Shugaba Tinubu ya taya Musulmai Barka da Sallah

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed and Umar Mikail

  1. Abin da ya sa Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur - Garba Shehu

    ...

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

    Mai magana da yawun tsohon shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban Muhammadu Buhari ya dakatar da batun cire tallafin man fetur da kuma daidaita tsarin canjin kudin kasashen waje na kasar "zuwa lokacin da ya dace."

    Shehu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, makwanni hudu bayan da Shugaba Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki daga hannun Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, ya kuma sanar da cire tallafin man fetur, inda farashi litar mai ta tashi daga naira 184 zuwa sama da naira 500.

    Shehu ya kuma yi nuni da cewa idan za a yi “maganar gaskiya a siyasance” gwamnatin Buhari, a kwanakinta na karshe, ba za ta iya ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da ka iya girgiza kasa ba “saboda jami'yyar APC na bukatan lashe zabe”.

    ''Tun da yanzu zabe ya wuce, shugaba Bola Tinubu ya fi dacewa ya ci gaba daga inda aka tsaya. Mu na da cikakkekn imanin cewa sabuwar gwamnatin za ta sa al’ummar kasa da daukacin al’ummarta su samu kyakkyawar makoma bayan wadannan manyan matakai na tattalin arziki”, in ji Shehu.

    Mai magana da yawun tsohon shugaban ya ci gaba da cewa duk da cewa tsohon shugaban kasan bai cire tallafin man fetur ba, amma ya cire tallafin wutar lantarki da tallafin taki da tallafin kan aikin Hajji, da na ziyarar Jerusalem, da tallafin dizal, da na man jirgin sama, da tallafin kalanzir da dai sauransu.

    • Zan cire tallafin man fetur ko za a yi zanga-zanga a Najeriya - Tinubu
    • Mene ne tallafin man fetur kuma me ya sa batun cire shi ke kaɗa hantar ƴan Najeriya?
  2. Zazzaɓin maleriya ya ɓulla a Amurka

    Sauro

    Asalin hoton, AFP

    Mahukunta lafiya a Amurka sun ce a karon farko cikin shekaru 20, cutar malariya ta bulla a kasar.

    An ba da sanarwar ce bayan gano mutun hudu dauke da ke ita a Florida watanni biyu da suka gabata,

    Jami'an gwamnatin jihar Florida sun fitar da gargadi tare da jan hankalin mazauna yankin su rinka tsaftar muhallinsu da amfani da gidan sauro da maganin feshi.

    Haka kuma an fitar da irin wannan gargadi a jihar Texas.

    Ana iya cewa babu zazzaɓin maleriya a Amurka ko ba kasafai ake samunta ba a kasar, akasari mutane ne ke shiga, amma masana kimiyya sun yi gargadi cewa a yanzu zazzabin na iya yaduwa saboda sauyin yanayi.

    Maleriya na haddasa zazzabi mai tsanani da kasala. Kuma tana sanadin rayukan dubban mutane a duk shekara a fadin duniya.

  3. Barka

    Barkanmu da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi na jajiberin Babbar Sallah.

    Ibrahim Yusuf Mohammed ne da Umar Mikail ke fatan kun tashi lafiya kuma mu ne za mu kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Ku biyo mu.