Abubuwan da ke faruwa kan zaɓen gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa kan zaɓen gwamnoni da ake gudanarwa a wasu jihohin Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Afirka ta Kudu ta girke sojoji a asibitocin ƙasar kan yajin aikin ma'aikata

    Jami'ai

    Asalin hoton, Getty Images

    Afirka ta Kudu ta girke dakarun soji a asibitocin ƙasar yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar rahotonnin da ke cewa likitoci za su shiga yajin aikin da ma'aikata ke yi a ƙasar kan ƙarin albashi.

    Tun cikin makon da ya gabata ma'aikatan gwamnati a ƙasar ke zanga-zangar neman ƙarin kashi 10 cikin 100 na albashi. Gwamnatin ƙasar dai ta yi wa ma'aikatan karin kashi 4.7 cikin 100.

    Ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar har sai gwamnatin ƙasar ta biya musu buƙatunsu.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an girke dakarun soji a asibitocin Thelle Mogoerane, da Sebokeng a yankin Bheki Mlangeni, yankin da zanga-zangar ta fi ƙamari.

    Ministan lafiyar ƙasar Joe Phaahla ya ce yajin-aikin ya yi sanadiyyar rasa rayuka

  2. Sudan ta Kudu ta tabbatar da ɓarkewar cutar kwalara a ƙasar

    Hukumomin lafiya a Sudan ta Kudu sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar kwalara a jihar Upper Nile ya kai 248.

    Ministan lafiya na ƙasar Byinj Ernest Apuktong ya ce cibiyoyin kwantar da marasa lafiya a yankin Malakal sun cika da marasa lafiya sakamakon ɓarkewar cutar.

    Gwamnatin ƙasar ta samu taimakon allurorin riga-kafi daga masu bayar da tallafi na duniya, yayin da take shirin fara gudanar da riga-kafin cutar ranar 15 ga watan Maris.

    Humumomin ƙasar su umarci jama'a da su kai rahoton duk wani mutum da suka ga alamar ya kamu da cutar, tare da umartar 'yan gudun hijira da su bar sansanonin da suka cika da jama'a ko suka rasa tsabtataccen ruwan sha a sansanin.

  3. Wani ɗan bindiga ya kashe mutum 10 a Mexico

    Akalla mutane 10 sun rasa ransu wasu da dama suka jikkata a Mexico bayan da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a wani gidan shan barasa inda ya yi harbin kai mai-uwa-da-wabi a kan mutanen da ke wajen.

    Lamarin ya faru ne a daren Asabar a tsakiyar jihar Guanajuato, jihar da ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi biyu ke fada akai don ƙwace ikonta.

    Watanni huɗu da suka gabata lamari makamancin wannan ya faru a yankin.

    Mambobin ƙungiyar 'yan daban nan ta Santa Rosa de Lima, sun bar wani saƙo a rubuce a wajen da lamarin ya faru inda suka zargi mai gidan barasan da goyon bayan ƙungiyar da suke adawa da ita ta Halisco New Generation cartel.

  4. Kwale-kwale ya kife da 'yan ci-rani a tekun Libya

    Kwale-kwale

    Asalin hoton, EPA

    Kusan mutum 30 ne ake fargabar sun ɓace bayan da wani kwale-kwale ɗauke da 'yan ci-rani ya kife a gaɓar ruwan Libya.

    Wata ƙungiyar agaji mai suna 'Alarm Phone' ta ce mutanen za su iya rayuwa muddin ƙasashen Turai ba su yanke shawarar barinsu su nutse ba.

    Ƙungiyar agajin ta 'Alarm Phone' ta ce ita ce ta farko da 'yanci ranin suka tuntuɓa a ranar Asabar inda suka shaida mata halin da suke ciki na cewa akwai yiwuwar jirgin nasu ya kife.

    To sai dai nan take ta sanar da mahukuntan Libya, to amma sai suka shaida mata cewa masu tsaron gaɓar tekun Italiya ne za su shirya duk wani aikin ceto.

    Masu tsaron gabar tekun Italiya sun ce jirgin ruwan na daidai yankin da ake iya ceto mutane idan sun nutse.

    To amma kuma kai wa ga waɗanda ke cikin kwale-kwalen zai zamo abu mai wuya saboda yanayi maras kyau.

  5. Maraba

    Jama'a barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, fatan kujn wari gari lafiya.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan kasancewa tare da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, amma za mu fi mayar da hankali ga Najeriya da sauran makwabtan ƙasashe.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawar kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu...