Gobara ta lalata shaguna a kasuwar Rimi da ke Kano

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Ƴan bindiga sun kashe mutum huɗu da mace mai ciki da sace wasu aƙalla 50 a jihar Niger

    Hoton ƴan bindiga

    Asalin hoton, AFP

    Ƴan ta'adda sun hallaka wata mata mai juna biyu na wata shida da wasu mutum huɗu a garin Agwa da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Naija.

    Haka kuma 'yan ta'addar sun sace kusan mutum 50 da raunata wasu a hare-haren da suka kai jiya Talata a yankin ƙaramar hukumar ta Rafi da kuma Wushishi kamar yadda jaridar Vanguard.

    Rahotanni sun ce maharan sun riƙa harbin kan mai-uwa-da-wabi a lokacin da suka kai farmakin, sai dai sojoji sun katse musu hanzari inda suka farmake su da hari ta sama.

    Duk da cewa sojojin sun kore su to amma ƴan bindigar sun yi awon-gaba da mutum aƙalla 50, yawanci yara da mata kamar yadda bayanai suka nuna.

    Al'ummar yankin da abin ya faru na nuna fargaba kan tsaronsu yayin da ake shirin zaɓen gwamna da ƴan majalisar dokokin jiha ranar Asabar.

    Kwamishinan tsaro da ayyukan jin-ƙai na jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar da kai harin zuwa lokacin bayyana labarin, ya ce ba su tantance yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

  2. An tuhumi malamar makaranta a Uganda da laifin alaƙar maɗigo

    Hoton mai fafutukar ƴancin masu neman jinsi ɗaya

    Asalin hoton, afp

    Bayanan hoto, Laifin neman jinsi ɗaya ka iya janyo wa mutum ɗaurin rai da rai a Uganda

    An tuhumi wata malamar makarantar boko mai shekara 43 a Uganda da laifin alaƙar maɗigo da wata mata a yankin gabashin ƙasar.

    An gurfanar da malamar tare da abokiyar alaƙar tata ne a wata kotun majistare a birnin Jinja da ke da nisan kilomita 80 daga babban birnin ƙasar Kampala a jiya Talata.

    Idan har aka same su da laifi za a iya yanke musu ɗaurin da ya kai na shekara bakwai a gidan yari.

    A yayin sauraren shari'ar matan sun ƙi amsa laifinsu saboda haka kotun ta tura su zaman waƙafi har zuwa ranar 14 ga watan nan na Maris.

    A ranar Asabar ne aka kama matan, kwana ɗaya bayan da iyayen ɗalibai a makarantar 'yan mata ta PMM Girls suka yi tururuwa zuwa makarantar domin fitar da ƴaƴansu saboda zargin cewa malamar na neman koya wa ɗaliban harakar neman jinsi ɗaya.

    Alaƙar neman jinsi ɗaya a Uganda laifi ne da ka iya sa a yi wa mutum ɗaurin rai da rai.

  3. Kotu ta hana bayar da jerin sunayen masu zaɓe a Zimbabwe

    kayan zaɓe

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotu a Zimbabwe ta hana bayar da kundin jerin sunayen masu zaɓe na kwamfuta bisa dalilai na tsaron ƙasa saboda zargin cewa za a iya yin maguɗi da zaɓe.

    Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan da wani ɗan majalisar dokoki na hamayya Allan Makharm ya shigar da ƙara bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta hana shi kwafin sunayen a watan Oktoba shekarar da ta wuce.

    Ɗan majalisar ya nemi a ba shi sunayen a kwamfuta mai makon na takarda saboda a cewarsa na takardar nada yawa kuma zai yi masa tsada sosa ya yi fito da su.

    A dangane da hakan ne babbar kotun Harare a jiya Talata ta yanke hukuncin cewa kundin sunayen muhimmin abu ne da ba za a baria fitar da shi ya bayyana ga jama'a ba ba tare da an yi la'akari da haɗarin sakin kundin ba ga tsaron ƙasa saboda za a iya yin maguɗi da shi.

    A watan Yuli ne za a yi babban zaɓe a Zimbabwe.

  4. Kotu za ta yanke hukunci kan duba muhimman kayayyakin zaɓe

    BVAS

    Asalin hoton, Twitter/INEC

    Nan gaba kaɗan ne yau a Najeriya ake sa ran kotu za ta yanke hukunci kan buƙatar da wasu jam'iyyun adawar ƙasar suka shigar gabanta suna neman a ba su damar duba kayayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su, ranar 25 ga watan jiya.

    'Yan takarar jam'iyyun adawa na PDP Atiku Abubakar da na LP Peter Obi ne, tare da zaɓaɓɓen shugaba ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne suka buƙaci kotun da ta tilasta wa INEC adana kayayyakin da aka gudanar da zaɓen da su gabanin shigar da ƙara don ƙalubalantar sakamakon zaɓen, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

    To sai dai hukumar zaɓen ƙasar ta buƙaci kotun da ta ba ta damar sake saita na'urorin BVAS gabanin zaɓen gwamnoni da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

    INEC ɗin dai ta sha alwashin yin amfani da na'urar BVAS a zaɓukan na gwamnoni da ke tafe a ƙarshen makon da muke ciki.

    Jam'iyyar PDP ta ce buƙatar da INEC ta gabatar na sake saita na'urorin, ta yi shi ne da nufin goge cikakkiyar shaidar sahihancin zaɓen da ke ƙunshe cikin na'urorin.

    Hukumar zaɓen ƙasar INEC dai ta sha suka, a gefe guda kuma ta sha yabo kan zaɓen shugaban ƙasar da ta gudanar, wanda masu sanya idanu suka ce yana cike da matsaloli na shirin hukumar da rashin gudanar da komai a bayyane.

  5. Rasha ta ce an shirya rahotonnin kai hari Nord Stream ne don ɗauke hankalin mutane

    Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya ce rahotannin da kafafen yaɗa labari suka yaɗa a bara kan harin da aka kai wa bututun Nord Stream an yi ne domin ɗauke hankalin mutane zuwa wani ɓangaren.

    Da yake hira da kamfanin dillancin labaran Rasha, Ria, Mr Peskov ya jaddada yarda da cewa jami'an Amurka sun yi amanna da cewa ana kai harin ba tare da cikakken bincike ba.

    Wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa, ya ce watakil ƙungiyoyin da ke mara wa Ukraine baya su ne suka kai hare-haren, yayin da binciken Amurka ya ce babu alamun hakan.

    A wani rahoton na daban da kafar yaɗa labaran Jamus ta bayyana, ta ce wani bincike ya nuna yadda akai amfani da wani kwale-kwale wajen dasa ababen fashewa a bututun.

    Sun yi zargin mallakin Ukraine ne. A ɓangare guda kuma jami'an Rasha sun sha kiran Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike kan hakan.

  6. Amurka na shirin haramta amfani da shafin TikTok a ƙasar

    Tiktok

    Fadar gwammnatin Amurka ta ce tana goyon-bayan wani ƙudirin doka na gamayar jam'iyyun siyasar ƙasar biyu da zai bai wa Shugaba Biden ƙarfin haramta amfanin da shafin TikTok na China da sauran wasu fasahohin ƙasashen ƙetare da za su kasance barazana ga tsaron ƙasar.

    Mataimaki na musamman kan harkar tsaron Fadar White House Jake Sullivan ya ce ƙudurin zai bai wa gwamnatin Amurka damar kare kanta daga kutsen wasu gwamnatocin.

    Ƙudirin daI ya samu amincewar gwamman 'yan jam'iyyun Democrats da Republican a majalisar dattijai.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da wannan shafi don sanin irin wainar da ake toyawa a sassan duniya, inda za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa a kan labaran da muke wallafawa

    Ku biyo mu...