Shugaban sojojin hayar Rasha 'Wagner' ya ce ana yi musu zagon-ƙasa a Bakhmut

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙungiyar sojojin hayar Rasha Wagner ya ce ba sa samun alburusan da suke buƙata daga Moscow, yayin da take ƙoƙarin karɓe iko da birnin Bakhmut.
Dakarun Rasha - da suka hadar da na Wagner da sojojin gwamnatin ƙasar - na ƙoƙarin ƙwace iko da birnin wanda ke gabashin Ukraine.
To sai dai shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi ƙorafi kan rashin alburushi yana mai cewa hakan na faruwa ne saboda watakila matakan da ake bi wajen samar da alburusan masu tsauri ne ko kuma ana yi musu ƙafar-ungulu ne kawai''.
Dangantaka tsakanin Wagner da Rasha na ƙara yin tsami.
ƙungiyar Wagner na da dubban dakaru da ke yaƙi a Ukraine - inda aka ɗauki wasunsu aiki kai-tseye daga gidajen yarin da suke ciki - Kuma suna taka muhimmiyar rawa a yaƙin.
A wani saƙo da ya wallafa ranar Lahadi Mista Prigozhin ya ce tun ranar 22 ga watan Fabrairu aka sanya hannu a kan takardar izinin sayen alburusan, inda aka yi tsammanin kai alburusan birnin kwana guda bayan nan.









