Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za a mayar da dakin otel din da Messi ya sauka gidan adana kayan tarihi a Qatar

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Qatar za ta kyautar wa Lebanon motocin da aka yi amfani da su a gasar Kofin Duniya

    Qatar za ta kyautar da manyan motocin ɗaukar fasinja da aka yi amfani da su a gasar Kofin Duniya ga ƙasar Lebanon domin taimaka wa harkokin sufuri a ƙasar, kamar yadda kafar yada labaran Lebanon ta ruwaito.

    Wasu majiyoyi sun ce firaministan ƙasar Najib Mikati ya tattauna batun da jami'an ƙasar Qatar bayan kammala gasar Kofin Duniya.

    Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Qatar suka bayyana aniyarsu ta kyautar da wasu kayayyakin da ta yi amfani da su a lokacin gasar Kofin Duniya ga wasu ƙasashe masu tasowa.

    Cikin abubuwan da Qatar ɗin ta ce za ta kyautar har da manyan filayen wasanni da aka yi amfani da su a lokacin gasar, da kujerun da ke filayen wasan, baya ga manyan motocin 1,000 da aka yi amfani da su wajen yin zirga-zirga da 'yan kallo kyauta a lokacin gasar.

  2. Fiye da mutum 50 ne suka mutu a rikicin ƙabilanci a Sudan ta Kudu

    Fiye da mutum 50 ne suka mutu wasu da yawa suka jikkata a wani faɗan ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin 'yan ƙabilar Jonglei da yankin Pibor a gabashin Sudan ta Kudu, kamar yadda wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a ƙasar ta ruwaito.

    Kafar yada labaran ta ambato ministan yaɗa labaran yankin na Pibor Abraham Kelang Jiji na cewa mutum 56 ne suka mutu wasu ƙarin 17 suka jikkata a faɗan da ya auku a garin Gumuruk da ke kudancin ƙasar.

    Mista Jiji ya ƙara da cewa mafi yawan waɗanda suka mutu a rikicin matasa ne.

    Rikicin na zuwa ne kwanaki bayan da majalisar Dinkin Duniya ta bayar da gargaɗi game da ɓarkewar rikici a kasar bayan da Matasa masu dauke da makamai da ƙungiyar tayar da ƙayar baya suka ayyana ɗauka sojoji domin shirin ƙaddamar da hare-hare a yankunan biyu.

    Faɗan ƙabilanci ya yi sanadin kashe ɗaruruwan mutane tare da raba dubbai da muhallansu a yankuna daban-daban na Sudan ta Kudu a wannan shekarar.

  3. Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar ga Najeriya domin taimaka wa waɗanda ambaliya ta shafa

    Ƙasar Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar domin taimaka wa yankunan da ambaliya ruwa ta shafa a faɗin Najeriya.

    Tallafin ƙari ne kan dala miliyan ɗaya da hukumar bayar da tallafi ta ƙasar Amurka ta bayar domin taimaka wa waɗanda ambaliya ruwa ta shafa a ƙasar.

    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya sauka a daminar bana ya shafi fiye da mutum miliyan 4.4 a faɗin ƙasar, lamarin da ya raba mutum akalla miliyan 2.4 da muhallansu, tare da lalata dubban gidaje. Inda kuma sama da mutum 660 suka rasa rayukansu.

  4. Maraba

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sunana Abdullahi Bello kuma ni zan ja ragamar shafin a daidai wannan lokaci.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta