An ga watan Sallah a Saudiyya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mutum miliyan 2.5 ne suka halarci saukar Al'qur'ani a daren 29 a Masallacin Makkah

    Masu ibada a Masallacin Harami na Makkah

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masallacin Harami guda biyu sun cika makil da masu ibada

    Sama da masu ibada miliyan 2.5 ne suka halarci saukar Al-Qur’ani a daren 29 na watan azumi, a babban Masallacin Juma’a na Makkah. Cikin mutanen har da masu aikin Umarah da kuma waɗanda sallar ce kawai ta kai su.

    Sheikh Abdurahman Al-Sudais, babban limamin Masallacin Harami guda biyu ne ya jagoranci sallar a babban Masallacin Juma’a, wanda mutane sama da miliyan biyu suka halarta.

    Masallacin Harami guda biyu sun cika makil da masu ibada har ma da titunan da ke kewaye da su.

    Da yake jagorantar addu'o'in, Sheikh Al-Sudais ya roki Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta wa dukkan musulmi a wannan dare mai albarka, ya kuma tseratar da su daga shiga wutar jahannama.

    Ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da kare Masarautar Saudiyya da shugabanninta da kuma dukkan ƙasashen musulmi daga dukkan sharri, ya kuma ba su lafiya da kwanciyar hankali.

    Masu ibada a Masallacin Harami na Makkah

    Asalin hoton, Haramain SharifainTwitter

  2. Libya ta musanta hannu a rikicin Sudan

    Rundunar sojin ƙasar Libya da ke mubaya'a ga Janar Khalifa Haftar, ta musanta mara wa wata jam'iyya mai hamayya a Sudan a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗa.

    Janar Haftar ne ke jagorantar gwamnatin rikon ƙwarya ta Libya da ke da iko a gabashin ƙasar, amma ƙasashen duniya sunyi watsi da jagorancin nasa.

    Kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito cewa mai magana da yawun dakarun na Libya, Ahmad Mesmari ya musanta rahotannin bayar da goyon baya ga wani ɓangare a Sudan.

    Ya ce sojojin ƙasar a shirye suke su taimaka wajen shiga tsakani don warware rikicin Sudan.

    Tun a ranar Asabar ne dai sojojin Sudan da dakarun RSF ke fafatawa a faɗan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 270.

  3. Najeriya ta musanta gaza biyan bashin China

    Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A baya-bayan nan dai Najeriya ta yi asarar kuɗin shiga sakamakon yawaitar hare-haren kan hanyoyin jiragen kasa

    Ofishin kula da basussuka na Najeriya, ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza biyan kuɗin ruwa ga China don samun bashi.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa an ci tarar Najeriya $90m bayan bashin da China ke bin ta ya ƙaru zuwa dala miliyan 240 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

    An ce an karɓo bashin ne domin gyara wasu layukan dogo a ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, DMO ya musanta rahotannin, inda ya ce Najeriya ta jajirce wajen ganin ta mutunta bashin da ake bin ta, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen biyan basussukan da ta ciyo.

    Sanarwar ta kara da cewa, "Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta biya bashin da ake bin ta a kan lokaci."

    Don haka ofishin ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin.

    Ya zuwa watan Disamba na 2021, DMO ya ce, bashin da China ke bin Najeriya ya kai dala biliyan 4.1, sai dai bai yi ƙarin haske ba kan yawan bashin da Najeriya ta ciyo ba daga ƙasar China ba zuwa yanzu.

    A shekarun baya-bayan nan dai Najeriya ta yi asarar kuɗin shiga sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa kan hanyoyin jiragen kasa da kuma sace fasinjojin da ya yi sanadiyar dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a wasu hanyoyin na ɗan wani lokaci.

  4. An shiga ruɗani a Yemen bayan turmutsutsun rabon kayan sallah

    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Wani hoton bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mutane suka shiga ruɗani a wajen wata makaranta da aka samu mutuwar mutum 80 a turmutsusun rabon kayan sallah a Bab al-Yemen da ke Sanaa, babban birnin ƙasar.

    Akwai kuma ƙarin mutane da suka jikkata - ciki har da mutum 13 waɗanda ke asibiti cikinn mawuyacin hali, a cewar jami'ai.

    Ɗaruruwan mutane ne ciki har da ƙananan yara suka taru a wata makaranta domin karɓar tallafin kayan sallah.

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida na kungiyar Houthi, ya ɗora laifin turmutsusun kan rashin tsari mai kyau na rabon tallafin daga wajen jami'ai.

    Sai dai shaidun gani da ido biyu, sun bayyana cewa mayakan ƴan Houthiu sun yi harbi a iska a wani yunkuri na shawo kan dandazon mutane da suka taru, inda hakan ya jawo wayoyin wutar lantarki suka haɗu tare da fashewa da kuma kawo ruɗani a cikin mutane.

  5. Yara miliyan 67 ba su ƙarasa riga-kafi ba saboda korona - UNICEF

    Rigakafi

    Asalin hoton, UNICEF

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin duniya ya ce kusan yara miliyan 67 ne ba su samu damar yin allurar riga-kafi a karon farko ko kuma ba a ƙarasa yi musu riga-kafin ba saboda kullen korona.

    UNICEF ya ce ba a samu damar kai maganin rigakafin ba a sama da Ƙasashe ɗari sannan yayi gargaɗin cewa aminta da rigakafi da akayi a ƙasashen duniya zai iya samun tasgaro.

    Wakiliyar BBC ta ce kwarin gwiwar da ake da shi kan rigakafi ya ragu fiye da kashi 3 a ƙasashen Koriya ta Kudu da Ghana da Senegal da kuma Japan.

    Tuni dai wannan raguwar ya kawo koma baya kasancewar a shekarar da ta gabata adadin yara da suka kamu da cutar Polio ya ruɓanya.

  6. Mutum 80 sun mutu a turmutsutsun rabon kayan sallah a Yemen

    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Mayakan ƙungiyar Houthi sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 80 a wani turmutsutsu da ya auku yayin rabon kayan ƙaramar sallah a Sanaa babban birnin Yemen.

    Ɗaruruwan mutane ne ciki har da ƙananan yara suka taru a wata makaranta domin karɓar tallafin kayan sallah.

    Jami'an kungiyar Houthi da ke da iko da birnin sun ce lamarin ya auku ne a yankin Bab-al-Yemen.

    Wakilin BBC ya ce jami'an lafiya na daga ƙungiyar Houthi da ke iko da babban birnin na Yemen sun ce an garzaya da waɗanda suka ji raunuka da kuma waɗanda suka mutu zuwa asibiti a Bab-al-Yemen ɗin da ke tsakiyar birnin.

    Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yanayi na ruɗani da kuma gawawwakin yara duk kwakkwance.

  7. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa, barkan mu da safiyar Alhamis.

    Ahmad Tijjani Bawage ke muku lale marhabin da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.