A Najeriya, `yan majakisar dattawa da ta
wakilai sun zartar da kasafin kudin kasar na badi da aka kiyasta
zai ci naira tiriliyon kusan ashirin da biyu.
'Yan majalisar sun yi karin naira
tiriliyon Daya da doriya a kan adadin kudin da bangaren zartarwa ya tura
musu. Kazalika sun amince da wata kwarya-kwaryar kasafin kudi, har suka kara
wa`adin aiwatar da kasafin kudin wannan shekara mai karewa zuwa watan Maris din
badi.
`Yan majalisar sun bayyana cewa sun amince da kasafin
kudin ne bayan sun yi nazarinsa ciki da bai, kana suka zartar da shi, har ma
suka yi kari a wuraren da suka dace kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su
damar yi.
Senata Barau Jibrin wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na
majalisar dattawan Najeriya ya shaidawa BBC cewa; ''Daman kudirinmu shi ne mu tabbatar an kammala kasafin kudi a kowacce karshen shekara kafin mu tafi hutun sabuwar shekara, yadda da zarrar an dawo za a fara amfani da shi.
Akwai abubuwan da ya kamata a tanada, ko ma an yi tanadin amma bai wadatar ba, misali kudin da aka bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC dan haka an kara mata kudade.
Sai bangaren jami'an tsaro musamman sojojin ruwa da na kasa da sauransu, su ma an kara musu an kawo tiriliyan 20 da doriya, amma karin da aka yi ya sa kasafin ya haura naira tiriliyan 21.''
Su ma `yan majalisar wakilai sun zartar da kasafin kudin,
inda baki ya zo daya da na `yan majalisar dattawa.Baya ga kudin-shiga da gwamnati ke sa ran samu, sai an hada
da rance za a cike gibin kasafin kudi.
Kazalika a yayin zaman zartar da kasafin kudin ne `yan
majalisar suka zartar da wata kwarya-kwaryar kasafin kudi ta wannan shekara mai
karewa da ta kai naira biliyon dari takwas da `yan kai don aiwatar da wasu
ayyuka na gaggawa sakamakon ta`adin da ambaliyar ruwa ta yi, kudin da shi ma
aka ce za a samo shi ne ta hanyar karbar rance.
Kodayake wasu daga cikin `yan majalisar ba su goyi bayan
bijiro da kwarya-kwaryar kasafin kudin a irin wanan lokacin ba, ciki har da Senata Mohammed
Ali Ndume da ya fito daga jihar Borno.
Tun a makon jiya ne `yan majalisar suka yi yunkurin
zartar da kasafin amma lamarin ya gagara, sakamakon rashin daidaita wasu
alkaluma daga wasu hukumomin gwamnati.