Masu gabatar da kara sun kammala gabatar da shaidunsu a shari'ar Dan China da Ummita
Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Aisha Shariff Bappa
Rufewa
Anan muka kawo karshen shafin kai tsaye da ke kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makoftanta har da wasu kasashen duniya.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu, amma kafin zuwan lokacin ku ziyarci shafinmu na Intanet bbchausa.com domin karanta wasu labaran na daban.
Shafukanmu na sada zumunta da muhawara na Facebook da Instagram, akwai labarai da rahotanni da hotuna har da bidiyo masu kayatarwa.
A madadin sauran abokan aiki, Badriyya Tijjani Kalarawi ke mu ku fatan Alkhairi daga nan sashen Hausa na BBC.
Mu kwana Lafiya.
'Yan sanda sun kashe 'yan IPOB a Ebonyi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu fafutukar kafa kasar Biafra sun dade su na tada zaune tsaye a kudancin kasar.
Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya, ta ce sun kashe mambobin kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB, a musayar wutar da suka yi ranar Laraba.
Jaridar vanguard ta rawaito cewa an kuma kai samame sansanin 'yan OPOB din, inda aka gano gurneti guda 13 da ake kyautata zaton kirar Rasha ne, an kuma samu abin sanyawa mutne shokin na lantarki 210, da motocin alfarma 2 kirar Lexus 300, da babura masu dan karen gudu 5, da bindiga kirar pump action guda 2, da kananan bindigogi, ciki har da AK 47 da GPNG, da kakin soji kusan 30.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Ebonyi SP Chris Anyanwu ya shaidawa manema labarai a birnin Abakaliki, sun gano mutanen a sansanonin da suka kafa a garuruwan Umuleje, Amaeze da Nkalaha a karamar hukumar Ishielu a jihar.
Zelensky ya bai wa Biden kyautar lambar girma ta soji
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Zalensky lokacin da ya bai wa Biden kyautar ban girma ta soji
Ya yin da shugaba Biden da Zalensky ke ci gaba da tattaunawa a fadar White House, shugaban na Ukraine ya bai wa shugaban Amirka Joe Biden lambar ban girma ta soji.
Da ya ke mika ma sa lambar, Zelensky ya ce "ina alfahari da wannan ziyara,'' ya kara da cewa a jiya lokacin da ya kai wa sojojin da ke bakin daga ziyara a Bakhmut, wani Kaftin din soji ya ce masa ''ka bai wa Joe Biden kyautar ban girma ta soji,'' saboda shi din ''gwarzon shugaba ne.''
Shugaba Biden cike da annashuwa, ya godewa Zelensky, tare da cewa tabbas zai yi magana da wannan kaftin din sojin, kuma zai ba da kyauta ta musamman a kai ma sa Ukraine.
Biden ya yi wa Zalensky maraba a fadar White House
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Karon farko da Zalensky ya kai ziyara wata kasa tun bayan mamayar Rasha a Ukraine
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya isa fadar White House da ke Amirka, inda aka shinfida darduma mai launin Ja domin yi masa tarba ta musamman.
A gefe da gefen dardumar an kafa totocin Ukraine da Amirka, inda shugaba Biden da mai dakinsa suka tarbe shi.
Biden da Zalensky da matarsa Jill, sun yi musabaha da matashin shugaban Ukraine din tare da daukar hotuna.
Sun shiga cikin fadar shugaban kasa, inda za su tattauna kan batutuwa da dama a wani ofishi na musamman.
Ana sa ran za su dauki awa biyu su na ganawa, batun taimakawa Ukraine na daga cikin abin da ake sa ran shugaba Biden zai jaddadawa takwaran na sa.
Gwamnati ta daure dan jaridar Kamaru shekara 12 a kurkuku
Asalin hoton, via CPJ
Bayanan hoto, A watan Yulin 2016 ne aka kama dan jaridar mai shekara 73, ya musanta zargin da ake yi ma sa
Bayan tsare shi na sama da shekara shida, da dage shari'ar da ake yi ma sa sama da sau 100, an yankewa tsohon shugaban kafar yada labaran jamhuriyar Kamaru daurin shekara 12 a gidan kaso.
Wata kotu a birnin Yawunde ce ta yankewa Amadou Vamoulké hukuncin, kan laifin almubazzaranci da kudade da bai wa ma'aikata kyautar karin albashi ba tare da sanin hukumomi ba.
Sai dai Amadou ya musanta aikata ba daidai ba. An yi ta sukar yadda ake tafiiyar da shari'ar da ake yi masa, musamman kungiyoyin kare hakkin dan adam.
Jami'an wata runduna ta musamman mai suna Sparrowhawk ne suka kama Mista Vamoulké, wadda ta yi suna wajen kama duk wani da ke adawa da shugaba Paul Biya.
Lauyan da ke kare wanda ake tuhumar Alice Nkom, ta ce shari'ar bi ta da kullin siyasa ne da neman bata masa suna.
Masu gabatar da kara sun kammala gabatar da shaidunsu a shari'ar Dan China da Ummita, Daga Zaharaddin Lawan a Kano
Asalin hoton, OTHER
A jihar Kano da ke arewacin
Najeriya, masu gabatar da kara sun ce sun kammala gabatar da shaidunsu a ranar Laraba a
shari'ar dan kasar Chinan nan wanda ake zargi da kashe wata matashiya mai suna Ummita.
Sai dai sun ce ba su shirya tunkarar shaidun wanda ake zargin ba, inda
alkalin babbar kotun ya dagen zaman zuwa ranar juma’a.
Babbar kotun, ta saurari
shaida na karshe daga bangaren masu bagatar da kara a shari’ar zargin da ake
yiwa Mista Geng Quangrong dan kasar China, da kashe tsohuwar
budurwarsa Ummulkhuksum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shaidar wani
dan sanda ne, Aminu Halilu inda ya tabbatar wa da kotu cewa ranar 16 ga watan
Satumbar 2021 shi ne ya dauki bayanan wanda ake tuhuma sannan ya sanya hannu
kan takardar.
Sai dai lauyan Mista Geng, ya ce tilasta masa aka yi fadin abin da aka rubuta tare da tilasta masa
sanya hannu, aka kuma hankaɗa shi cikin sel aka kulle.
Don haka lauyan ya ce
basu amince da bayanan da aka gabatar ba ciki har da takardun asibiti.
To sai dai mai shari’a
Sanusi Ado Ma’aji ya amince da bayanan shaidar a matsayin exhibit C, ko da yake
ya ce idan ya bincika ya gano tursasa wanda ake zargin aka yi, domin ya bayar da
bayanan a caji ofis to zai yi watsi da bayanan.
Sannan ya kuma amince da bayanan
asibiti da bangaren masu kara suka gabatar, kuma shi ne abin da ya haifar da
jayayya da dogon turancin da har sai da aka tafi hutu.
Sai ranar Juma’a ne 23
ga wannan watan nan, ɗan ƙasar Chanan nan zai fara gabatar da shaidunsa a
shari'ar da ake yi masa kan zargin kashe Ummita.
Emefiele: 'Ba zan iya zuwa majalisa ba saboda zan je turai asibiti'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Majalisar wakilai ta gayyaci Emefiele ya yi ma ta bayani kan tsarin kayyade kudin da masu ajiya a bankuna za su iya cirewa da aikawa
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya rubutawa Majalisar wakilan kasar wasika, a ciki ya yi bayanin dalilin da ya sa ba zai amsa goron gayyatar da suka aika ma sa ba.
Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ne ya karanta wasikar ta Emefiele, a zauren majalisar a ranar Talata.
Jaridar Premium Times, ta ambato Gbajabiamila ya shaidawa zauren majalisar cewa Emefiele, zai tafi kasar wajen domin duba lafiyarsa don haka ba zai samu damar halartar zaman ba.
Kakakin majalisar wakilana ya ci gaba da cewa: ''Idan ba a manta ba majalisar ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriyar ya bayyana gaban ta a ranar Alhamis din makon da ya wuce, amma bai samu zuwa ba saboda ya na tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke halartar taron kasashen Afirka da Amirka a birnin DC.''
Gwamnan CBN na shan matsin lamba tun bayan kaddamar da sabbin takardun naira 200, 500 da 1000 da aka yi, wasu na ganin baidace ba saboda kudin an yi su kodaddu da ake fargabar masu damfara ka iya yin irinsu, amma CBN ya ce sam lamarin ba haka ya ke ba.
Hisbah a Kano za ta fara kama 'yan mata da ke talla a tituna
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Hisba a Kano da ke arewacin Najeriya ta fara shirin kama matan da ke talla akan titunan jihar.
Kafar yada labaran Radio Najeriya ta rawaito, mataimakiyar mukaddashin kwamanda mai kula da harkokin mata, Malama Ummulkulsum Kasim ce ta yi wannan bayanin, bayan kama wasu mata a titinan karamar hukumar Kumbotso.
Malama Ummulkulsum ta ce yawancin matan da ke talla akan tituna da daddare 'yan mata ne da ke saida gyara da goro, da rogo, ko kayan lambu da sauransu.
Ta ce yawancin 'yan tallan an gano su a tashoshin mota, da wurin makanikai abin takaicin kuma da daddare.
Malama Ummulkulsum ta ce ''hakkin iyaye ne killace 'ya'yansu da tabbar da ba su tarbiyya da ilimi, da kare su daga aikata ba daidai ba. Kuma addinin musulunci ya tabbatar da hakan, bai kamata a bar 'ya'ya mata da na yawo kara zube da sunan talla ba.''
Radio Nigeria ta rawaito kwanakin da suka gabata hukumar Hisba a jihar Kanon ta yi nasarar kama wasu matasa 19 kan zargin halartar auren jinsi a Kano, ko da ya ke Amarya da Angon sun tsere har yanzu ba a san inda suka buya ba.
Mata na bore kan haramcin zuwa jami'a da Taliban ta yi
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Taliban ta haramtawa mata zuwa makarantar Sakandare da Jami'a
'Yan mata a Afghanistan sanye da hijabi sun cika wasu titunan jami'o'insu, domin zanga-zangar kin amincewa da matakin gwamnatin Taliban na haramtawa mata zuwa Jami'a.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun hana matan wucewa tare da tasa keyarsu komawa inda suka fito.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna matan na rusa kuka lokacin da jami'an tsaron suka korasu.
Watanni 16 kenan da gwamnatin Taliban ta hana mata mata 'yan makarantar sakandare , lamarin da ya janyo damuwa ganin yadda ake yi wa ilimin mata kafar ungulu.
Wata daliba a jami'ar Kabul ta shaidawa BBC ''Sun wargaza rayuwarmu, sun wargaza gada daya tilo da ke tsakaninmu da ingantacciyar rayuwa.''
An dakile yunkurin juyin mulki a kasar Gambia
Bayanan hoto, A shekarar 2016 Adama Barrow ya zama shugaban Gambia
Wata sanarwa da gwamnatin Gambia ta fitar, ta ce an yi nasarar dakile wani yunkuri da marasa kishin kasa, suka yi na kifar da gwamnatin.
An kama sojoji da dama da wasu mutane uku da ake zargin da hannu a kitsawa sun tsere amma ana ci gaba da nemansu.
Lamarin ya faru tun a ranar Talata, kuma kawo yanzu babu cikakken bayani kan wadanda suke da hannu a yunkurin kifar da shugaba Adama Barrow daga mulkin da ya ke kan wa'adi na biyu da aka sake rantsar da shi a bara.
Kasar Gambia na daga cikin kasashen Afirka masu zaman lafiya, da 'yan yawon bude ido ke yawan zuwa lokutan hutu saboda manyan tekuna da namun daji da ta ke da su.
Shugaba Barrow ya yi nasara a zaben da aka yi na watan Disambar 2016, da shugaba Yahya Jameh ya sha kaye.
An tilastawa Mr Jammeh tserewa daga kasar zuwa Equatorial Guinea, ko da ya ke har yanzu ya na da karfin fada aji a kasar Gambia.
An yanke wa wani dan jarida hukuncin zaman gidan yari na shekaru 12 a Kamaru
An yankewa wani tsohon shugaban wata kafar yada labaran gwamnati a Kamaru hukuncin daurin shekaru 12 a gidan kurkuku saboda almubazzaranci da kudaden al'umma.
Amadou Vamoulke ya kwashe shekaru shida a tsare.
An kuma same shi da laifin wadaka da kudaden gwamnati da kuma baiwa ma'aikata wasu alawus -alawus ba tare da an ba shi iznin yin haka ba a hukumance, tsakanin shekarar 2005 da 2006.
An dai yi ta dage shari'ar da ake masa har fiye da sau 100, sannan kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi ta kiraye kirayen da a sake shi, bayan sun yi ta sukar shari'ar.
Amadou mai shekaru 73 ya musanta aikata ba daidai ba a lokacin da yake shugabantar kafar yada labaran gwamnati ta Kamaru ko CRTV.
Lauyoyinsa sun bayyana shari'ar a matsayin wacce ta saba doka
INEC ta kulla yarjejeniya da masu motocin haya da jiragen ruwa
Asalin hoton, OTHER
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya,wato INEC, ta kullu wata yarjejeniya tsakaninta da
kungiyar motocin haya da masu motocin da na jiragen ruwa, kan yadda za su yi
jigila da ma’aikatan hukumar da kuma kayayyakin zabe a lokutan zaben 2023.
Yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan rawar da
sufuri zai taka a zabukan da za a gudanar a Najeriya a shekara mai zuwa.
A bangare guda kuma, Tarayyar Turai ta ce za ta aike da
masu sa ido kan zaben da aka shirya gudanarwa a ranakun 25 ga watan Fabrairu da kuma na 11 ga watan Maris din 2023.
Yarjejeniyar an kullata ne domin ganin yadda za a kai
mambobi da kuma kayayyakin aikin zaben wuraren zaben a kan lokaci kuma cikin
aminci.
A yayin kulla wannan yarjejeniya, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce suna bukatar manyan motoci na haya da kanana har ma
da jiragen ruwa domin kai wa ga garuruwan da ke kan hayi.
A cewarsa akwai bukatar mutane sama da miliyan daya
da za su yi aikin da motoci sama da 100,000 da jiragen ruwa 4,200 domin
yin jigilar kayayyakin aiki zuwa rumfunan zabe 176,846 a mazabu 8,809 cikin
kananan hukumomi 774 na jihohin kasar 36.
Irin wannan yarjejeniya aka cimma a ranar 12 ga watan
Disambar 2018, domin gudanar da zaben 2019 wanda a cewar shugaban hukumar,
nasarar da aka samu ta gudanar da zaben lafiya ta sa aka kara karfafa amfani da
hanyar sufurin.
India ta kara sanya ido game da cutar korona bayan ta yi kamari a China
Ma'aikatar lafiya ta India ta kara zage damtse bayan karuwar cutar korona a China.
Gwamnatin kasar ta ba wa dukkan jihohin kasar umarnin tabbatar da ana kebe tare da ba wa wadanda suka kamu da cutar kulawa ta musamman don gujewa yaduwarta.
Kazalika gwamnatin ta bukaci jihohin da su kara himma a kokarin da suke wajen kare yaduwar cutar musamman a lokutan bukukuwan kirsimeti da na karshen shekara.
A shekarun 2022 da 2021, India ta fuskanci yaduwar cutar korona da mace macen mutane saboda cutar, to amma an samu sauki a 2022.
A cewar kididdigar gwamnatin kasar, ana samu mutum 1,200 da ke kamuwa da cutar korona a kowanne mako.
Tuni aka ci gaba da yi wa wadanda ba su karbi rigakafin cutar ba allurar.
'Yan bindiga sun kai hari gidan wani basarake a Kaduna
Asalin hoton, OTHER
Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan sarkin Fadan Ayu, da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da karamin dansa, Sahabi Halidu Ibrahim.
Sakataren majalisar sarkin, Jibril Adamu Muhammed, ya shaida wa manema labarai cewa ga dukkan alamu maharan suna harin basaraken ne, saboda kai tsaye da suka shiga gidan dakinsa suka nufa suna harba bindiga.
'Yan bindigar sun yi ta harbi amma kuma Allah ya kare basaraken, a don haka ne suka tafi dansa in ji sakataren.
Jibril Adamu, ya ce, bayan sun fice daga gidan tare da dan basaraken, sun kira waya inda mahaifiyar yaron ta dauka amma suka ce ba za su yi magana da ita ba sai da mahaifin.
Har yanzu dai ana dakon kiran 'yan bindigar don jin yadda za a yi wajen ceto dan.
Ana tuhumar 'yan mata takwas da kashe wani mutum a Toronto
Asalin hoton, Getty Images
Ana tuhumar wasu 'yan mata takwas da kashe wani mutum dan kimanin shekara 59 a Toronton na kasar Canada.
Jami'an 'yan sanda sun ce 'yan matan wadanda ke a tsakanin shekaru 13 da 16, ana zarginsu da cakawa mutumin wuka.
Mutumin da kawo yanzu ba a kai ga gane ko waye ba, na zaune ne a wani waje da ake tsugunnar da mutanen da ba su da muhalli.
Magajin garin John Tory, ya bayana lamarin a matsayin abin tashin hankali.
Tuni aka kama 'yan matan inda aka wkace makamai daga hannunsu.
'Yan sanda sun ce 'yan matan sun hadu ne ta kafar sada zumunta, sannan kuma uku daga cikinsu dama sun taba shuga hannun 'yan sanda.
Zelensky zai tafi Amurka don ganawa da Joe Biden
Asalin hoton, EPA
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya na kan hanyarsa ta zuwa Amurka, inda zai gana da shugaban kasar Joe Biden.
Wannan ce tafiyarsa ta farko da zai yi tun bayan da Rasha ta fara mamaya a kasarsa a watan Fabairun da ya wuce.
Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da ziyarar ta Mr Zelensky, ta na mai cewa za a ba wa Ukraine baturan makamai masu linzami don kara kare kasar daga hare haren Rasha.
Mr Zelensky dai na yawan karbar bakuncin shugabannin kasashen waje a Kyiv, sannan kuma ya na kai wa dakarunsa da ke sassan kasar ziyara akai-akai.
Amurka ita ce kasar da ta fi ba wa Ukraine taimakon makamai don mayar wa da Rasha martani.
Ana kuma ganin wannan ziyara za ta kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine.
Musk zai sauka daga shugabancin kamfanin Twitter
Asalin hoton, Reuters
Mamallakin kamfanin Twitter, Elon Musk ya ce zai yi murabus a matsayin babban jami'in kamfanin da zarar ya samu wani da zai maye gurbinsa.
Ya wallafa a shafinsa cewa idan hakan ta faru, shi kuma zai mayar da hankali ne wajen tafiyar da rukunin ma'aikatan da ke kula da rumbun adana bayanai da manhajojin kamfanin.
Matakin na baya-bayan nan da Musk ya ɗauka na zuwa ne kwanaki uku bayan da galibin mutane suka bayyana ra'ayin ya sauka daga shugabancin kamfanin a wata ƙuri'ar jin ra'ayi da ya buɗe.
Sama da mutum miliyan 17 ne suka bayyana ra'ayinsu kuma tun farko Mista Musk ya ce zai mutunta sakamakon.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaban kamfe din Peter Obi ya ajiye mukaminsa
Asalin hoton, Okupe/Facebook
Darekta Janar na yakin neman zaben Peter Obi a matsayin shugaban Najeriya karkashe inuwar jam'iyyar LP, Doyin Okupe ya sauka daga mukaminsa.
Ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa Obi a ranar 20 ga watan Disambar, 2022.
A cewarsa, ya sauka ne saboda kada abubuwan da ke faruwa da shi su shafi yakin neman zaben Peter Obi a 2023.
Murabus din Doyin Okupe na zuwa ne kwana guda bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda laifin rashawa.
Tun a shekarar 2019 ne hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Okupe a gaban kotu kan zargin karɓar kuɗaɗe daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, waɗanda ya gaza yin bayani kansu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Matar da ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Filato
Asalin hoton, OTHER
Wata mata mai suna Lucy Tapnang, 'yar shekara 29 da haihuwa ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare a Filato.
Matar wadda wasu 'yan bindiga suka sace tare da wasu mutum uku, ta yi ta maza inda ta kwace bindiga samfurin AK47 daga hannun daya daga cikin wadanda suka sace su, to amma duk da haka sai da suka ji mata rauni da wuka.
Lucy wadda mazauniyar Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ce, na kan hanyarta ne ta zuwa karamar hukumar Mangu tare da wasu fasinjoji bakwai a cikin motar, a nan ne 'yan bindiga suka tare su.
Lucy ta shaida wa shalkwatar 'yan sanda da ke Jos cewa, lamarin abin tsoro da tashin hankali ne.
Ta ce," A dai dai lokacin da muka kusa isa makarantar kimiyya ta Kuru, sai kawai muka ga wasu mutane sun tsayar da motar da muke ciki.Nan na ga wani mutum da bindiga a cikinsu yana kuma umartar duk mutanen motar mu sauka muka kuma mika wayoyin salularmu da kudi.A lokacin sai kawai na ce da fasinjojin motar ku fa maza ne yakamata mu yi ta maza don mu ceci kanmu, to amma sai suka ce mini ai mutanen na da bindiga kada su illatar da su."
To daga nan ne ita ta yi mazan ta wufce bindigar da ke hannun daya daga cikin masu satar mutanen in ji mai magana da yawun 'yan sanda jihar Alfred Alabo, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya ce, sauran fasinjojin ma sun taimaka mata bayan da suka ga ta kwace bindigar mutum guda.
Jami'in dan sandan ya ce ko da suka samu labarin harin sai suka aika jami'ansu ba tare da bata lokaci ba aka ceto mutanen.
‘Yan Boko Haram sun kona rumbunan hatsi da gidaje a Borno
Asalin hoton, OTHER
Mayakan Boko
Haram sun kai hari kauyen Jibwiwi a karamar hukumar Hawul da ke jihar Borno a
arewacin Najeriya.
Mayakan sun kona gidaje da dama tare da kona rumbunan hatsi.
Rahotanni
sun ce an kona a kalla gidaje takwas da rumbunan hatsi da ya kunshi Dawa da Masara da sauran nau'ukan hatsi da dama.
’Yan Boko Haram din sun je kauyen ne a kan
babura da yammacin ranar Litinin.
Kuma sun kona rumbunan ba tare da daukar komai
ba.
Wani dan kungiyar sintiri a kauyen ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, bayan
mayakan sun kona gidaje da rumbuna a kauyen, sai suka wuce zuwa garin Ngulde da ke karamar Hukumar Askira
Uba, to amma sun murkushe su da taimakon mafarautar yankin.