Dole Isra'ilawa su kaucewa ɗaukar doka a hannu - Netanyahu

Wani Bafalasdine ya bindige yahudawan Isra'ila a harabar wajen bautarsu da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye, lokacin da yahudawan suka taru domin gudanar da ibadarsu.
Nan take dai 'yan sandan Isra'ila suka kashe dan bindigar.
A wani jawabi da ya gabatar a talabiji bayan faruwar al'amarin, Firaminista Benjamin Netanyahu ya umarci 'yan Isra'ila su kaucewa daukan doka a hannunsu.
Netanyahu ya ce yanayi ne irinsa mafi muni a tsawon shekaru, sai dai Yana mai jadada musu cewa gwamnatinsa za ta sanar da matakan gaggawa na martani.
Mayakan Falasdinu sun yi murnar kai wannan hari, sai dai ba su bayyana ko akwai hannusu a harin ba.
