An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ranar Masoya: Hukumar yaki da AIDS a Najeriya ta shawarci matasa su guji wuce gona da iri

    Hoton alamar soyayya

    Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta Najeriya ta gargadi matasa da su gu ji sharholiyar da za ta iya kai su ga hadarin kamuwa da cutar.

    Shugaban hukumar da ake kira NACA a takaice, Gambo Aliyu, shi ne ya yi gargadin ga jama'a musamman matasa, a jiya Litinin.

    A sakonsa na ranar masoya da ake kira Valentine's Day na wannan shekara, shugaban ya bukaci 'yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci su yi gwaji domin sanin matsayinsu dangane da cutar ta HIV/AIDS

    Aliyu ya shawarci matasa da su yi bikin cikin nuna so da kauna da kare masoyansu daga duk wani abu da zai iya cutar da su, sannan su guji aikata abin da zai iya kai su ga kamuwa da cuta mai karya garkuwari jiki da sauran cutuka na jima'i.

    Shugaban ya ce, a wannan lokaci na bikin ranar ta masoya ta duniya ana samun yawan abubuwa barkatar na saduwa da sauran dabi'u tsakanin maza da mata da kan iya kai su ga wani yanayi na nadama.

    A duk shekara rana irin ta yau 14 ga watan Fabarairu ake bikin Ranar Masoya a duniya, wadda ake kira Valentie's Day.

  2. Shugaban Tunisia na kama 'yan jarida da masu hamayya da gwamnatinsa

    Hoton shugaba kais na Tunisia

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaba Kais Saied ya ce matakin na kare fadawar kasar cikin rikici ne

    'Yan sanda a Tunisia sun kama shugaban wani gidan rediyo a rana ta uku na kamen 'yan siyasa da masu fafutika.

    Wakiliyar BBC ta ce, Mahukunta sun kai sumame gidan Noureddine Boutar, na tashar Mosaique FM, da ke yawaita watsa shirye-shirye da ke caccakar shugaban kasar Kais Saied.

    Tun ranar Asabar, 'yan sanda suka kama wani hamshakin ɗan kasuwa, Kamal Eltaief, da fitaccen ɗan siyasa, Khayam Turki, da wani jigo a jam'iyyar hamayya, da wasu alkalai biyu da tsohon jami'in diflomasiyya.

    Yayin da ake nuna damuwa kan 'yancin siyasa, Shugaba Kais Saied ya kare matakinsa, da ya ce ya yi daidai da doka, kuma hakan yana da amfani domin kare Tunisia daga faɗawa cikin rikici.

  3. Sarkin Musulmi ya bukaci Shugaba Buhari ya dau mataki kan batun sauyin kudi

    Hoton Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar

    Asalin hoton, DAULAR USMANIYYA

    Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama'a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kauce wa bore.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sultan din ya nuna takaicinsa a jiya Litinin kan lamarin inda ya nuna damuwa kan yadda jama'a suka fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda canjin kudin.

    Matsalar sauytin kudin ta kara tsananta a tsakanin jama'a bayan da rahotanni suka nuna cewa bakuna sun daina ansar tsoffin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

    A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Kolin kasar ta hana Babban bankin kasar aiwatar da tsarinsa na hana amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu, har sai ta yanke hukunci a kasar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar a kan lamarin.

    A gobe Laraba ne Kotun Kolin ta ce za ta yanke hukunci a kan karar wadda gwamnonin jihohin uku suka shigar.

    Jihohin Kano da Naija da Ekiti da kuma Ondo suma sun bi sahun jihohin uku inda suka shigar da kara a gaban kotun kolin kan batun sauyin kudin.

  4. Cutar mashako ta kama mutum 216 ta hallaka 40 a Najeriya

    Hoton allura

    Asalin hoton, Getty Images

    Cibiyar yaki da cututtuka ta najeriya ta tabbatar da cewa mutum 216 ne cutar mashako (diphtheria) ta kama a jihohin Kano da Yobe da Lagos da kuma Osun.

    Sannan kuma zuwa yanzu kamar yadda bayanan hukumar suka nuna cutar ta kashe mutum 40 a jihohin Kano da Lagos.

    Daga cikin mutanen da suka rasu Kano tana da 38 yayin da Lagos take da biyu, in ji hukumar.

    Haka kuma hukumar ta ce mutanen da suka kamu da rashin lafiya wadanda ake ganin ko cutar ce suma ta kama su yanzu sun kai 523 a jihohi biyar.

    Jihohin kuwa su ne Kano da Yobe da Katsina da Lagos da kuma Osun.

    Shugaban kwamitin kwararru da ke yaki da cutar ta mashako a hukumar ta NCDC, Dr Bola Lawal, shi ne ya gabatar da wadannan bayanai a wani taro ta intanet a jiya Litinin.

    Dr Lawal ya ce hukumar ta tashi tsaye wajen taimaka wa kwararrun da ke aikin yaki da cutar a jihohin da ta bayyana na Kano da Katsina da Yobe da Lagos da kuma Osun.

  5. Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata, Muhammad Annur Muhammad ne zai kasance da ku a wannan shafi da ke kawo muku labarai kai tsaye, daga yanzu zuwa wani lokaci.

    Mu shashe baki da wannan karin maganar, ''Idan Allah Ya kawo makashinka sai kuma Ya kawo macecinka''