gurfanar da shi gaban kotu a Miami cikin watan jiya.
Malaman Iran sun soki matakin dawo da Hizba
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ...
Malamai masu bincike a kwalejin Musulunci ta Iran sun soki matakin dawo da jami’an Hizba don tilasta wa mata sanya hijabi a ƙasar.
Majalisar malaman ta zargi hukumomin da ke yunƙurin tilasta sa hijabin da ɗaukar matakan da suka zarce ka’ida a kan matan da basu sanya hijabin ba.
Malaman sun bayyana matakin da jami'an Hizban ke dauka a matsayin wanda ya saɓa wa tanadin doka kuma ba lallai ne ya yi nasara ba.
A baya-bayan nan ne, hukumomi a Iran suka ƙara matsa lamba wajen ganin mata suna sanya hijabi don mayar da martani ga zanga-zangar bijirewa sa hijabi wadda ta karaɗe ƙasar a bara.
Ƴan Hisban Iran za su ci gaba da kama matan da ba su rufe kansu
Sweden ta kwashe jami'an diflomasiyyarta daga Iraƙi
Bayanan hoto, ...
Ma'aikatar harkokin wajen Sweden ta kwashe jami'an diflomasiyyarta daga birnin Bagadaza na Iraƙi, bayan harin da aka kai wa ofishin jakadancinta da ke babban birnin, kuma aka ƙona shi a ranar Alhamis.
Ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka auka wa ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza ranar Laraba, bayan ƙona Al-Qur'ani da wani dan Iraqi mai neman mafakar siyasa ya yi a ƙasar Sweden.
Da ma dai mutumin ya taɓa ƙona littafin mai tsarki.
Lamarin ya janyo zanga-zanga a Iraƙi da kuma makwabciyarta Iran.
Haka kuma ya janyo kiraye-kirayen a daina amfani da kayan da aka samar daga kasar Sweden a ƙasashen Musulmai.
Ƙasashen Musulmi sun fusata da ƙona Alƙur'ani a Sweden
Gwamnatin Bauchi ta sanar da tuɓe masu sarauta shida a jihar
Asalin hoton, Sanator Bala Mohammed/Twitter
Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da korar hakimai da dagatai shida saboda a cewarta an same su da shiga harkokin siyasa da cin iyakar gandun dazuka ba bisa ƙa'ida ba.
Matakin korar wanda ya shafi masu riƙe da sarauta a masarautun Bauchi da Katagum, yana ƙunshe ne a sanarwar da Babban Sakataren riƙo a hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomi, Nasiru Ibrahim ya fitar.
Mutanen da lamarin ya shafa a cewar sanarwar, sun haɗar da Hakimin Udubo, Alhaji Aminu Muhammad Malami da Hakimin Azare Alhaji Bashir Kabir Umar da Dagacin Gadiya, Umar Omar da Dagacin Tarmasawa, Umar Bani dukkansu a masarautar Katagum.
Sai kuma Dagacin Beni Bello Suleman da Dagacin Badara, Alhaji Yusuf Aliyu Badara a masarautar Bauchi.
Sanarwar ta ambato hukumar na cewa ta amince da korar masu riƙe da sarautun ne saboda shiga harkokin siyasar jam'iyya da aikata ba daidai ba da cin iyakar dazuka ba bisa ƙa'ida ba da sare itatuwa da ɓarnatar da dukiyar jama'a da rashin biyayya, waɗanda suka saɓa da dokokin aikin gwamnati.
Tinubu ya buƙaci a sauya dokokin aikin soji a Najeriya da makwabtanta
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kamata Najeriya da makwabtanta da ke yankin tafkin Chadi su ƙara ƙaimi wajen sauya dokoki da ayyukan sojin ƙasashensu.
Bola Tinubu ya ce sauya dokokin aikin sojin ya zama wajibi sakamakon yadda ƙasashen yankin ke fama da ƙaruwar tashe-tashen hankula.
Yayin da yake jawabi awajen bikin yayen manyan sojoji kwas na 45 da aka gudanar kwalejin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna, shugaban kasar ya lissafo wasu kalubalen tsaro da ke fuskantar sojojin ƙasar da na sauran ƙasashen yankin tafkin Chadi, waɗanda ya ce suna amfani da tsoffin dokokin aikin soji.
Shugaban na Najeriya - wanda ya ƙarfafa wa ƙasashen Afirka gwiwa wajen yin aiki tare don kawar da kalubale guda da suke fuskanta - ya yaba da irin yunkurin da ƙasashen yankin tafkin Chadi ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.
Ya ƙara da cewa hadin kan da ƙasashen yankin tafkin Chadin ke yi wajen yakar ayyukan 'yan bindiga abin a yaba ne, amma yayi kira da a sauya dokokin domin kawar da barazanar da suke fuskanta
''Dole mu yi kokarin sauya dokokin aikin sojinmu. domin yakar makiyan da ke barazana ga ƙasashenmu''.
Dole mu mu sake shiri domin kawar da wannan matsala. Wannan kuma na bukatar sauyi tunani da tsare-tsare da dabarun da amuke amfani da su.
haka kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da bikin wajen bayyana manufar tsaro da gwamnatinsa ke son cimmawa, yana mai cewa zai mayar da hankali wajen samar da tsaro da adalci da dimokradiyya da ci gaban ƙasar.
Rundunar sojin saman Najeriya za ta samu ƙarin jiragen yaƙi 51
Asalin hoton, Getty Images
Babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Vice Marshal Hasan Abubakar ya ce rundunar za ta samu ƙarin jiragen yaƙi 51 domin yaƙar ayyukan 'yan bindiga a sassan ƙasar daban-daban.
Babban hafsan ya bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin sojin saman Makurdi cikin jihar Benue, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar.
Ya ƙara da cewa samun karin jiragen zai taimaka wajen habaka ayyukan horon da rundunar take bai wa jami'anta.
Air Vice Marshal Hasan Abubakar ya ce jiragen sun haɗar da manyan jiragen tattara bayanai, da masu saukar ungulu, da sauran jiragen yaƙin soji.
Samun karin jiragen ya nuna irin burin da gwamnatin ƙasar ke da shi na bunƙasa kayan aiki ga rundunar, domin magance matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta, kamar yadda babban hafsan sojin saman ya bayyana.
Ya ƙara da cewa rundunar sojin saman za ta ci gaba da aiki da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalolin ƙasar.
EFCC ta gurfanar da Stella Oduah a kotu kan badaƙalar naira biliyan biyar
Hukumar Yaki da cin hanci da yi wa tattalin arzikin Najeriya Ta'annati EFCC ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Oduah, tare da wasu mutum takwas a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.
An gurfanar da mutanen ne kan zarge-zarge 25 da suka haɗa da halasta kuɗin haram, da haɗin baki, tare da amfani da wani asusun ajiyar banki marar suna a bankin First Bank da aka samu kimanin naira biliyan biyar a cikinsa.
Sai dai bayan karanto musu zarge-zargen Oduah tare da sauran mutanen takwas ciki har da wata tsohuwar hadimarta, sun musanta duka zarge-zargen da hukumar ke yi musu.
Alkalin kotun, Mai shari'a Inyang Ekwo ya umarci ofishin babban Atoni-Janar na ƙasa da ya karbi hurumin shigar da ƙarar daga hannun hukumar ta EFCC.
Stella Oduah ta riƙe muƙamin ministar sufurin jiragen sama a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014.
Kotu ta ki yarda a taso keyar Diezani
Kotu ta mallakawa gwamnati kadarorin Diezani
FIRS ta tara harajin naira tiriliyan 5.5 cikin wata shida
Asalin hoton, FIRS/Twitter
Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Najeriya (FIRS) ta bayyana karɓar harajin naira tiriliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.
Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana haka a lokacin taron Majalisar tattalin arzikin ta ƙasar da ya gudana ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar de ke Abuja.
Wannan ne karo na farko da hukumar ta tara adadi mafi yawa na kuɗin haraji a cikin wata shida, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar.
Rahoton da Muhammad Nami ya gabatar wa majalisar tattalin arzikin, ya nuna cewa abin da hukumar ta tara ya zarta abinda ta ƙiyasta samu a cikin rabin shekarar.
Tun da farko hukumar ta ƙiyasta tara naira tiriliyan 5.3 a cikin wata shidan farko na shekarar.
Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin harajin da hukumar ta tara a ɓangaren man fetur, naira tiriliyan 2.03 ne ya fi yawa cikin harajin da hukumar ta tara.
Sai kuma naira tiriliyan 3.76 da hukumar ta tara daga sauran bangarori.
Manyan matakan rage raɗaɗi biyar da gwamnatin Najeriya za ta ɗauka
'Yan Najeriya fiye da 1,500 ne suka nemi kafa tarihi tun bayan Hilda - Kundin Guinness
Babban Editan Kundin Kafa Tarihi na Duniya, Guinness World Records Craig Glenday, ya shaida wa BBC cewa kundin ya samu takardun neman buƙatar kafa tarihi daga 'yan Najeriya 1, 572 a yunƙurinsu na kafa tarihi tun bayan tarihin daɗewa a girki da Hilda Bachi ta kafa.
Mista Glenday ya kuma shawarci mutane da su riƙa yin rajista da kundin tare da bin sharuɗansa kafin fara yunƙurin kafa tarihin.
Kundin na Guinness ya kuma ƙarfafa wa 'yan Afirka gwiwa wajen koyi da Hilda Bachi a fannin kafa tarihi.
Tun bayan kafa tarihin Hilda mutane da dama ne suka yi yunƙurin kafa tarihi a wasu fannoni daban-daban daga nahiyar Afirka.
An samu wanda ya yi yunkurin kafa tarihin kuka mafi tsawo, da mai suyan dodon koɗi da sauran abubuwa duk a yunkurinsu na kafa tarihi.
"Ina son ganin mutane na yunƙurin kafa tarihi'' in ji mista Glenday.
"Haƙiƙa muna so ganin mutanen Afirka a fagen kafa tarihi, saboda abu ne mai kyau."
Haka kuma ya ƙara da cewa kundin tarihin na Guinness na so a sanar da shi tun da fari, kafin a yi yunƙurin kafa tarihin, domin ya samu damar auna tarihin da ake son kafawar, ta hanyar bin sharudan kundin.
Mista Glenday ya ce kundin tarihin na yin watsi da kaso 95 cikin 100 na tarihin da aka yi yunkurin kafawa, sakamakon rashin bin ka'idojin kundin.
Tinubu ya amince da kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohi
Asalin hoton, Twitter/Bola Tinubu
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bora Ahemd Tinubu ya amince ca kafa asusun
gina ababen more rayuwa a jihohin kasar 36, a wani mataki na rage wa yan kasar
radadin cire tarafın man fetur.
Shugaban ya amince da matakin ne a lokacin taron wata wata na
kamitin kula da asusun raba kudin, shiga na gwamnatin kasar (FAAC) da aka
gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Dele
Alake ya fitar, ya ce sabon asusun zai taimaka wa jihohin kasar wajen zuba jari a bangarorin sufuri da harkokin noma da gina tituna da kasuwanni da kiwon dabbobi da
bangaren lafiya da ilimi musamman a matakin farko, da wutar lantarki da ruwan
sha domin habaka tattalin arzki da samar da ayyukan yi ga yan kasar.
Kwamitin ya kuma amince da ajiye wani bangare na kudin da ake
rabawa a kowane wata domin takaita tasirin aeruwar shiga da za a iya
samu sakamakon matakan cire tallatin mai da daidata farashin dala tare da
hauhawar farashin kayayyaki za su iya haifarwa.
Asalin hoton, Twitter/Bola Tinubu
Kwamitin ya ce daga cikin naira tiliyan 1.9 na kudin shigar da aka samu a watan Yunin 2023, naira biliyan 907 ne kawai za a raba tsakanin matakan gwamnatin kasar uku, yayin da za a ajiye naira biyan 790 a asusun.
Wadannan kudaden da za a riƙa ajiyewa za su taimaka wajen samar da asusun gina ababen more rayuwa tare da aiwatar da wasu abubuwa, domin tabbatar da an yi amfani da kudin tallafin wajen gina muhimman abubuwan ci gaba, domin inganta rayuwar yan kasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma kwamitin ya yaba wa shugaban kasar bisa matakin cire tatafin man tare da bullo da matakai daban-daban na tallafa wa 'yan kasar domin rage masu raɗadin cire tallafin.
Manyan matakan rage raɗaɗi biyar da gwamnatin Najeriya za ta ɗauka
A bai wa gwamnati lokaci kan cire tallafin man fetur - Sarkin Kano
Gwamnan Darfur na son fafaren hula su mallaki makamai
Asalin hoton, AFP
Gwamnan yankin Darfur da ke yammacin Sudan Minni Arko Minnawi ya sake nanata kiransa na fararen hula su mallaki makamai domin kare kansu.
Mista Minnawi - wanda tsohon ɗan tawaye ne ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la'akari da halin da yankin ke ciki a yanzu.
A baya ma mista Minnawi ya yi makamancin wannan kira, sakamakon karuwar fargabar da ake da ita kanɓarkewar yaƙin basasa a yankin wanda ya ƙunshi jihohi biyar, sakamakon yaƙe-yaƙen ƙabilanci da yankin ke fuskanta.
A jiya ne ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta aike da jirage uku ɗauke da magunguna zuwa ya ƙasar domin tallafa wa al'ummar ƙasar da ke fama da yake-yake.
Gwamnatin Kaduna ta gargaɗi al'umma kan ɓullar Mashaƙo
Asalin hoton, Facebook/Uba sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya umarci ma'aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace kan ɓullar cutar mashaƙo a wasu yankunan jihar
Ma'aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da bullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema'a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bayan samun rahotonnin ɓullar cutar tare da rasa rayuka a garuruwan.
Binciken farko da ma'aikatar lafiyar jihar ta gudanar ya nuna cewa an fara samun ɓullar cutar mashaƙo a garin na Kafancan tun farkon watan Yuli.
Sanarwar ta kuma ambato gwamnan na yaba wa hukumomin lafiyar jihar bisa ɗaukar matakan gaggawa na daƙile yaɗuwar cutar, tare da yin kira a gare ta da ta ci gaba da ƙoƙari domin yaƙar cutar a faɗin jihar.
A baya-bayan nan cutar mashaƙo na ci gaba da ɓulla a wasu jihohin ƙasar, tare da rahotonnin rasa rayuka masu yawa a wasu jihohin.
Alamomin cutar sun haɗar da wahalar numfashi, da zazzaɓi mai zafi, da tari, da kasala, da zafin maƙogoro da kuma kumburin wuya.
Hukumar lafiyar ta kuma shawarci mazauna jihar da su ɗauki matakan kariya domin kaucewa bazuwar cutar a faɗin jihar.
shawarwarin da hukumar ta bayara sun haɗar da:
Yawan wanke hannu da sabulu.
Kauce wa cuɗanya da mutanen da suka kamu da cutar
Rufe baki da hanci a lokacin tari ko atishawa
Kaurace wa makaranta ko wurin aikin idan ba ka da lafiya
Yin atisaye ko sassarfa domin inganta garkuwar jiki