Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya ta gargaɗi bankuna a kan hulda da Kamaru da Vietnam da Croatia

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Ibrahim Yusuf Mohammed and Haruna Kakangi

  1. An yanke wa masu satar mutane ɗaurin shekara 21

    Wata kotu a Jumhoriyar demokradiyar Kongo ta yanke wa wasu mutane 21 da aka kama da laifin satar mutane hukuncin ɗaurin shekara 21 a gidan yari.

    Mai shari'a Evariste Ewalaseno ya yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, bayan gomman mutane da abin ya shafa sun bayyana a gaban kotun don bayar da shaida.

    Shaidun sun ba da labarin yadda ’yan kungiyar suka yi awon gaba da wasu daga cikin su bayan da aka yi garkuwa da su a cikin motocin tasi a cikin birnin kinshasa.

    An kammala shari'ar ne bayan kusan kwana guda na sauraren koken-koken jama'a.

    Kotun ta bude zama ne a ranar Laraba da yamma kuma ta bayar da umarnin kama su nan take domin kai su gidan yari, bayan yanke hukuncin na yau.

    A cikin bukatun da ya gabatar a gaban kotu, mai gabatar da ƙara Edmond Isova, ya nemi a yanke wa masu laifin hukuncin kisa.

    Kotun ta bayar da umarnin biyan diyya daga dala 10,000 zuwa dala 20,000 ga mutane 23 da abin ya shafa, ciki har da Serge Movili Mazami, wani fitaccen makaɗi wanda aka fi sani da Celeo Scram, wanda aka yi masa fashi.

    Kotun ta ce masu laifin na iya daukaka kara kan hukuncin.

    Jama’a da dama ne suka halarci zaman domin sanya ido, duk da cewa an yanke hukuncin ne da maraicen yau Juma’a.

    Jama'a sun hallara don jinjina wa kotun kuma hukuncin da aka yanke ya samu karɓuwa ga mazauna Kinshasa, waɗanda da dama suka kasance cikin fargabar shiga tasi.

    Wadanda aka yanke wa hukuncin dai kashi na farko ne na mutane 27 da ake tuhuma da laifin gudanar da ayyukan a Kinshasa babban birnin kasar.

  2. Amurka za ta tura wa Ukraine bam mai jigida domin yaƙi da Rasha

    Amurka ta tabbatar da cewa za ta aike da bama-bamai masu 'ya'ya zuwa Ukraine domin dakarunta su yi amfani da su wajen yaƙar sojojin mamaye na Rasha.

    Mai bayar da shawara kan harkokin tsaro a fadar White House, Jake Sullivan ya ce matakin martani ne kan buƙatun da Kyiv ta gabatar ganin cewa Rasha na amfani da manyan makamai a yakin.

    Mista Sullivan ya ce babu lokacin da Amurka za ta bar Ukraine cikin rashin tsaro, kuma ya ce bama-baman na Amurka sun fi aiki sosai fiye da waɗanda Rasha ke amfani da su.

    Inda hakan ke nufin ba a cika samun ragowar waɗanda ba su fashe ba.

  3. An yanke wa ɗan bindiga-daɗi hukuncin ɗaurin rai-da-rai sau 90 a jere

    An yanke wa wani dan bindiga da ya harbe mutane ashirin da uku a wani babban kanti na Walmart da ke jihar Texas ta Amurka a shekarar 2019 hukuncin ɗaurin rai-da-rai sau 90 jere.

    Patrick Crusius ya aiwatar da harin, inda ya hari mutane baƙi, musamman waɗanda suka fito daga nahiyar Kudancin Amurka, mintuna kadan bayan ya wallafa wani saƙo a intanet, inda ya yi nuni da abin da ya kira 'farmakin' da baƙin haure ke kawo wa Amurka.

    Ya amsa tuhumar manyan laifukan da ake yi masa guda casa'in da suka hada da laifuka arba'in da biyar na nuna ƙiyayya a watan Fabrairu.

    Harin da aka kai a birnin El Paso ya kasance ɗaya daga cikin manyan harbe-harbe mafi muni a tarihin Amurka.

  4. An garzaya da Van Der Sar asibiti saboda tsiyayar jini a ƙwaƙwalwa

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da Ajax Edwin Van Der Sar na samun kulawa ta musamman bayan da ya samu zubar jini a kwakwalwarsa.

    An bayar da rahoton cewa, mai shekarun 52, yana jinya a wani asibiti a Croatia, inda ya tafi hutu.

    Ajax ta ce tsohon dan wasan na Netherlands, wanda ya ci wa ƙasarsa wasanni 130, "ba ya cikin mummunan hali."

    Ta ƙara da cewa "Kowa a Ajax na yi wa Edwin fatan samun sauƙi cikin hanzari."

    Van der Sar ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban Ajax a watan Mayu bayan ƙungiyar ta ƙare a matsayi na uku a gasar kulob na ƙasar Holland kuma ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a karon farko tun 2009.

    Ya yi ritaya daga buga wasa bayan ya bar United a shekarar 2011 kafin ya koma ƙungiyar Ajax a shekarar 2012 a matsayin ɗan majalisar gudanarwarta, kafin ya zama shugaban kungiyar ƙwalon ƙafar a shekarar 2016.

    Van der Sar ya buga wa Machester United wasanni 266 kuma ya taimaka mata wajen lashe kofunan Firimiya uku da gasar zakarun Turai a 2008.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, Manchester United ta ce: Tana yi ma Van der Sar fatan samun sauki cikin hanzari.

    Ya kuma buga gasar Premier a Fulham da kuma a Seria A a Juventus.

  5. An buƙaci Tunisiya ta daina korar baƙaƙen fata ƴan ci-rani

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch (HRW) ta ce ya kamata mahukuntan a ƙasar Tunisiya su dakatar da abin da aka bayyana a matsayin "kawar" da bakin haure da suka fito daga kudu da sahara.

    Kungiyar ta ce a cikin 'yan kwanakin da suka gabata kasar Tunisiya ta kori ƴan ci-rani masu neman mafaka da dama musamman baƙaƙen fata daga ƙasashen Afirka da suka hada da yara da mata masu juna biyu daga tashar jiragen ruwa na Sfax da ke kusa da kan iyakar ƙasar Libiya.

    Ta ce an bar su a maƙale kuma suna cikin mawuyacin hali a wani yanki mai nisa a cikin hamada.

    Lauren Seibert, mai bincike kan 'yancin 'yan gudun hijira a HRW ta ce "Ya kamata gwamnatin Tunisiya ta dakatar da korar baki tare da bayar da agajin gaggawa ga ƴan ci-rani na Afirka da kuma masu neman mafaka da aka riga aka kora zuwa wani yanki mai hadari.

    Rikicin na baya-bayan nan dai ya samo asali ne sakamakon kisan wani ɗan ƙasar Tunisiya a lokacin wani artabu tsakanin 'yan Tunisiya da ƴan ci-rani a Sfax, a ranar 3 ga watan Yuli.

    Tashin hankalin ya ci gaba da yin kamari, wanda ya kai ga yawaitar hare-hare masu nasaba da kabilanci.

    Ƙungiyar ta HRW ta buƙaci gwamnatin Tunisia da ta gudanar da cikakken bincike kan cin zarafin da aka samu tare da hukunta jami'an tsaron da ke da alhakin kai harin.

    Tashin hankali ya ƙaru a Tunisiya tun bayan da shugaban ƙasar Kais Saied ya yi zargin cewa baƙin hauren na da hannu a cikin wata makarkashiya da ke neman sauya fasalin al'ummar ƙasar.

  6. Gwamnan Taraba ya ayyana karatun firamare da sakandare kyauta don rage raɗaɗin cire tallafin mai

    Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ayyana karatu a matsayin kyauta a daukacin makarantun firamare da sakandare da ke faɗin jihar.

    Gwamnan ya ce matakin zai fara aiki ne daga zangon karatu mai zuwa, domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi.

    Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Emmanuel Bello ya fitar.

    Gwamnan ya jaddada cewa hakkin gwamnati ne ta dauki nauyin ilimi a matakin farko, saboda haka bai kamata dalibai su rika biyan ko sisi ba.

    Ya ce baya ga cika alkawarin neman zabe, wahalhalun da aka samu na cire tallafin man fetur sun sanya ya zama wajibi a ɗauki wannan mataki.

    A baya dai gwamnan ya rage kudaden shiga jami’o’i da kashi 50 cikin 100 domin rage wahalhalun da al'umma ke fuskanta.

  7. Saliba ya tsawaita zamansa a Arsenal

  8. Wace ce mace ta farko Babbar Alƙaliya ta jihar Kano?

  9. An kori malamar jinyar da ta yi lalata da maras lafiya

    An kori wata malamar jinyar masu lalurar ƙwaƙwalwa a yankin Shropshire da ke Birtaniya bayan ta yi lalata da wani majinyaci.

    Matar, mai suna Samantha Bourton wadda ke aiki da gidauniyar ma’aikatar lafiya ta Birtaniya, an gano cewa tana zuwa gidan majinyacin har a lokutan da ba na aiki ba.

    Wani kwamitin bincike da aka kafa ya kuma gano cewa ta ƙi bayar da rahoton cewa mara lafiyan ya taɓa yin tunanin kashe kansa.

    Hukumar tantance malaman jinya da ungozoma ta Birtaniya ta ce ba za a lamunci wannan ɗabi’a ta malamar jinyar ba.

    Ganin cewa ƙimar aikin zai zube idan aka bar ta ta ci gaba da aiki.

    A cikin wani bayani, kwamitin ya ce Ms Bourton ba ta musanta cewa ta sadu da majinyacin ba a watan Mayu na 2021.

    Kwamitin ya ce ta tuntuɓi mutumin ta hanyar amfani da lambar waya ta ƙashin kanta sannan ta ziyarce shi sau biyu a lokutan da ba na aiki ba.

    Sai dai an gano cewa sauran ziyarar da ta kai masa daga baya, ba ta yi ne domin yin lalata da shi ba.

    A yanzu an dakatar da ita na wata 18, a matsayin matakin farko, inda za ta iya ɗaukaka ƙara a tsakanin wa’adin.

    Sai dai idan ba ta ɗaukaka ƙara ba, korar ta tabbata.

  10. An ɗauki tsauraran matakan tsaro gabanin zanga-zangar Kenya

    An ɗauki tsauraran matakan tsaro a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya da wasu manyan garuruwa a daidai lokacin da ake tsammanin magoya bayan 'yan adawa za su gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa.

    An bayar da rahoton zanga-zanga a wurare da dama da suka hadar da Nairobi da Mombasa da Kisumu, inda 'yan sanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa jama'a.

    Kafofin yada labarai na cikin gida sun ce masu zanga-zangar sun lalata wuraren kasuwanci da dama a Kisumu.

    An dai samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar a sassa da dama na birnin Nairobi, kuma an toshe wata babbar hanyar zuwa cikin birninin da safe.

    Ana sa ran jagoran 'yan adawa Raila Odinga zai yi jawabi a wani babban gangamin siyasa a babban birnin ƙasar nan gaba.

    Sannan zai sanar da komawar zanga-zangar ta mako-mako a fadin Kenya.

    Hukumomin ƙasar sun ba da damar gudanar da gangamin amma sun yi gargadi ga masu zanga-zangar da kada su shiga tsakiyar birnin Nairobi.

    Ana sa ran Mr Odinga zai fara gangamin tattara sa hannu domin nuna goyon baya ga yunƙurin tilastawa gwamnati rage farashin muhimman kayayyaki kamar man fetur.

    Zanga-zangar ta zo ne bayan shugaban ƙasar William Ruto ya sa hannu a kan ƙuduri mai janyo ka-ce-na-ce don ƙara haraji zuwa doka- a ciki har da na man fetur .

  11. Najeriya ta gargaɗi bankuna a kan hulda da Kamaru da Vietnam da Croatia

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a ƙasar su ƙara sanya ido wajen harkokin kasuwanci da mutane daga ƙasashen Kamaru da Croatia da kuma Vietnam.

    Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare da hada-hadar kuɗi Mista Chibuzo Efobi ya fitar a Abuja.

    A cewar CBN, bankunan Najeriya da sauran cibiyoyin kudi na bukatar su yi hankali da yin hulɗar kasuwanci da waɗancan ƙasashe, saboda a baya-bayan nan, Hukumar sa ido kan ayyukan halatta kuɗin haram da kuɗaɗen aikata ta'addanci a duniya (FAFT) ta sanya su a jerin ƙasashen da ake sanya wa ido.

    Sanarwar ta ce, "An janyo hankalin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ga sakamakon da hukumar FAFT ta gudanar daga ranar 21 - 23 ga watan Yuni, 2023 inda ta sanya Kamaru da Croatia da kuma Vietnam a cikin jerin ƙasashe da za a ƙara sa wa ido"

    "Bugu da ƙari, Koriya ta Kudu da Iran da Myanmar sun ci gaba da kasancewa cikin jerin ƙasashen da ake sanya wa ido."

    A watan Fabrairu, hukumar FAFT dai ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da za a sawa ido amma sanarwar baya-bayan nan daga Hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya ta ce yunkurin da ƙasar ta yi na ficewa daga cikin jerin ya tilastawa FATF rage wuraren da aka ga tana da rauni daga 84 zuwa 15.

    • CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
    • CBN ya taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa a banki da POS
  12. Ricikin Khartoum ya tilasta wa fiye da mutum miliyan uku barin muhallansu - OIM

    Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya (OIM) ta ce akalla mutum miliyan hudu ne suka tsere daga birnin Khartoum zuwa jihar al-Jazir mai makwabtaka, bayan barkewar fada tsakanin sojoji da dakarun sa kai na Rapid Support Forces (RSF) a kasar a tsakiyar watan Afrilu.

    Hukumar ta kuma ce akalla mutum 700,000 ne suka fice daga kasar tun bayan barkewar rickin.

    Kafin barkewar rikicin, akwai sama da mutum miliyan shida a biranen Khartoum da Omdurman da Bahri.

    Jihar al-Jazira tana kudancin Khartoum kuma tana cikin yankunan da fadan ya fi kamari.

    A baya-bayan nan dai bangarorin da ke afada da juna sun tsananta kai hare-hare, inda aka yi ta samun tashe-tashen hankula a sassa da dama na ƙasar da suka hada da yankunan Khartoum da Darfur da kuma Kordofan.

  13. An ɗaure matashin da ya kashe malamarsa a kan ƙwauron maki

  14. 'Yan sandan Kano za su buga wasan sada zumunta da tubabbun 'yan daba

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano (CP), Muhammed Usaini Gumel, ya ce hukumar za ta shirya wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar ta da wasu ‘yan daban da suka tuba, a wani mataki na tabbatar da gaskiyar tubansu.

    Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wasu mutane 108 da aka kama da laifuka daban-daban a lokacin bikin Sallah da ya gabata.

    Ya ce, “Za mu bullo da wata hanya ta daban don tabbatar da cewa wadannan ‘yan daban suna canza rayuwarsu tare da zama mutanen kirki. Har ma za mu shirya gasar wasanni da su. Za mu buga wasan ƙwallon ƙafa.

    “Yanzu za mu mayar da hanalin mu da idanunmu kan ayyukan ‘yan daba (daba) da ke kunno kai, musamman a cikin babban birnin Kano'', in ji Kwamishinan.

    CP Muhammed ya ƙara da cewa sun tsara dabarun aiki da kuma ingantaciyar hanyar tara bayanan sirri domin magance duk wani nau'in laifi da ake aikatawa a ciki da wajen jihar Kano.

    • Mutane da dama sun jikkata a rikicin siyasar Kano
    • Zaɓen 2023: "Na tuba da banga abin da 'yan siyasa ke ba mu ko abinci ba zai saya ba"
  15. Aƙalla sojojin Wagner 600 sun janye daga CAR

    Sojojin Wagner kimanin 600 sun janye daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), kamar yadda jaridar Le Democrate mai zaman kanta ta ruwaito.

    Jaridar ta ce "A cikin 'yan kwanakin nan, an lura cewa wasu mayaƙan Wagner suna ficewa dagan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya."

    Ya kara da cewa, watakila janyewar tasu na da alaƙa ne da yunƙurin tawayen da shugabansu Yevgeny Prigozhin ya yi a watan Yuni kan gwamnatin Vladmir Putin.

    Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil adama ta All Eyes ta faɗa a ranar Alhamis cewa tsakanin soja 500 zuwa 600 na Wagner ne suka bar ƙasar.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta yi alƙawarin cewa sojoji masu horas da jami'an tsaro za su ci gaba da a Jamhuriyar Afirta ta Tsakiya da Mali duk da rikicin tawayen sojojin Wagner.

    An ba da rahoton janyewar kusan mako guda bayan da Sergei Lavrov na Rasha ya ce ƙasashen Afirka na da 'yancin ko dai su ci gaba da aiki da sojojin Wagner ko kuma su raba gari da su.

    Tashin hankalin da Wagner ta yi a watan jiya ya haifar da tambayoyi da rashin tabbas a kan makomar sojojin ƙungiyar da ke aiki a Mali, CAR, waɗanda kuma aka yi imanin akwai su a Burkina Faso da Sudan.

    • Shin me juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
    • Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin
  16. 'Yan sandan da suka taka mutum da mota na fuskantar hukunci a Najeriya

    Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya na riƙo, Olukayode Egbetokun, ya ce ‘yan sandan da ake zargi da taka wani mutum da mota lokacin da yake ɗaure da ankwa a jihar Edo, suna fuskantar ladabtarwa.

    Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, bayan ‘yan sanda sun taka shi da motarsu ne, sai kuma suka yi ta jan sa a ƙasa a kan titin Ekpoma na jihar Edo.

    An ce lamarin ya haifar da fargaba da tunzuri a yankin.

    A ranar Juma’ar da ta gabata ne Babban Sufeton ya sammaci ‘yan sandan da suka aikata wannan abu zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja.

    Sai dai kuma wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar ranar Alhamis ta ce Babban Sufeto ya bayar da umarnin rushe ayarin ƴan sandan a jihar.

    Sanarwar ta ce, “A wani namijin yunƙuri don magance rashin ɗa’ar da wasu ‘yan sanda suka aikata a rundunar ‘yan sandan Edo ta hanyar taka wani ɗan ƙasa da mota a Ekpoma, muƙaddashin babban sufeton na Najeriya ya dauki matakin rusa ayarin 'yan sandan nan take."

    "Wannan matakin na da nufin daidaita zaman 'yan sanda a jihar da ƙarfafa gwiwar jama'a ta yadda za su sake yarda da 'yan sanda."

    Ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin nuna cewa rundunar ta yi Allah-wadai da irin wannan hali.

  17. 'Yan majalisar adawar Ghana sun kauracewa majalisar

    ‘Yan majalisar adawa a Ghana sun kaurace wa zaman majalisar a ranar Alhamis, domin nuna goyon bayansu ga shugabansu a majalisar da kuma wani sabon zababben dan majalisar, wadanda ke fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume daban-daban.

    Babbar jam'iyyar adawa ta National Democratic Congress, ta ce wannan shi ne farkon matakan da suke dauka "don kawo karshen zalintar da ake yi wa" 'yan majalisar.

    Rashin halartar 'yan majalisar waɗanda ke da rabin 'yan majalisar dokokin Ghana ya tilasta wa shugaban majalisar dage ci gaba da zaman majalisar saboda yawancin batutuwan da ake tattaunawa a majalisar tambayoyi ne daga 'yan majalisar adawan.

    Ana zargin shugaban marasa rinjaye Cassiel Ato Forson da barnatar da kudi dala miliyan 2.5 wajen sayo motocin daukar marasa lafiya 200, zargin da ya musanta.

    Sabon dan majalisar kuma, James Quayson, yana fuskantar shari'a kan zargin amfani da takardun bogi da yi karya.

    Ya bayyana shari’ar da ake yi masa a matsayin razanarwa, sannan kuma ya ce bi-ta-da-kullin siyasa ce kawai.

    Kotun kolin ta soke zaben nasa ne kasancewar yana da takardun shaidar zama dan kasar Gnba da Canada, amma kuma bai bayyana hakan ba a lokacin da ya tsaya takarar a zaben 2020.

    Alkalin wata babbar kotu ya umarce shi ya gurfana a gaban kotu a kowace rana, umarnin da yanzu yake kalubalantarsa ​​a kotun daukaka kara.

  18. Ku San Malamanku tare da Dr Abubakar Sani Birnin Kudu

  19. An samu raguwar sare dajin Amazon

    Gwamnatin Brazil ta ce adadin sare itatuwa a dajin Amazon ya ragu da kashi uku cikin watanni shida na farkon wa'adin mulkin shugaba Luiz Inacio Lula da Silva.

    Bayanan cibiyar binciken sararin samaniyar kasar sun nuna cewa girman murabba'in kilomita 2650 na fadin dajin aka sare a farkon rabin shekarar nan, abun da ke nufin adadin ya ragu, idan aka kwatanta da 4000.

    Shugaba Lula da Silva ya yi alƙawarin kawo ƙarshen lalata dajin mafi girma a duniya, wanda yake zargin ba a ba shi kulawar da ta dace ba, a zamanin mulkin shugaba Jair Bolsonaro da ya gabace shi.

    Kare dajin Amazon na da matukar muhimmanci a duniya a yakin da ake yi da matsalar sauyin yanayi, amma yana fuskantar barazanar gobarar daji, inda galibi yake shafe filayen noma.

    Brazil ke da kusan kashi 60 na dajin, wanda ya shafi wasu kasashen Latin

  20. MDD ta yi kiran a gaggauta kai wa Haiti dauki

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira da a kara daukar matakai domin tunkarar matsalolin tsaro cikin gaggawa a kasar Haiti.

    Mista Guterres, wanda ya ziyarci kasar a makon da ya gabata, ya ce shi da kansa ya ga irin mawuyacin halin da ake ciki, ya kuma yi kira da a tura dakarun kasa da kasa cikin gaggawa.

    Ya ce dole ne duniya ta tashi tsaye, wajen kawo karshen tashin hankalin, da kuma kawo zaman lafiya.

    Ministan harkokin wajen Haiti, Jean Victor Geneus, ya ce Majalisar Dinkin Duniya na da alhakin daidaita al'amura a Haiti.