Mayaƙan Wagner na horas da sojojin Belarus

Asalin hoton, Getty Images
Cikin wata sanarwa da Belarus ta fitar, ta ce sojojin hayar Wagner sun fara horar da dakarunta
Sanarwar ita ce tabbaci na farko a hukumance cewa wasu mayakan Wagner sun koma Belarus, makonni bayan tutsun da suka yi a Rasha.
Wani bidiyon ma'aikatar tsaron ƙasar ya nuna wasu mutane sanye da takunkumi na horar da wasu sojoji.
Bidiyon bai yi ƙarin bayani game da adadin mayaƙan na Wegner da ke Belarus ba.
Dama shugaba Alexender Lukashenko ne ya miƙa tayin karbarsu, a wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙashen boren da suka yi wa Moscow.
Ukraine ta ce tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Belarus, sai dai ba ta hango wata barazana ba zuwa yanzu.
- Shin juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
- Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin
