Ma'aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aiki

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Sojojin Najeriya sun kuɓutar da masu juna-biyu daga gidan sayar da jarirai

    gg

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da runduna ta 14 a Ohafia sun kai samame wani gidan da ake zargi ana ajiye mata don su haihu kafin sayar da jariran a unguwar Umunkpei Nvosi ta yankin ƙaramar hukumar Ngwa cikin jihar Abia da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Sojojin sun samu nasarar kuɓutar da mata 22, waɗanda 21 daga cikinsu ke da juna biyu, baya ga jarirai biyu.

    Sauran abubuwan da aka samu a cikin gidan sun haɗar da injin bayar da wutar lantarki da tukunyar gas, da buhun shinkafa, da man girki da buhun garin kwaki biyu da sauran abubuwa.

    Jami'an tsaron sun ce sun kai samamen ne bayan da suka samu bayanan sirri, cewa wadda ta mallakin gidan na sayar da jarirai ga wasu mutanen domin aikata tsafi, da masu safarar yara.

    Ana zargin cewa matar ta ɗauki lokaci tana aikata laifin a yankin bayan da aka riƙa ganin sassan jikin mutane a kusa da ginin gidan.

    Wani daga cikin dakarun sojin ya ce matar da ta mallaki gidan ta tsere a lokacin samamen, sai dai ya ce ana ƙoƙarin kama ta.

    Tuni jamai'an tsaron suka miƙa matan da suka kuɓutar tare da jariran zuwa hannun gwamnatin jihar Abia domin ɗaukar mataki na gaba.

  2. Sojojin Sudan sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Mataimakin shugaban majalisar dake mulki a Sudan, Malik Agar, ya yi maraba da wata yarjejeniyar tsagaita wutar da za a cimma.

    Amma ya ce ba za a sanya hannu kan yarjejeniyar ba har sai dukkannin dakarun da ke ƙasar sun janye daga Khartoum babban birnin kasar.

    Ya ce ba wai batun amincewa a tsagaita wuta ba ne kawai, idan ana so a samu abin da ake buƙata to akwai buƙatar janye sojoji daga ma'aikatun gwamnati da kuma yankunan gidanjen jama'a.

    Rikici na ƙara ta'azzara a Khartoum da kuma yammacin yankin Darfur tun bayan bayan rushewar yarjejeniyar da aka cimma a Saudi Arabia a makon da ya wuce.

    Dukkan ɓangarorin da ke rikici da juna a ƙasar na zargin juna da karya ƙa'idojin yarjejeniyar.

    To amma duk da haka ana fatan masu shiga tsakanin a birnin Jedda za su cimma matsayra da za ta kawo karshen rikicin ƙasar.

  3. An koma zirga-zirga a titin jirgin ƙasan da aka samu hatsari a Indiya

    ee

    Asalin hoton, Getty Images

    Jiragen ƙasa sun koma zirga-zirga a layin dogon da aka samu mummunan hatsarin jiragen ƙasa a ranar Jumma'ar da ta wuce a India.

    An shafe fiye da sa'oi 50 babu jirgin ƙasan da ya bi ta layin dogon da lamarin ya afku, saboda ƙoƙarin da aka yi na cire taragon jiragen ƙasan da suka yi taho-mu-gama da juna a Odisha.

    Mutane fiye da 280 ne suka rasa ransu a hatsarin jiragen ƙasan, yayin da har yanzu kuma ba a kai ga tantance wasu mutanen da lamarin ya rutsa da su ba kusan 300.

    Tuni dai aka fara bincike akan abin da ya janyo hadarin.

  4. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da sadiyar wannan ranar ta Litinin, da Bahaushe ke yi wa kirari da 'Mande tushen aiki ko da Nasara na tsoronki'

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin sanar da ku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.