El-Rufai ya umarci ma'aikatun Gwamnatin Kaduna su tabbatar suna karɓar tsohon kuɗi

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Isra'ila ta kai hari ta sama zuwa Syria

    Birnin Damascus

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafafen yaa labaran Syria sun ce Isra'ila ta kai wani farmaki ta sama a babban birnin kasarta, Damascus.

    Sojojin Syria sun ce akallam mutum biyar ne suka mutu bayan harin na ranar Lahadi a birnin Damascus da da kewayansa.

    Jami'ai sun ce an lalata wani gini a tsakiyar unguwar Kafr Sousa da ke Damascus, tare da kashe fararen hula huɗu da soja ɗaya.

    Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Syrian Observatory for Human rights da ke da mazauni a Birntaniya ta ce samamen ya halaka mutum 15 ciki har da farar hula, ya kuma lalata gidaje a birnin.

    A cewarta, harin ya shafi wasu wurare da ke kusa da cibiyar al'adu ta Iran.

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ki cewa komai kan batun.

    Amma dai Isra'ila ta sha kai hare-hare kan wurare a Syria da ke da alaƙa da Iran da mayaƙan Hezbollah kuma ba ta cika ɗaukar nauyin hare-haren ba

  2. Amurka ta gargaɗi China kan bai wa Rasha tallafi a yakin Ukraine

    Biden Xi

    Asalin hoton, REUTERS/EPA

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ya gargaɗi China cewa za ta ɗandɗna kuɗarta idan har ta bai wa Rasha wani taimako a yaƙin da take a Ukraine.

    Mista Blinken ya bayyana haka ne a wata ganawa da babban jami'in diflomasiyyar China, Wang Yi a wani ɓangare na taron tsaro a Munich.

    Da yake magana daga bisani, Mista Blinken ya ce Amurka ta samu bayanai cewa China na duba yiwuwar samar wa Rasha makamai abin da ya ce zai janyo babbar matsala ga alaƙarsu.

    Jami'an biyu sun kuma yi magana kan balan-balan ɗin da aka kakkaɓo daga North Carolina a farkon watan nan.

    Mista Blinken ya gargaɗi China da kada ta sake ta sake keta sararin samaniyar Amurka yayin da Wang Yi kuma ya ce Amurka ta gurgunta alaƙarsu saboda matakin da ta ɗauka.

  3. Assalamu alaikum

    Abdullahi Bello Diginza ke muku barka da hutun ƙarshen mako, tare da fatan kasancewa tare da ku a daidai wannan lokaci.

    Ku kasance da mu a wannan shafi don sanin halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da sauran makwabtan ƙasashe.

    Ga kuma shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara