'Yan sanda sun karyata kai hari kotun majistare a jihar Imo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Mutum 12 sun rasa ransu a hadarin mota a hanyar Neja

    Hadarin Mota

    Asalin hoton, OTHER

    Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.

    Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.

    Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.

    Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.

    Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.

    Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.

  2. Barkanmu da safiyar Litinin

    Masu bibiyar wannan shafin ni ce Aisha Shariff Baffa na ke muku barka da safiyar Litinin.

    Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbc hausa.