An dage tattara sakamakon zaben shugaban Najeriya zuwa ranar Litinin
Wannan shafi ne da yake kawo maku bayanai kan abubuwan da suke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Abdullahi Bello Diginza, Yusuf Yakasai and Nabeela Mukhtar Uba
Halin da ake ciki ya zuwa yanzu kan zaɓen Najeriya na 2023

- Wasu jihohi na ci gaba da gudanar da zaɓe.
- Wasu jihohin kuma na kirga kuri'u.
- INEC na bibiyar halin da ake ciki daga jihohi a ɗakinta na tattara bayanai domin sanar da mutane.
- INEC za ta buɗe zauren karɓar sakamakon zaɓe na ƙasa a yau Lahadi.
- INEC Ba ta fara sanar da sakamakon zaɓen ba ya zuwa yanzu.
Yadda ma'aikatan INEC ke tururuwar kai sakamakon zaɓe a Kano

Biyo bayan rashin kammala karɓar sakamakon zaɓe a jiya daga hannun ma'aikatan INEC na wucin gadi, a yau ake sa ran kammala karɓar dukkan sakamakon da aka kammala tattarawa daga rumfunan zaɓe.
An fuskanci jinkirin ne a wurare da dama sakamakon rashin isar kayan aiki rumfunan zaɓe a kan lokaci ko kuma gazawar na'urar BVAS wajen tantance masu kaɗa ƙuri'a.



Gwamnan Borno ya yi alƙawarin bai wa 'yan kasuwar da gobara ta shafa tallafin N1bn

Asalin hoton, Governor Borno/Facebook
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da bai wa 'yan kasuwar da gobara ta ƙona musu shaguna, tallafin naira biliyan ɗaya.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai Isa Gusau ya fitar, ta ce ya fitar da tallafin ne domin ragewa 'yan kasuwar raɗaɗi da suke ciki bayan ƙonewar shagunansu da kuma irin wahalhalu da za su iya shiga idan ba su samu wani tallafi ba a nan gaba.
Sanarwar ta ce za a kafa wani kwamiti don duba irin asarar da mutane suka yi da nufin taimaka musu da abin da ya kamata.
Har ila yau, gwamna Zulum ya kuma ce za a ɗauki matakai wajen ganin an kare afkuwar irin hakan a nan gaba saboda a baya an taɓa samun irin wannan gobara.
A don haka, ya yi kira ga a kwantar da hankula a yayin da gwamnati ke ƙoƙarin ganin an tallafa wa mutanen da abin ya shafa don rage musu raɗaɗi.
A jiya da daddare ne dai aka samu tashin gobarar a babbar kasuwa da ke birnin Maiduguri, inda ta yi ɓarnar da har yanzu ba a iya tantance girmar ta ba.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ku karɓi sakamakon zaɓe da hannu bibbiyu - Abdulsalami Abubakar
Bayanan bidiyo, Saurari bayanan tsohon shugaban Najeriya Abdussalami Abubukar kan zaɓen ƙasar Tsohon Shugaban Kasa Abdussalam Abubakar, wanda kuma ya jagoranci sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam'iyyun siyasa a ƙasar, ya bukaci 'yan Najeriya da su karɓi sakamakon zaɓen da INEC za ta sanar da hannu biyu-biyu, a yayin da ake fara tattara sakamako a matakin jihohi da na tarayya.
Jihohin da INEC ta ce za a ci gaba da zaɓe ranar Lahadi
Zaɓen Najeriya 2023: Rahotannin tarwatsa rumfunan zaɓe a wurare daban-daban

Rahotanni na tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya cikin lumana a yankuna daban-daban na Najeriya.
To amma akwai rahotannin tashin hakali a wasu jihohi kamar Legas da Kogi.
A Legas, bayanai sun ce an ƙwace akwatin zaɓe a wasu rumfuna, haka nan wasu sun koka game da cewa an hana su kaɗa ƙuri’a tare da korarsu daga rumfunan zaɓe.
A wani jawabi nasa, shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce masu tayar da zaune tsaye sun kai hari kan rumfunan zaɓe a jihohin Delta da Katsina tare da ƙwace na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a.
Amma lamarin ya kai ga ɗage zaɓe zuwa ranar Lahadi a rumfunan zaɓe 141 a jihar Bayelsa saboda irin waɗannan tashe-tashen hankali.
Haka nan Farfesa Yakubu ya ce wasu ƴan bindiga sun buɗe wuta kan masu aikin zaɓe a yankin Gwoza, inda suka raunata ma’aikata.


Jami'an zaɓe na jiran INEC ta fara karɓar sakamako a Adamawa
Bayani kan maƙala - Marubuci, Salihu Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Yola

Wasu malaman zaɓe sun koma babban ofishin hukumar zaɓe na INEC da ke Yola bayan shafe yinin ranar Asabar a bakin aiki a sassa daban-daban na jihar Adamawa.
Ma'aikata da kuma jami'an tsaro sun yi cirko-cirko a ofishin na INEC inda suke jiran a fara amsar takardun kaɗa kuri'a da kuma sauran kayayyakin zaɓe da suka mayar da su.
Ya zuwa safiyar Lahadi, babban ɗakin da hukumar zabe a Adamawa ta tanadar domin karɓar sakamakon zaɓen daga kananan hukumomi ya kasance fayau domin kuwa babu kowa cikinsa sai masu gadi.
Duk da yake a shelkwatar ta INEC ta jiha, ba a fara bayyana alƙaluman zaben ba, to amma an shafe tsawon dare ana tattara shi a ofisoshin hukumar zaɓe na wasu daga cikin ƙananan hukumomi 21 da ke jihar ta Adamawa.
Rahotanni dai sun nuna cewa zaɓen ya kammala a ko'ina a Adamawa ba tare da wata hatsaniya ba.
Ku kalli shirin safe na BBC Hausa na musamman kan zaɓen shugaban ƙasa a facebook
Gobara ta tashi a babbar kasuwar Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images
Wata gobara ta tashi a kasuwar da ake kira Monday Market da ke birnin Maiduguri.
Gobarar, wadda rahotanni suka ce ta tashi ne a daren jiya ta yi ɓarnar da har yanzu ba a tantance ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar birnin na Maiduguri sanadiyyar gobarar.
Wani ganau da BBC ta zanta da shi ya ce wutar na ci gaba da ci har zuwa safiyar Lahadi, inda mutane suka taru domin kai ɗauki.
Wani dan jarida da BBC ta tuntuɓa, Adamu Aliyu Ngulde ya ce mutane sun shiga cikin ruɗani saboda gobarar.

Asalin hoton, Getty Images
Ana samun jinkiri wurin tattara sakamakon zaɓe a wasu yankuna a Kano, Zahradden Lawan, Kano

Asalin hoton, Getty Images
A wasu wuraren an fara tattara sakamakon zaɓe, kamar na Sanatan Kano ta arewa wato a yankin Bichi.
Sai dai wasu wuraren kuma har zuwa safiyar Lahadi ana jira ne saboda sakamakon bai haɗu ba daga matakin cibiyoyi zuwa kananan hukumomi.
Haka shi ma sakamakon zaben shugaban ƙasa ana sa ran farawa a yau.
An samu jinkirin ne saboda jiya wasu wuraren ba a fara kada kuri'a a kan lokaci ba sannan na'urar tantance masu kada ƙuri'a ta VBAS ba ta yi aiki yadda ya kamata ba a wurare da dama sannan an ɗan samu yamutsi nan da can.
Yadda aka ci gaba da aikin zaɓe da daddare a Najeriya
Sanadiyyar rashin isar kayan zaɓe kan lokaci a Najeriya an ci gaba da gudanar da aiki cikin dare a wasu rumfunan zaɓe da ke faɗin Najeriya.
Ga hotunan yadda aka ci gaba da aikin tattara sakamakon zaɓen a unguwar Garki da ke Abuja.




Ana tattara sakamakon zaɓe a Najeriya

A Najeriya, kallo ya koma hukumar zabe, bayan kada kuri`a da miliyoyin al`ummar kasar suka yi a zaben shugaban kasa da na `yan majalisar dattawa da ta wakilai.
A jiya Asabar ne aka gudanar da zaben, wanda `yan takara daga jam`iyyun siyasa goma sha takwas suka fafata.
Yayin da aka kai cikin dare ana kada kuri'a a wasu mazabu, wasu kuma sai a yau Lahadi za a kammala zabe a rumfunan.
Sai dai a yanzu hankali ya karkata ga hedikwatar hukumar zaben kasar, wadda ke da alhakin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.
Barkanmu da warhaka!
Masu bibiyar mu a shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar Lahadi.
Yau dai kallo ya koma Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) inda ake tattarawa da sanar da sakamakon zaɓe.
Za mu kwashe yinin yau muna kawo maku duk abubuwan da ke faruwa daga ofishin hukumar zaɓen da kuma wasu sassa na Najeriya da ma duniya.
Yau ma Haruna Ibrahim Kakangi, da Buhari Muhammad Fagge da kuma Umar Mika'il ke bakin fama da asubahin yau.
Da fatan za ku kasance da mu a shafukanmu na intanet domin bibiyar duk abubuwan da ke faruwa.
