'Yan jarida a Kamaru na neman kariya saboda yawan kashe su da ake yi

'Yan jarida a Kamaru sun yi kira da a ƙara basu kariya biyo bayan kisan da aka yi wa abokin aikinsu Martinez Zogo, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati.
An tsinci gawar Mista Zogo wadda aka yi kaca-kaca da ita a kusa da Yawunde babban birnin ƙasar, kwana biyar bayan wasu mutane da ba a sani ba sun sace shi.
Gabanin mutuwarsa, ya yi barazanar zai fasa kwai game da cin hantsi a gwamnatence.
Kungiyar 'yan jarida ta Reporters Without Bordersta yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan wannan kisa, inda suka kira kasar da "ramin kabari ga 'yancin 'yan jarida".




