'Yan sanda sun karyata kai hari kotun majistare a jihar Imo
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Aisha Shariff Bappa and Badariyya Tijjani Kalarawi
Rufewa
Anan muka kawo karshen shafin kai tsaye da ke kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kasashe daban-daban na duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da wallafa muku sabbin labarai. Kafin zuwan lokacin za ku iya zuwa shafinmu na Intanet bbchausa.com domin karanta wasu labaran masu kayatarwa.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta na BBCHausa Facebook, da Twitter da Instagram domin kallon hotuna har da bidiyo.
Badriyya Tijjani Kalarawi ke sallama da ku daga nan sashen Hausa na BBC.
Mu kwana lafiya.
Ana musayar yawu kan tsige shugaban karamar hukuma a Jigawa
Asalin hoton, JIGAWA STATE GOVERNMENT
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta ce majalisar kansilolin karamar hukumar Ringim ba su da hurumin tsige shugaban karamar hukumar.
Wannan na zuwa ne bayan da kansilolin suka sanar da tsige shugaban karamar hukumar bisa zarginsa da gudanar da wasu ayyuka ba tare da sanin majalisar ba.
Shi ma mutumin da kansilolin ke cewa sun tsige din yace yana nan daram a kan kujerarsa kasancewar ba su da ikon yin hakan.
Kansilolin dai sun aikawa
majalisar dokokin jihar Jigawa wasika game da abin da suka yi, don majalisar ta
dauki mataki na gaba, amma majalisar ta shawarci kansilolin su koma baya su bi
tsarin doka, saboda a cewar shugaban kwamitin watsa labaran majalisar ba su
tura musu wasika takanas zuwa wurinsu ba, illa dai sun saka sunansu cikin jerin
wadanda ake sanar da su an dauki matakin.
MDD ta soki matakin korar lauya Bafalasdine daga Isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana korar da Isra'ila ta yi wa wani Bafaranshen lauya dan asalin Falasdinu a matsayin laifin yaki.
A ranar Lahadi ne aka sa Salah Hamouri a jirgi zuwa Faransa bayan da hukumomin Isra'ila suka tsare shi tun watan Maris ba tare da wani caji ba.
Kakakin hukumar kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Jeremy Laurence ya ce matakin babban cin karo ne da yarjejeniyar Geneva.
Ita dai Isra'ila ta kwace takardun shaidar zama a gabashin Kudus na Mista Hamouri, saboda zarginsa da keta dokokin tsaro.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Khartoum
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Tun bayan hambarar da mulkin shugaba Omar al-Bashir Sudan ta fada rikita-rikitar siyasa
Jami'an tsaro a Khartoum babban birnin kasar Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma gurneti domin tarwatsa dubban mutane da ke zanga-zangar adawa da mulkin soja.
Masu zanga-zangar sun nufi fadar shugaban kasa amma ‘yan sanda sun fatattake su.
Sun yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla kwanan nan tsakanin sojoji da farar hula, suna masu cewa ba ta da ma'ana.
An gudanar da zanga-zangar ne a daidai lokacin da ake cika shekaru hudu da hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.
Sauyin gwamnati da aka samu na dan wani lokaci ya kare cikin shekaru biyu, inda sojoji suka sake hambarar da gwamnati.
'Yan sanda sun karyata kai hari kotun majistare a jihar Imo
A Najeriya, rundunar
‘yan sandan jihar Imo da ke kudancin kasar, ta yi watsi da rahotannin da wasu kafafofin watsa labarai
a kasar ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan kotun majistire a
jihar tare da banka ma ta wuta.
A sanarwar da kakakin rundunar ya fitar, ya ce
wannan labari bashi da tushe bare makama, ta kuma yi mamaki da samu labarin hakan.
Ya bayyana cewa wutar lantarki ce ta janyo tashin gobara a kotun Majistare din, an kuma yi nasarar kashe ta ba tare da bata lokaci ba bisa agajin jami'an kashe gobara da jami'an tsaro.
An kuma killace harabar kotun da baza jami'an tsaro domin tabbtar da babu wanda ya shiga ciki, an kuma fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren.
Wannan dai
na zuwa ne, a daidai lokacin da wasu mahara na daban suka kai farmaki kan wata
al’umma cikin Enugu wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama.
Sojin saman Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Zamfara
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce hare-hare ta sama da ta ke kai wa maboyar 'yan bindiga sun hallaka gwammansu a jihar Zamfara da ke arewacin kasar.
Samame ta sama da sojin suka kai karamar hukumar Maru a karshen mako, ya biyo bayan munanan hare-haren da 'yan bindiga suka kai kauyukan da ke yankin.
Mazauna kauyukan da ke yankin sun shaidawa BBC cewa matsawar jami'an tsaron Najeriyar ta tilastawa 'yan bindigar da ke garkuwa da mutane, arcewa wani kauye mai suna Mutunji, inda nan ma akai muu luguden wuta.
Mazauna kauyukan sun kuma ce, sun ga gawawwakin 'yan bindigar har guda 60, da wasu 20 da suka jikkata, sai kuma baburan maharan da sojojin suka lalata.
Sai dai sun ce akwai tsirarun farar hula da lamarin ya rutsa da su, ciki har da wau tsofaffi da ke kokarin tserewa a lokacin da gungun 'yan bindigar akan babura da manyan makamai suka tunkaro kauyensu domin gujewa samamen da luguden wuta ta saman da sojojin Najeriyar ke yi babu kakkautawa.
FRSC ta baza jami'anta a sassa Najeriya domin bikin kirsimati da sabuwar shekara
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC, ta sanar da aike jami'anta a sassa daban-daban na kasar domin sintiri a tituna a lokacin bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara da ke tafe.
A jawabin da mukaddashin shugaban hukumar , Dauda Biu ya yi wa manema labarai a ranar Litinin, ya ce jami'ansu 36,224 ne za su yi wannan aikin.
Sai dai ya ce hukumar na bai wa 'yan Najeriya tabbacin kare lafiyarsu da dukiya a lokacin da ake wannan murna ta ganin karshen shekarar 2022 lafiya da fatan ganin 2023 da ke tafe.
A Najeriya dai ana yawan samun hadurran motoci a manya da kananan titunan kasar, musamman lokacin bukukuwan karshen shekara.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasar da 'yan sanda na dora alhakin hadurran ababen hawan kan tukin ganganci, ko gudu fiye da kima da direbobi ke yi, sai kuma rashin hakurin masu ababen hawa a lokacin da aka samu cunkoun ababen hawa.
Kwale-kwale dauke da 'yan Rohingya ya lalace a tekun Andaman
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Ba wannan ne karon farko da 'yan Rohingy suka samu kansu a tsaka mai wuya a cikin teku ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen da ke kusa da tekun Andama a kudu maso gbashin yankin Asiya, su taimakawa wani kwale-kwale da wuta ta dauke mi shi kusan makwanni biyu kenan, makare da 'yan gudun hijirar Rohingya 150.
An yi magana mutanen da ke cikin kwale-kwalen ta tarhon tauraron dan adam, inda suka tabbatar da mutuwar wasu daga 'yan uwansu ciki har da kananan yara.
Sun kuma ce ba su da abinci da ruwan sha. Tun ranar Juma'ar da ta wuce ne, MDD ta yi wannan kira amma har yanzu babu taimakon da ya isa ga mutanen.
Karamin kwale-kwalen kamun kifin ya bar kudancin Bangladesh a makon da ya wuce, a yanzu ya kai sama da kwanaki 21 akan teku. Yawancin wadanda ke cikin kwale-kwalen na kan hanyar zuwa kasar Malaysia ne.
Injin jirgin ne dai ya kasa, kwanaki kadan da fara tafiyar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika godiya ga wadanda suka aika masa da katunan taya murnar cika shekara 80 da haihuwa a duniya.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya aikewa manema labarai, ya ce cikin barkwanci shugaba Buharin ya ce ma'aikata ba su samu damar shagali a ranar ba: ''saboda da gangan na sanya ranar dawowata daga Amirka, kwana daya bayan wannan rana, domin kaucewa duk wasu bukukuwa da za a yi.''
Sanarwar ta ce, da ya ke yin jawabi a shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha, da manyan bakin da suka je gida domin taya shi murna, shugaba Buhari ya ce rana irin wannan daya ta ke da kowacce rana a bakin aiki.
Shugaba Buhari ya karanta sakon da ke cikin wani katin taya murna da manyan jami'an fadar suka bashi, a bainar jama'a, ya na cewa; ''a madadin daukacin ma'aikatan da ni kaina, mu na taya ka murnar zagayowar ranar Haihuwar jajirtacce shugaba, uban kasa, kuma babanmu.
Shugabanmu ne ya zama gwarzo a taron koli tsakanin kasashen Afirka da Amirka da aka gama kwanakin nan, mu na alfahari da kai, muna murnar ka dawo bakin aiki lafiya.''
INEC da NBC da masu ruwa da tsaki sun yi taro kan zaben 2023
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zabe ta Najeriya INEC, da hukumar da ke sa ido
kan kafofin watsa labarai ta NBC da sauran masu ruwa da tsaki a kan lamarin
zabe sun gudanar da wani taro a Abuja, babban birnin kasar.
Shi dai wannan taron an yi shi ne da zummar jawo
hankalin jam’iyyun siyasa da kafofin watsa labarai don ka da su bari a yi amfani
da su wajen halasta kudin haram a lokacin zaben 2023.
Taron na masu ruwa da tsaki kan maganar kawar da yin amfani
da kudi a zabe mai zuwa ya kunshi bangarori daban-daban.
Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahamud Yakubu, ya ce sun
cimma daidaito a tsakanin dukkan mahalarta taron.
Wasu dai daga bangaren mahalarta taron sun yi korafi kan
maganar kayyade fitar da kudi daga asusun banki duk rana da babban bakin
Najeriya ya sanar.
Jirgin ruwan yakin Thailand ya yi hatsari, soji 31 sun bata
Rundunar sojin ruwan Thailand ta tabbatar da batan sojoji31 bayan jirgin ruwan da suke ciki ya yi tsari dauke da sojoji da ma'aikata sama da 100 a cikinsa.
Jirgin ruwan mai suna HTMS Sukhothai, ya cika da ruwa bayan ya yi karo inda ruwa ya fara shiga ciki tare da nutsewa a daren jiya Lahadi.
Hotunan da sojin ruwan Thailand suka wallafa a shafinsu na intanet ya nuna wadanda suka tsira zaune a wani karamin jirgin sanye da rigar kariya daga nutsewa a ruwa.
A ranar Litinin, hukumomin Thailand suka sanar da kubutar sojoji 75 su na kuma ci gaba da neman wasu 31.
Mai magana da yawun sojin Admiral Admiral Pogkrong Monthardpalin, ya shaidawa BBC cewa ''za a fara gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin, kuma hakan ba ta taba faruwa da rundunarmu ba. Saboda jirgin lafiyayye ne ba shi da wata matsala.''
Za a je zagaye na biyu a zaben 'yan majalisar dokoki a Tunisiya
Hukumar zabe a Tunisiya ta ce za a gudanar da zagaye na biyu a mafi yawan yankunan kasar bayan da aka samu karancin fitowar masu kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi ranar Asabar.
Hukumar ta ce 'yan takara ashirin da daya ne suka samu nasara a zagayen farko na zaben, inda ta ce fiye da gundumomi dari da talatin ne za a fafata a zagaye na biyu a wata mai zuwa.
Kusan kashi tara cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a a Tunisiya sun fita rumfunan zabe ranar Asabar.
Jam'iyyun adawa sun yi kira ga shugaba Kais Saied ya yi murabus, bayan ya kafa wani sabon tsarin siyasa tun hawansa mulki a bara.
An kashe dakarun juyin juya halin Iran hudu
Kafofin watsa labaran cikin gida a Iran sun bayyana cewa an kashe wasu dakarun juyin juya hali hudu a yankin Sistani-Baluchistan da ke kudu maso gabashin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iran ya ambato cewa, wadanda suka kashe jami'an sun gudu zuwa Pakistan, sai dai ba a yi karin bayani ba.
Ana yawan gwabzawa tsakanin jami'an tsaro da masu safarar miyagun kwayoyi a yankin.
Sai dai kuma a baya bayan nan an fuskanci wasu munanan tashe-tashen hankula tsakanin jami'an tsaro da mutanen da ke shiga zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasar da ke cikin wata na hudu.
'Yan Tuwita sun bukaci Elon Musk ya sauka daga shugabancin kamfanin
Asalin hoton, Getty Images
Masu amfani da shafin Tuwita sun zabi Elon Musk ya sa sauka daga shugabancin kamfanin bayan da ya wallafa wani sakon jin ra'ayin masu amfani da shafin a kan makomarsa.
Kashi 57 cikin 100 na masu amfani da shafin sun zabi cewa shugaban kamfanin ya sauka.
Mr Musk, wanda ya sayi kamfanin a kan dala biliyan 44, ya ce zai amince da abin da sakamakon ya bayyana.
Mr Musk, wanda shi ne mai kamfanin Tesla da kuma Space X, na fuskantar suka tun bayan da karbe ragamar tafiyar da kamfanin.
Har kawo yanzu bai ce uffan ba tun bayan kammala zaben, to amma ko da ya sauka daga kan shugabancin kamfanin, zai ci gaba da kasancewa mai kamfanin.
Fiye da mutane miliyan 17 da miliyan 500 ne suka kaɗa ƙuri'ar a ranar Litinin, inda kaso 42.5 cikin 100 ne kadai suka zabi rashin amincewa da murabus din nasa.
Shugaban Ukraine ya bukaci taimakon na'urorin yaki ta sama
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bukaci kasashe kawayen kasarsa a arewaci da kuma yammacin turai da su kara taimaka wa kasarsa da na'urorin yaki ta sama.
Mr Zelensky, ya bayyana wannan bukata ga shugabannin kasashen ne ta bidiyo.
Shugaban na Ukraine ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki a Latvia cewa, samar da kayan yaki ta sama ne kadai hanyar da za a taka wa Rasha birki daga munanan hare haren da ta ke kai wa kasarsa.
Har yanzu Ukraine na fama da hare haren makamai masu linzami daga Rasha in da ta ke lalata mata tashoshinta makamashi.
An zabi Cyril Ramaphosa a matsayin wanda zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2024
Asalin hoton, Getty Images
Jam'iiyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu, ta sake zabar shugaba Cyril Ramaphosa, a matsayin shugaban jam'iiyar kuma wanda zai sake tsaya mata takara a 2024.
Mr Ramaphosa ya samu nasara a a kan abokin takararsa Zweli Mkhize da kuri'u 2,476.
Shugaban na Afirka ta Kudu ya samu nasarar ce duk da zarge zargen sama da fadi da wasu kudade, zargin da ako da yaushe yake musantawa.
Bayan sanar da samun nasarar ta sa, magoya bayansa sun rinka wake wake da raye raye.
Jam'iiyar ANC, ta kasance mai mulki a Afirka ta Kudu tun 1994.
Ronaldo ya yi gum da bakinsa game da nasarar Messi
Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo, mutumin da yafi kowa magoya a shafukan sada zumunta har yanzu bai ce komai ba, tun bayan da Lionel Messi ya taimaki Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.
Argentina ta samu galaba a kan Faransa da ci hudu da biyu a bugun fenariti bayan sun buga wasa tsawon minti 120 kuma aka tashi uku da uku.
Masoya kwallon kafa sun ce ba a taba buga wasan da ya kayatar kamar wannan ba a tarihin gasar cin kofin duniya.
Ronaldo wanda magoya bayansa miliyan 780 ne jumlace a shafukan Twitter da Instagram da kuma Facebook, ya yi gum da bakinsa game da nasarar Argentina da Messi.
Har yanzu bai taya Messi murna ba a bainar jama'a.
Cutar kwalara ta kashe mutum 20 a Cross Rivers
Asalin hoton, OTHER
A kalla mutane 20 sun rasa ransu yayin da wasu 30 kuma ke kwance a asibiti bayan da aka samu barkewar cutar kwalara a wasu kauyuka 10 da ke jihar Cross Rivers a kudancin Najeriya.
Mahukunta a jihar sun ce yawanci mutanen sun mutu ne a tsakanin ranakun 15 da 17 ga watan da Disambar shekarar da muke ciki.
Babbar jami'a a hukumar kulda da lafiya a matakin farko ta jihar, Janet Ekpeyong, ta shaida wa manema labarai cewa tuni gwamnatin jihar ta tura jami'an lafiya da kayan aiki zuwa yankunan da cutar ta barke don shawo kanta.
Ta ce, tawaga daga kungiyar likitoci ta Najeriya da wasu daga Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma na Kungiyar agaji ta Red Cross sun fara yunkuri don magance cutar a jihar.
Kauyukan da cutar ta barke na karkashin karamar Hukumar Abi, kuma suna fama da karancin tsaftataccen ruwan sha da kuma rashin tsaftar muhalli, abin da ake danganta wa da musabbabin barkewar cutar.
Dan bindiga ya harbe mutum biyar a Canada
Asalin hoton, Reuters
Mutane biyar sun rasa ransu bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wani rukunin gidaje da ke Toronto a Canada.
Ba tare da bata lokaci ba 'yan sanda suka mayar da martani ga harbin wanda aka yi a unguwar Vaughan, da ke da nisan kilomita 20 daga arewacin Toronto, kuma a take aka harbe dan bindigar.
An kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.
Tuni aka fara gudanar da bincike a kan dalilin harin.
Babban jami'in dan sanda a garin ya ce jami'ansu sun ga tashin hankali saboda yadda suka tsinci gawarwaki a cikin gidajen da ke unguwar.
An kwashe mutanen da ke zaune a rukunin gidajen, amma kuma an ce bayan bincike za a mayar da su gidajensu.
Ba kasafai ake samun harbe-harben bindiga a Canada ba, to amma a watannin baya bayan nan ana kara samun hare haren bindiga a kasar.
MDD ta yi kira da a kai dauki ga fasinjojin jirgin ruwan da suka makale a tekun Andaman su 150
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen da ke kusa da tekun Andaman ta su kai dauki ga wani jirgin ruwa da ya dauko mutane akalla 'yan gudun hijirar Rohingya 150 daga Myanmar.
Jirgin ya kasance babu wutar lantarki a cikinsa tsawon makonni uku.
Mutanen da ke cikin jirgin da aka samu ji ta bakinsu ta wayar tauraron dan adam, sun ce basu da ruwa da abinci.
Fasinjojin cikin jirgin sun hadar da mata da yara, kuma akwai rahotannin da ke cewa akwai wadanda suka mutu a cikinsu.
Rahotanni sun ce 'yan gudun hijirar Rohingya sun bar sansanonin da suke zaune a kudancin Bangladesh sun nufi Malaysia.