Yadda ta kaya a muhawarar 'yan takarar gwamna na jihar Kano

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Yan takara za su gabatar da kansu tare da manufofinsu

    'Yan takara za su gabatar da kansu tare da manufofinsu kowannensu

    muhawar
  2. 'Yan takarar sun hallara

    Tuni 'yan takara biyar na gwamnan jihar Kano, da za su fafata a wannan muhawara suka hallara a ɗakin gabatar da muhawarar domin fara muhawarar kamar yadda aka tsara.

    takara
  3. Tuni mahalarta suka fara isa ɗakin da za a gudanar da Muhawarar

    baƙi
    baƙi
    baƙi
    baƙi
  4. Yadda ma'aikatan BBC ke shirye-shiryen fara muhawarar

    shiri
    shiri
    shiri
    shiri
  5. Wanda zai jagoranci muhawarar

    Ibrahim Isa

    Ibrahim Isa na sashen Hausa na BBC ne zai jagoranci wannan muhawara wadda za a yada kai tseye a shafukan sada zumunta na BBCHausa da shafinmu na internet.

    Haka kuma za yaa muhawarar kai-tseye a wasu tasoshin FM da gidajen Talbijin a jihar ta Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya

    bbc
  6. 'Yan takarar da za su fafata a muhawarar

    Muhawara

    Za a yi muhawarar ne tsakanin 'yan takarar gwamna biyar a jihar wadda ta fi kowacce jiha yawan al'umma a faɗin kasar.

    'Yan takarar da za su fafata a wannan muhawara sun haɗar da Nasiru Yusuf Gawuna mataimakin gwamnan jihar kuma ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

    Sai kuma Sha'aban Ibrahim Sharada ɗan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni, wanda kuma ke takarar kujerar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar ADP.

    Sai kuma Abba Kabir Yusuf, wanda kuma ke takarar kujerar gwamnan ƙarƙashin inuwar jam'iyyara jam'iyyar NNPP.

    Sai Mohammed Sani Abacha wanda shi ma ke takarar kujerar gwamnan jihar ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

    Sai kuma Salihu Tanko Yakasai wanda shi ma ke takarar kujerar ta gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PRP

  7. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Kamar yadda muka alƙawarta muku a yau za mu kawo muku muhawarar 'yan takarar gwamna a jihar Kano kai-tseye a shafukanmu na sada zumunta da ma shafinmu na YouTube, da kuma wannan shafi namu na internet.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke tare da ku a wannan shafi na kai-tseye, domin kawo muku yadda muhawarar ke kasancewa.

    Haka kuma kuna iya bin mu a shafukanmu na BBCHausa Facebook da YouTube, domin kallon yadda muhawarar za ta kasance kai-tseye.

    Ku biyo mu....

    Diginza

    Asalin hoton, Diginza