Bankwana
A nan za mu dakata sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye.
Abdullahi Bello Diginza
A nan za mu dakata sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.

Ma'aikatar Tsaron Birtaniya ta ce akwai yiwuwar Rasha na amfani da sabon salo na leƙen asiri kan dakarun Ukraine ta hanyar tura balambalan.
Cikin wani bayani kan tsaro, ma'aikatar tsaron ta ce Ukraine ta harbo balambalan shida da ke ɗauke da na'urorin aika bayanai da suka ratsa sararin samaniyar birnin Kyiv a ranar Laraba.
Ta ce ba mamaki Rasha na ƙoƙarin tilasta wa Ukraine ta kai rarraba makamanta masu linzami.
Kazalika, ta ce an ga irin wannan balambalan ɗin a yankin Dnipropetrovsk, da kuma ƙasar Moldova, abin da ya jawo aka rufe samaniyar ƙasar na ɗan lokaci a ranar Talata.

An fitar da Neymar daga fili a kan gadon marasa lafiya a wasan da Paris St Germain ta doke Lille 4-3 a gasar Ligue 1 ranar Lahadi.
Kylian Mbappe da Neymar suka fara ci wa PSG kwallaye daga baya Lille ta zura uku ta hannun Bafode Diakite da Jonathan David da kuma Jonathan Bamba.
Daga baya Mbappe ya kara na biyu, sannan Lionel Messi ya zura na hudu a ragar Lille a bugun tazara.
Neymar ya ji rauni a karawar a mintuna kadan da komawa zagaye na biyu, inda likitocin aikin gaggawa suka fitar da shi daga filin.
Ya nuna yana shan radadi, wanda ya rufe fuskarsa da hannayensa a lokacin da ake kokarin fitar da shi a kan gadon marasa lafiya a Parc des Prince.
PSG ta kawo karshen wasa uku a jere da aka doke ta.

Graham Potter ya ce Kyafti, Cesar Azpilicueta ya farfado, bayan da aka kaishi asibiti, sakamakon rauni a karawa da Southampton ranar Asabar.
Azpilicueta ya fadi kasa baya motsi, bayan Sekou Mara ya doke shi da kafa a ka a gasar Premier a Stamford Bridge.
An hangi Mara na karkarwa yana tsammani raunin mai muni ne tare da wasu 'yan wasa, yayin da masu agajin gaggawa suka kai dauki da wuri.
An saka wa Azpilicueta na'urar taimakawa a yi nimfashi, kafin daga baya a fitar da shi daga fili, wanda ya suma.

Hukumomi a Turkiyya sun ce sun dakatar da ayyukan ceto a dukkan wuraren da girgizar ƙasa ta afku a ƙasar, ban da wuri biyu, yayin da ake fargabar ba za a sake ceto wasu da rai ba.
Tun daga safiyar Asabar ba a sake samun wani da rai ba daga ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe.
An ci gaba da aikin neman masu rai a wuraren da lamarin ya fi ƙamari na Kahramanmaras da Htay, amma za a tsagaita aikin a can ɗin ma a yau Lahadi.
Da yake ziyara a yankin, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya sanar da ƙarin dala miliyan ɗari na tallafin ƙasarsa ga Turkiyya.
"Tun farkon lamarin mun ba da dala miliyan tamanin da biyar don tallfawa da ruwan sha, da abinci, da matsugunai, yau kuma muna sake ba da sanarwar ƙarin dala miliyan ɗari don tallafa wa waɗanda suka fi tsananin buƙata," a cewar Blinken.
Zuwa yanzu, an yi ƙiyasin cewa girgizar da abin da ya biyo baya sun kashe mutum fiye da dubu arba'in da shida a Turkiyya da Syriya.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan bayan Brazil Marcelo ya soke kwantaraginsa da kungiyar ƙwallon ƙafa wata biyar bayan komawarsa.
A baya rahotanni na cewa ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara daya a watan Satumba, da kuma zaɓin tsawaitawa na shekara daya.
Dan wasan mai shekara 34 ya bugawa ƙungiyar wasa 10 ya kuma ci kwallo uku a duka wasannin da ya buga.
"Na yi zaman da ba zan taɓa mantawa da shi ba a Girka. Garin Piraeus da mutanensa na cikin zuciyata," makar yadda ya wallafa a zuciyarsa.

Asalin hoton, GIL WIZEN/WPY
Masu bincike a Kenya sun gano wani nau'in sauro da aka fi sani a Kudancin Asiya, kuma ba ya jin maganin feshin da ake amfani da shi a Afirka.
Sauron wanda aka fara gano shi shekara goma da ta wuce a ƙasar Djibouti, yanzu ya karaɗe ƙasashen Habasha da Sudan da Somaliya da kuma Nijeriya.
Ƙwararru a fannin lafiya na gargaɗin cewa, sauron yana iya janyo ƙaruwar masu fama da zazzaɓin cizon sauro.
Ayarin ƙwararru daga Cibiyar Binciken aikin Likitanci ta Kenya ta shaida sauron, wanda ya fi rayuwa a cikin birane, mai suna Anopheles Stephensi, a lokacin wani aikin lura da kai-komo da aka saba lokaci-lokaci cikin yankin Marsabit na arewacin Kenya.
Alƙaluma daga asibitoci a can, sun kuma nuna ƙaruwar masu fama da zazzaɓin cizon sauro duk da yake yanzu ba lokaci ne da aka saba samun cutar ba. Saurayen yankin dai ba su cika samun kumari a yankuna masu fama da fari ba.
Sai dai wannan nau'in sauron mai mamaya yana iya kai labari a yanayi irin na rani da ma na damuna, kuma yana iya ƙyanƙyasa a ko'ina.
A wasu ƙasashen, an samu tsutsar da sauron ya ƙyanƙyashe a mazuban ruwa cikin wasu birane.
Ƙwararru na nuna damuwa cewa yanzu sauro zai yi ta baza cutar zazzaɓi tsawon shekara maimakon lokaci-lokaci kamar yadda aka saba gani.
Zai kuma kasance abu mai wahala a iya kakkaɓe cutar zazzaɓin cizon sauro, wadda ta zama ɗaya daga cikin manyan cutukan da suka fi kashe ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar.

Asalin hoton, RFE
Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta yi wa mutum goma sha ɗaya bulala a fili, waɗanda suka haɗa da maza tara da mata biyu, a arewa maso gabashin ƙasar.
Dandazon mutane ne suka shaida lamarin, cikinsu har da jami'an gwamnatin Taliban ɗin.
Babbar kotun Shari'ar Musulunci ta ce ta kama su da laifin rashin tarbiyya da ayyukan da ba su dace ba. Wannan ne karon farko da aka gudanar da bulalar a lardin Badakhshan tun bayan da Taliban ta hau mulki wata takwas da suka wuce.
A wasu wuraren na faɗin ƙasar kuwa, an yi irin wannan hukunci sau fiye da ɗari biyu da hamsin.

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi nasa da ci uku babu ko ɗaya a kan abokiyar karawarta Leicester City a filin wasa na Old Trafford.
Marcos Rashford ne ya fara jefa kwallon farko a wasan a minti na 25 da fara wasan, kafin daga bisani ya ƙara ta biyu a minti na 56, wato bayan hutun rabin lokacin.
Sancho ne ya ƙara ta uku a minti na 61 wanda kuma da sakamakon ne ta kara zama daram a matsayi na uku na gasar Premier, da tazarar maki uku tsakaninta da City da ke ta biyu.
Maki biyar ne kacal tsakanin United ɗin da ke ta uku da Arsenal da ke ta ɗaya.
Rashford ya ci kwallo 23 cikin duka wasannin da ya bugawa United a wannan kakar.
Wannan ne wasa na 10 da United ta buga ba tare da an jefa mata ko kwallo daya ba a raga.

Gwamman mabiya addinin Kirista ne suka yi zanga-zanga a Delhi babban birnin Indiya kan abin da suka kira ƙaruwar hare-hare da ake kai musu.
Shugabannin Kirista a faɗin Indiya sun ce mabiya addinin, waɗanda ke cikin marasa rinjaye, na zaune cikin ɗarɗar.
Suka ce an samu hare-haren ƙiyayyya kan Kiristoci sau fiye da dubu ɗaya da ɗari ɗaya cikin shekara biyu da suka gabata, kuma suka yi kira ga hukumomi da su ba su kariya.
Masu kishin ƙabila da addinin Hindu na zargin Musulamai da Kiristoci da yin amfani da hanyoyin da suka ce ba su dace ba wajen sauya wa Indiyawa ra'ayi.
An sha ganin masu tsattsauran ra'ayin Hindu a bidiyo na kira a fili da a kai wa wasu mabiya addinai hari.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta ƙwace hodar ibilis da tabar wiwi, da wasu muggan ƙwayoyi da aka yi niyyar fitar da su zuwa Turai da wasu sassan na duniya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogiramn 58, da kuma tabar wiwi a filayen jiragen saman Abuja da Legas da kuma wasu wurare a ƙasar.

Asalin hoton, NDLEA/Twitter
Sanarwar ta ce jami'an hukumar sun kama wasu 'yan kasuwa uku da take zargi da hannu a yankin Ojo da ke Legas
Haka kuma hukumar ta ce ta kwato ƙwayoyin Tramadol miliyan 2,684,900 da wasu magunguna a lokacin samamen da ta gabatar a makon da ya gabata a faɗin ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Kaduna Govt.
Gwamantin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Malam Nasir El-Rufai ya umarci ma'aikatu da hukomin gwamnatin jihar da su tabbatar cewa hukumominsu da ke karɓar haraji sun ci gaba da karɓar tsoho da sabon kuɗi.
A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce za a yi hakan ne bisa umarnin Kotun Kolin ƙasar na ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
Haka kuma gwamnan ya ce dokokin jihar Kaduna sun haramta wa hukumomin gwamnatin jihar karɓar haraji kuɗi hannu.
Sai dai kawai hukumomin da gwamnatin jihar ta amincewa karɓar garin kuɗin, waɗanda su ma ya yi kira a gare su da su yi biyayya da hukuncin Kotun Kolin ƙasar.
Gwamna El-Rufai dai na daga cikin gwamnonin da jihohinsu suka kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Kolin ƙasar bisa matakin sauya fasalin kuɗin, tare da ƙalubalantar daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shirin namu na wannan makon ya amsa ɗinbim tambayoyi da kuka aiko mana game da dalilan da yake sanya wa a sauya fasalin kuɗi a ƙasa.
Dangane da wannan tambaya Raliya Zubairu ta tuntuɓi Dakta Shamsudden Muhammad masanin tattalin arziki kuma malami a jami'ar bayero da ke Kano a Najeriya.

Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarkashin jam’iyyar NNPP Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi mamakin yadda ya ga wasu gwamnonin APC ke zagi ko sukar shugaban ƙasar kan sauyin kuɗi.
A wani sako da ɗan takarar ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce bai taɓa tunanin cewa za a kai matakin da wasu daga cikin gwamnonin za su fito su riƙa zagin shugaba Buhari ba.
‘’Haƙiƙa na yi mamakin yadda waɗannan abubuwa suke faruwa, kuma abin sai ya ba ka mamakin me ke damunsu?’’
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce watakila kuma maganar EFCC - cewa wasu daga cikinsu sun ɓoye biliyoyin kuɗi a gidajensu- haka take.
‘’Dan haka wannan tsari da aka zo da shi, zai mayar da biliyoyin kuɗin da suka sace tamkar yayi ko takardu marasa amfani, ina ga wannan shi ne dalilin da ya sa suka fusata’’, in ji Kwankwaso
Ya ƙara da cewa gwamnonin ba suna yi ne don ƙaunar talakawansu ba, domin kuwa a cewarsa babu wani dalili ko hujjar da suka nuna cewa suna ƙaunar talakawan nasu.
Kwankwaso ya kuma ce jam’iyyarsa za ta taimaka wa gwamnatin tarayya musamman a ranar zaɓe wajen sanya idanu domin taimaka wa EFCC da ‘yan sanda da sauran hukumomi wajen fallasa masu amfani da kuɗi domin sayen ƙuri’a.
A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo
A yau mun kawo muku labarin Kaikayi wanda Hannatu Mahmud birnin Yero Kaduna, mazauniyar unguwar Dalladin Nasidi da ke birnin Kano ta rubuta, Aisha Sherrif Baffa kuma ta karanta

Asalin hoton, Getty Images
Nan gaba kaɗan ne a yau za a mayar da gawar ɗan wasan Ghana Christian Atsu zuwa gida daga Turkiyya inda ya mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa wani yanki na ƙasar.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar ta ce gwamnatin ƙasar na gudanar da shirye-shirye domin tarbar gawar ɗan wasan.
Ana sa ran isar gawar zuwa ƙasar da misalin ƙarfe 7:40 na maraicen ƙasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gawar Atsu za ta isa Ghana ne a jirgin Turkish airlines tare da rakiyar jakadan Ghana a Turkiyya da kuma iyalan ɗan wasan.
Sanarwar ta ce gwamantin ƙasar tare da hukumar wasannin ƙasar ne za su tarbi gawar a filin saukar jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa da ke Kotoka.
Daga ƙarshe sanarwar ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan ɗan wasan tare da addu'ar neman gafara a gare shi.
Atsu dai ya rasu ne sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa Turkiyya da Syria kusan makonni biyu da suka gabata.
A ranar Asabar ne wakilin ɗan wasan ya bayyana gano gawarsa a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansa kwaniki 13 bayan afkuwar girgizar ƙasar.
Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle.

Asalin hoton, Ghana Foreign ministry

Asalin hoton, TWITTER/@JIDESANWOOLU
Gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga jama'ar jihar da su kwantar da hankulansu kan fusatar da suka yi dangane da wahalhalun ƙarancin kuɗi da ake fuskanta a ƙasar.
Gwamnan ya yi wannan kira ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke Marina, kan matsalar da ake ciki ta sauyin kuɗi a ƙasar.
Sanwo-Olu ya umarci mazauna jihar da su kauce wa duk wani tashin hankali, da zanga-zanga da ƙone-ƙone yana mai cewa hakan ba zai kawo mafita ga matsala ko wahalhalun da ake ciki ba
Ya ce “Ina mai jinjina a gare ku mutanen Legas dangane da haƙuri da juriya da kuka nuna a cikin wannan hali da ake ciki na tsaka-mai-wuya''.
“yan uwana al'ummar Legas, ina kira da tattausar murya a gare ku, a matsayina na gwamnanku, dan Allah ku kwantar da hankula a wannan lokaci, ku guji duk wani abu da zai tayar da hankali da zanga-zanga da kuma ƙone-ƙonea faɗin jiharmu'', in ji gamnan.
“Duk da wahalhalun da kowa ke ciki, tashin hankali ba zai zame mana mafita ba, duka mun sani cewa akwai mutanen da ke son yin amfani da tashe-tashen hankulan ta hanyar yin kalaman da ke tunzura jama'a''
''Kuma duk suna yin wannan ne da nufin hana ku damar kaɗa ƙuri'unku a zaɓen shugaban ƙasa, ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki, dan haka kada ku ba su dama su cimma manufarsu,''in ji Sanwo-Olu.
gwamnan ya ci gaba da cewa ba adalci ba ne kai hari kan dukiyoyin gwamnati da na al'umma.
A ranar Juma'a ne dai aka samu rahotonnin da ke cewa wasu fusatatun matasa sun toshe wasu titunan birnin Legas tare da ƙona tayoyi, sakamakon fusatar da suka yi kan ƙarancin takardun naira a ƙasar.

Asalin hoton, EFCC
Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC ta gano ƙarin naira miliyan 900 na hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasar wato NHIS.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato mai magana da yawon hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren na bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mista Uwujaren, ya yi zargin cewa kuɗin wani ɓangare ne da wasu bankunan ƙasar suka riƙe tun 2015 suka ƙi sanya wa a asusun hukumar Inshorar Lafiyar ƙasar wato NHIS.
Ya ƙara da cewa a yanzu an tura kuɗin zuwa asusun na NHIS.
Ya ci gaba da cewa a ranar 10 ga watan Fabrairun 2022, hukumarsu ta EFCC ta sakar wa NHIS ɗin naira biliyan 1.5 da ta kwato daga bankunan.
Haka kuma a ranar 5 ga watan Agustan 2022, EFCC ta ƙara sakar wa NHIS naira biliyan 1.4
A baya dai babban sakataren hukumar NHIS Farfesa Muhammad Nasir Sambo, ya sha yabawa da ƙwazon hukumar ta EFCC wajen taimaka wa NHIS ƙwato kuɗadenta da suka maƙale a wasu bankunan kasuwancin ƙasar.

Gwamnan jihar gombe Alhaji Inuwa Yayaya ya ce yana neman wa'adi na biyu ne domin karasa ayyukan raya ƙasa da ya fara aiwatarwa a jihar Gombe
A tattaunawarsa da BBC gwamnan ya ce shi da jam'iyyarsa sun cika kashi 85 na alƙawuran da ya ɗaukar wa al'ummar jihar
Gwamnan ya kuma ce duk da raunin tattalin arziki da annobar korona ta kawo, ya samu nasarar gudanar da wasu manyan ayyuka a jihar

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sandan jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya ta ce jami'anta sun samu nasarar kama wasu gawartatun 'yan fashi da makami, waɗanda ke ƙoƙarin guduwa bayan sun aikata fashin.
A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Benjamin Hundeyin, ya fitar ranar Asabar ya ce rundunar ta kama waɗanda ake zargin bayan da ta samu bayanan da ke cewa suna aikata fashi a kan haryar Ibeju zuwa Lekki.
Sanarwar ta ce bayan kama 'yan fashi , an kuma kwato ƙananan bindigogi guda biyu, da kwanson zuba alburusai maƙare da alburusan , da manyan wayoyin hannu guda biyu.
Mista Hundeyin ya ce bayan fara gudanar da bincike ne kuma aka gano mutumin da ke sayar musu da makaman.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ya ce mutanen biyu, sun amsa cewa sun daɗe suna aikata fashi a wannan wuri, ya kuma ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.