Za a mayar da dakin otel din da Messi ya sauka gidan adana kayan tarihi a Qatar
Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Rufewa, Daga Badriyya Tijjani Kalarawi
Asalin hoton, kalarawi84
Ana muka kawo karshen shafin da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kasashen makofta har da wasu kasahen duniya.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da wasu labarai da rahotannin, kafin zuwan lokacin za ku iya ziyartar shafinmu na intanet bbchausa.com, domin karanta wasu karin labaran.
Za ku iya zuwa shafukan mu na sada zumunta da muhawara na BBCHausa facebook, da Twitter da Instagram, da shafinmu na Youtube domin kallon bidiyo iri daban-daban.
Amma yanzu, Badriyya Tijjani Kalarawi ke muku fatan alkhairi daga nan sashen Hausa na BBC.
Mu kwana lafiya.
Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta bara kan karin kudin makaranta, Daga Zahraddeen Lawal a Kano
Asalin hoton, OTHERS
Bayanan hoto, Daliban jami'o'in gwamnatin Najeriya sun shafe watanni su na yajin aiki
A Najeriya iyaye sun fara kokawa da karin kudin makaranta da wasu jami’oin kasar suka yi wasu
kuma ke shirin yi, ita kuwa kungiyar daliban jami’oin kasar ta ce bazata sabu ba.
Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki
zai kasance wata babbar matsala ga daliban da kuma iyayensu.
Tuni kungiyar ta ce
ka kafa wani kwamiti a shiyoyin Najeriya don su zauna da jami’o’in game da
yadda za a shawo kan al’amarin.
Sanarwar da wasu jami’o’in
Najeriya suka fitar cewa daga zangon karatu na gaba a kwana da sanin an kara
kudin makaranta, ya yi matukar jefa wasu iyayen da dalibai cikin zukumi da
jimami, saboda a cewarsu dama da kyar da jimibin goshi suke biyan kudin
makarantar na yanzu.
Wani uba ya shaidawa BBC cewa ya kadu matuka da 'yar shi ta kawo mishi takardar batun karin kudin jami'ar.
'''Ya ta da ke jami'ar gwamnati da ke Dutse a jihar Jigawa ta kawo min takardar kuma an rubanya kudin har sau biyu, gaskiya gwamnati ya kamata ta saurari kukan mutane, abinci ma na neman gagarar mutane.
Kullum su na dabbaka batun yin ilimi, to amma da alama wasu sai dai su hakura da karatun saboda ba su da hanyar biyan kudin karatun.''
Suma daliban sun ce sam-sam
wannan matakin bai yi dai-dai ba, inda suka kafa kwamitoci a shiyoyin Najeriya
don zama tare da samun matsaya da jami’o’in da suka kara kudin ko suke shirin
karawa.
Kungiyar malaman jami’oin ta
ASUU tace da ma ta san za a rina, saboda kudaden gudanarwa da jami’o’in suke
karba daga gwamnatin tarayya basa isa.
Bayanai na cewa tuni wasu
jami’oin suka kara kudin makarantar da fiye da kashi dari, inda karin zai fara
aiki a zangon karatu na gaba, sannan wasu da dama ciki har da jami’ar tarayya
da ke Dutsen jihar Jigawa suke kan tattauna yadda za su yi kari.
Majalisar dokokin Najeriya ta zartar da kasafin kudin shekarar 2023, Daga Ibrahim Isa a Abuja
Asalin hoton, @NGRSENATE
Bayanan hoto, Shugaba Buhari a zauren majalisa
A Najeriya, `yan majakisar dattawa da ta
wakilai sun zartar da kasafin kudin kasar na badi da aka kiyasta
zai ci naira tiriliyon kusan ashirin da biyu.
'Yan majalisar sun yi karin naira
tiriliyon Daya da doriya a kan adadin kudin da bangaren zartarwa ya tura
musu. Kazalika sun amince da wata kwarya-kwaryar kasafin kudi, har suka kara
wa`adin aiwatar da kasafin kudin wannan shekara mai karewa zuwa watan Maris din
badi.
`Yan majalisar sun bayyana cewa sun amince da kasafin
kudin ne bayan sun yi nazarinsa ciki da bai, kana suka zartar da shi, har ma
suka yi kari a wuraren da suka dace kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su
damar yi.
Senata Barau Jibrin wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na
majalisar dattawan Najeriya ya shaidawa BBC cewa; ''Daman kudirinmu shi ne mu tabbatar an kammala kasafin kudi a kowacce karshen shekara kafin mu tafi hutun sabuwar shekara, yadda da zarrar an dawo za a fara amfani da shi.
Akwai abubuwan da ya kamata a tanada, ko ma an yi tanadin amma bai wadatar ba, misali kudin da aka bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC dan haka an kara mata kudade.
Sai bangaren jami'an tsaro musamman sojojin ruwa da na kasa da sauransu, su ma an kara musu an kawo tiriliyan 20 da doriya, amma karin da aka yi ya sa kasafin ya haura naira tiriliyan 21.''
Su ma `yan majalisar wakilai sun zartar da kasafin kudin,
inda baki ya zo daya da na `yan majalisar dattawa.Baya ga kudin-shiga da gwamnati ke sa ran samu, sai an hada
da rance za a cike gibin kasafin kudi.
Kazalika a yayin zaman zartar da kasafin kudin ne `yan
majalisar suka zartar da wata kwarya-kwaryar kasafin kudi ta wannan shekara mai
karewa da ta kai naira biliyon dari takwas da `yan kai don aiwatar da wasu
ayyuka na gaggawa sakamakon ta`adin da ambaliyar ruwa ta yi, kudin da shi ma
aka ce za a samo shi ne ta hanyar karbar rance.
Kodayake wasu daga cikin `yan majalisar ba su goyi bayan
bijiro da kwarya-kwaryar kasafin kudin a irin wanan lokacin ba, ciki har da Senata Mohammed
Ali Ndume da ya fito daga jihar Borno.
Tun a makon jiya ne `yan majalisar suka yi yunkurin
zartar da kasafin amma lamarin ya gagara, sakamakon rashin daidaita wasu
alkaluma daga wasu hukumomin gwamnati.
Majalisar wakilan Amirka na son haramtawa mambobi amfani da TikTok
Asalin hoton, Getty Images
A hukumance an haramtawa 'yan majalisar wakilan Amirka amfani da manhajar Tiktok a duk wasu na'urori mallakin majalisar.
Jaridar Vanguard ta Najeriya ta rawaito cewa, an gabatar da kudurin doka na musamman kan manhajar da kuma ake sa ran haramcin zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
Vanguard ta ambato kamfanin dillancin labarai na Reuters na cewa babban jami'in majalisar wakilan Amirka da ba a bayyana sunansa ba na cewa, TikTok babbar barazana ce ga tsaron kasa, sannan ana bukatar cire manhajar daga wayoyin salula samfurin na zamani ko komai da ruwanka.
Mutane na amfani da manhajar TikTok domi yada abubuwan da ba su dace ba, ko da ya ke wasu na amfana da ita kan abubuwa da dama na rayuwa.
Masunci ya kwa biyu makale da karfen teku domin ya rayu
An gano wani masunci makale jikin karfen da ke nuna alama da ke tsakiyar teku, bayan da akai tunanin ya bata, bayan fadawa ruwa daga kwale-kwalen da ya ke ciki a Brazil.
David Soares, mai shekara 43, 'yan uwan shi masunta ne suka gano shi a tekun Atlantika kwanaki biyu, bayan tunanin ya bata a tekun.
Ya shaidawa kafafen yada barai cewa ya fado ne daga jirgin ruwan da ya ke kamun kifi daga ciki, sanna ya yi ninkaya zuwa karfen alamar da ke tsakiyar teken da ya makale har sama.
Likitoci dai sun yi gaggawa saya masa karin ruwa saboda yadda ya galabaita.
A ranar Kirsimati ne Mista Santos ya tafi tekun da ke birnin Rio de Janeiro domin kamun kfi amma ya hadu da wannan bala'i.
Jirgin Ethiopia ya koma jigila yankin Tigray da yaki ya daidaita
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tun fara yaki tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen yankin Tigray a shekarar 2021 aka dakatar da jigilar fasinja yankin
Kamfanin jirgin sama na Ethiopia, ya saanar da komawa jigilar jingin fasinja babban birnin yankin Tigray, watanni 18 da dakatar da hakan.
Shugaban kamfanin Mesfin Tasew ya shaidawa manema labarai cewa, jirgin zai dauko iyalai daga Mekelle bbban birnin yankin, domin sada su da 'yan uwa da abokan aikin da suka dade ba su hadu ba saboda yakin da yankin ke fama da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa hanyoyin sadarwa a tarho sun fara aiki.
Tun barkewa yaki a Tigray kafar sadarwa ta yanke daga yankin da sauran sassan Habasha da duniya baki daya.
AA ranar Litinin ne wakilan gwamnatin Habasha suka kai ziyara Mekelle domin tattauna yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban yankin Tigray Debretsion Gebremichae, ya sanar da cewa zaman lafiya ba zai tabbatu da dorewa ba har sai dakarun Eritrea da 'yan dabar Amhara da ke marawa sojin gwamnatin Habasha baya sun fice daga kasar baki daya.
Za a mayar da dakin otel din da Messi ya sauka gidan adana kayan tarihi a Qatar
Jamai'ar Qatar ta sanar da mayar da dakin otel din da Messi ya zauna, a yayin gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar, karamin gidan tarihi.
Dakin wanda Messi ya zauan da abokinsa kuma dan wasan Ajantina Sergio Aguero a karshen gasar, ya tashi daga dakin saukar baki a cewar kamfanin labarai ta Qatar.
Maimakon haka tuni shirye-shirye suka nuna za'a mayar da dakin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafan Faransa Paris Saint- Gernamain, don girmama dan wasan daga dalibai da bakin da zasu ziyarci karamin gidan ajiye tarihin.
Sun ce za'a bar dakin a yadda yake, kuma za a bar shi ga baki, amma ba za'a amince a zuna a cikin sa ba matsayin gida.
Daktaktan yada labaran jami'ar ta Qatar, Hitmi al Hitmi, ya ce dukkan kayan da su ke mallakin Messi ne zai zama abin tarhi ga dalibai da yaran kasar da ke tasowa nan gaba, don shaida nasarar da Messin ya samu a lokacin gasar kofin Duniya da aka yi a kasar.
Shugaban Nijar ya ƙaddamar da aikin cibiyar lantarki mai karfin Megawatts 22 a Damagaram
Shugaban Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya ƙaddamar da aikin cibiyar wutar lantarki mai karfin Megawatts
22 da aka gina a jihar Damagaram a yau.
A ranar 3 ga watan Augustn 2021 ne shugaban ya aza tubalin
fara gina wannan cibiya da aka ware wa kudin da suka haura CFA biliyan 66.
Baya ga Damagaram, jihohin Zinder da Maradi da Tahoua ma za su
ci gajiyar wannan tasha.
Hakan na cikin tsarinn Shugaba Bazoum na samar da isashen
makamashin da zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar.
Dusar ƙanƙara na zuba a wasu yankunan Saudiyya
Asalin hoton, Saudi Gazzette
Dusar kankarar ce ke sauka yanzu a saudiya. Dusar kankarar ta mamaye duwatsun Al-Lawz dake yankin Tabuk, tun ranar Talata, a cewar kamanin dillancin labaran Saudiya SPA.
Wuraren da kankarar ke zuba ya zama abun jan hankalin ga mazuna yankin da baki 'yan yawon bude idanu, da suka zo daga kasashe don shakatawa acikin dusar dake zuba.
Daraktan hukumar kula da yanayi a birnin Alenizi da ke arewacin Saudiya ya ce zubar dusar kankarar na baya rasa nasaba da dalilai guda biyu, a duwatsun Al-Lawz da sauran wasu yankuna da ke kusa da shi.
Asalin hoton, Saudi Gazzette
Asalin hoton, Saudi Gazzette
Amurka zata sanya dokoki kan matafiya da ga China kan Korona
Asalin hoton, EPA
Amurka na duba yiwuwar
sanya sababin dokokin kan cutar korona kan matafiyan daga China, bayan Beijing
ta sanar da sake bude iyakokinta a wata mai zuwa.
Hukumomi a Amurka sun ce saboda rashin sahihan bayanai kan korona, bayan samun aruwar wadan da suka kamu daga cutar da ake samu a China.
a ranar Laraba Italy ta sanar da shirin ta na san ya dokar da zata tilasta yin gwajin korona, bayan tsauraran matakai da aka zayyana a Japan, Malaysia, Taiwan and India.
Beijing ta ce ya kamata dokokin da wasu kashen ke sakawa kan korona, a ringa saka wadan ke da da alaƙa da gwajin "kimiya".
Tuni Hukumomi a Italiya, suka fara yiwa bakin da suka zo daga China gwajin korona.
Ƴan sanda Nijar sun bankaɗo gungun ƴan fashi masu ƙwace wa attajirai dukiya
A
yankin Matameye na jihar Damagaram ƴan sanda ne suka yi nasarar bankado wani
gungu na ƴan fashi da makami da ke kai wa masu kudi hare-hare suna ƙwace masu
kudi.
Sai dai babban daraktan ƴan sanda na
gundumar Matameye ya ce babban gungu ne mai mambobi a Matameye da Zinder, har da
wasu ma'aikatan banki biyu da ke bai wa ƴan fashin bayanai kan wadanda
suka kai ko suka ɗauko mayan kudi daga banki.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da ɗan sanda da ya kashe lauya a Legas
Asalin hoton, Nig.Police
Babban Sifeton 'yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin dakatar da mataimakin sufuritandan 'yan sanda Drambi Vandi, jami'in da ya harbe tare da kashe wata lauya mai suna Omobolanle Raheem a birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, a yayin da hukumar ke jiran cikakken rahoton binciken kisan.
A wata sanarwa da shalkwatar rundunar 'yan sandan da ke Abuja ta fitar, babban Sifetan ya ce dakatar da jami'in na daga cikin tsare-tsaren ladabtarwa na hukumar.
Babban Sifeton ya ƙara da cewa an dakarar da jami'in ne domin bayar da damar yin bincike cikin adalci ba tare da wata tangarɗa ba.
Haka kuma babban jami'in 'yan sandan ya sake nanata ƙudurin hukumar na barin doka ta yi aiki a kan kowa, tare da ƙara tabbatar wa da al'umma burin rundunar ƙarƙashin jagorancinsa na tabbatar da cewa an yi adalci game da batun kisan lauyar.
Mrs Omobolanle Raheem ta gamu da ajalinta ne a unguwar Ajah yayin da take kan hanyarta ta komawa gida daga addu’o’in zagayowar ranar ta Kirtimeti.
Lokaci ya yi da za a hukunta 'yan siyasa masu ci-da-addini - El-Rufai
Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Mallam Nasir El-Rufai ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta 'yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.
Rahotonni sun ambato gwaman na wannan maganar ranar Talata a lokacin bikin ƙaddamar da babban ofishin 'gidauniyar zaman lafiya da ci gaba' ta mai alfarma sarkin musulmi
El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini da su riƙa gudanar da addu'o'in samun ingantaccen zaɓe da samun zaman lafiya a fadin ƙasar.
Ya ce “Ina so na yi amfani da wannan damar na yi kira ga shugabanninmu da ke nan, masu girma sarakunan gargajiya da malamanmu da su ci gaba da yi wa ƙasarmu addu'o'in samun zaman lafiya da samun ingantaccen zaɓe, tare da yin addu'ar Allah ya zaɓa wa ƙasarmu shugabannin na-gari da za su haɗa kan ƙasar tare da ciyar da ita gaba''
''A matsayina na ɗan ƙasa, kuma gwamna sannan kuma musulmi bana jin daɗin yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci a matsayin makaminsu na yaƙin neman zaɓe'', in ji El-Rufai.
Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta waɗanda ke ƙoƙarin amfani da addinin a matsayin makamin yaƙin neman zabe.
Zaɓen 2023: Buhari ya umarci jami'an tsaro da su kasance 'yan ba-ruwanmu
Asalin hoton, others
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaron ƙasar da za su yi aiki da hukumar zaɓen ƙasar a lokacin zaɓukan 2023 da ke tafe da su kasance 'yan ba-ruwanmu, tare da nuna ƙwarewar aiki.
Sannan kuma su nesanta kansu daga duk abubuwan da za su kawo matsala ga ayyukansu.
Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga jami'an ne ranar Laraba a lokacin bikin ƙaddamar da rukunin gidajen jami'an hukumar tattara bayanan sirri a unguwar Idu da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Buhari ya umarci hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun kula da ayyukan rarraba tare da lura da muhimman kayayyakin zaɓe cikin nuna ƙwarewar aiki kamar yadda yake kunshe cikin dokokin hukumomin tsaron.
Majalisar dattawa ta amince da ƙaramin kasafin kuɗi da Buhari ya aike mata
Asalin hoton, @DRAHMADLAWAN
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙaramin kasafin kuɗi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya aike mata na naira biliyan 819.5
Majalisar ta amince da kasafin ranar Laraba, bayan da ta yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi wanda Sanata Barau Jibrin ya jagoranta.
Sanata Barau ya ce za a yi amfani da kuɗin ne wajen kammala wasu manyan ayyukan, ciki har da gyaran hanyoyi da madatsun ruwan da ambaliya ta lalata.
Ya ƙara da cewa za a samu kuɗin ne daga basussuka na cikin gida da gwamnatin tarayya za ta ciyo.
A cikin wasiƙarsa ta aike wa majalisar dokoki kasar kasafin kuɗin, shugaba Buhari ya ce ''ƙasar ta fuskanci mummunar ambaliya a wannan shekarar, wacce ta haddasa cinye gonaki a yayin da ake dab da girbe amfanin gona. Hakan kuma ka iya kawo matsalar karancin abinci a ƙasar''.
'Yan majalisa sun titsiye shugaban ASUU kan zargin cewa Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar
Asalin hoton, others
Wasu mambobin majalisar wakilan Najeriya sun titseye shugaban ƙungiyar malaman jami'o'in ƙasar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, kan wasu zarge-zarge da ya yi na cewa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar wajen jan hankalinta domin janyewa daga yajin aikin da ta shafe watanni tana yi.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa a wata hira da shugaban ASUUn ya yi da wata jarida a ƙasar ranar talata ya zargi Gbajabiamila da cewa ya yi amfani da yaudara wajen sanya ƙungiyar janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a watan Oktoba.
Ta hanyar rubutaccen alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta biya malaman duka albashin watannin da ta riƙe musu ba tare da ɓata lokaci ba.
Yayin da yake mayar da martani game da zargin na shugaban ASUU a Abuja, mai magana da yawun majalisar wakilan ƙasar Benjamin Okezie Kalu ya ce babu inda kakakin majalisar ya yi alƙawarin warware matsalar albashin da malaman ke bin gwamnatin tarayya bashi.
Inda ya ce majalisar wakilan ta taimaka ne kawai wajen kawo ƙarshen yajin aikin, ta hanyar yin ƙoƙari wajen inganta albashin malaman jami'o'in tare da taimakawa wajen samar da kuɗin inganta jami'o'in ƙasar.
Fafaroma Benedict yana cikin matsananciyar jinya - Fafaroma Francis
Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Francis ya ce tsohon fafaroman da ya gada wato fafaroma Benedict na cikin matsananciyar rashin lafiya, inda ya buƙaci masu ziyarar ibada a cocin Vatican da su sanya shi cikin addu'o'insu.
A shekarar 2013 ne dai tsohon fafaroman mai shekara 95, ya zama babban shugaban ɗarikar Katolika na farko da ya sauka daga muƙaminsa cikin shekarar 600, inda ya ce ya sauka daga muƙamin nasa ne saboda shekaru.
A ƙarshen huɗubar da ya gabatar wa mabiya a cocinsa ne dai fafaroma Fransis ya buƙace su da sanya tsohon fafaroman cikin addu'o'insu na ibada.
Daga baya ne kuma fadar vatican ta ce rashin lafiyar tsohon fafaroman ta tsananta.
A farkon wannan watan ne fafaroma fransis ya ce yana yawan ziyartar tsohon fafaroman domin duba lafiyarsa.
Hauhawar farashin abinci da faɗuwar darajar naira na shafar 'yan Najeriya - MDD
Asalin hoton, others
Bayanan hoto, MDD ta ce duniya ta fuskanci tsadar abinci mafi muni sau uku a wannan ƙarni
Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci da ƙaruwar farashin dala na shafar 'yan Najeriya da wasu ƙasashe masu tasowa.
Rahoton ya ce waɗannan al'amura biyu sun tilasta wa mutane da dama a ƙasashe masu tasowa daina yin wasu muhimman abubuwa, ciki har da rashin samun abin da za su ci, da tilasta wasu cire 'ya'yansu daga makarantu.
Rahoton wanda aka fitar cikin watan Disamba ya ce farashin abinci ya ƙaru a ko'ina, inda ya kai matakin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi, kamar yadda ƙungiyar kula da rikice-rikice ta duniya ta bayyana.
“Wannan barazana ce ga abinci a faɗin duniya, to amma matsalar ta fi ƙamarai ga ƙasashe masu tasowa da ke sayo abincin daga ƙasashen waje.
Kuma saɓanin matsalar abinci da aka fuskanta a baya, a yanzu ana fuskantar matsaloli biyu ne ciki kuwa har da batun tsadar kuɗin dala wanda da shi ne ake cinikayya tsakanin kasashe''.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa duniya ta fuskanci manyan matsalolin tashin farashin abinci guda uku a wannan ƙarni da muke ciki.
Duniya ta fuskanci tashin farashin abinci na farko a wannan ƙarni tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008, sai na biyu tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012, sai kuma na yanzu wanda annobar Korona da yaƙin Ukraine suka haddasa.
Gwamnatin tarayya za ta ƙara wa ma'aikata albashi - Ngige
Asalin hoton, others
Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Villa.
Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma'aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.
Da aka tambaye shi sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ''ƙwarai kuwa, wannan shi ne abin da nake faɗa cewa kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma'aikata ta ƙasar''.
“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin'', in ji ministan.
Kan batun albashin wata takwas da malaman jami'o'in ƙasar ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.
Jiragen Ethiopian Air za su koma sauka a yankin Tigray
Asalin hoton, Ethiopian Airlines
Jiragen babban kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Ethiopian Airlines za su koma sauka a babban birnin yankin Tigray Mekelle da yaƙi a ɗaiɗaita, bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu cikin watan Nuwamba a Afirka ta Kudu.
Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ambato shugaban kamfanin Ethiopian Airlines Mesfin
Tasew na cewa filin jirgin saman Mekelle na cikin yanayi mai kyau.
Ya ƙara da cewa a yanzu jirgi ɗaya ne zai riƙa sauka a mekelle a kowacce rana, kafin daga bi-sani a ƙara idan buƙatar hakan ta taso.
An dawo da wutar lantarki da internet a gomman garuruwan yankin a wani ɓangare na yarjejeniyar, bayan da aka katse su sakamakon karɓe iko da yankin da 'yan tawayen TPLF suka yi a watan Yunin 2021.