An zargi sojojin Najeriya da zubar da cikin matan da Boko Haram ta yi wa Fyaɗe

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. 'Sojojin Sudan za su miƙa mulki da zarar ƴan siyasa suka cimma matsaya'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban mulkin soji na Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su miƙa mulki da zarar ƙungiyoyin farar hula suka cimma matsaya kan kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya.

    Burhan ya ce ɓangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar ranar biyar ga watan Disamba, wadda ta ƙunshi batun kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ƙarƙashin farar hula za su kafa kwamitocin samar da kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Ya ce miƙa mulki ga farar hula ya danganta ne ga lokacin da ƙungiyoyin farar hula za su kwashe wajen samar da matsaya.

    Ya kuma jaddada cewa sojoji sun ceci ƙasar ne a lokacin da suka yi juyin mulki na ranar 25 ga watan Oktoban 2021.

  2. Rashin tabbas bayan ritaya ke sanya ma’aikatan gwamnati yin sata - Jonathan

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

    Asalin hoton, AFP

    Tshohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce rashin tabbas game da samun kulawa bayan yin ritaya ne ke rura wutar ayyukan rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnatin ƙasar.

    Jonathan ya bayyana haka ne ranar Talata a lokacin ƙaddamar da wani littafi game da rayuwar tsohon limamin cocin fadar gwamnatin tarayya, Obioma Onwuzurumba.

    A cewar tsohon shugaban ƙasar “ɗaya daga cikin manyan matsalolin Najeriya, wanda ga dukkan alama shi ne ya sa rashawa ta yi katutu, shi ne mutane ba su san me zai faru da su ba gobe...shi ya sa irin waɗannan mutane kan ce tunda yanzu ina kan aiki bari na taimaka wa kaina ko ta halin ƙaƙa.”

    Inda ya ƙara da cewa doka ba ta bai wa ma’aikata damar yin kasuwanci ko mallakar kamfanoni ba, sannan babu wanda zai kula da kai ko yaranka bayan ka bar aiki.

    Daga nan sai ya buƙaci masu hali su samar da wani shiri na tallafa wa tsofaffi, domin a cewarsa hakan zai taimaka rage matsalar.

  3. Mata sun fi maza saurin fushi - bincike

    Wata kuri'a da aka kada a kasashe sama da 150, ya gano mata sun fi maza samun kai cikin bakin ciki, da damuwa da saurin fusata.

    BBC ce ta jagoranci bincikn a wani bangare na shirin ta na Mata 100 rabin al'ummar duniya, an kuma dauki shekara 10 ana gudanar da binciken.

    A shekarar 2012 rahotanni sun bayyana maza da mata sun yi kunnen doki ta fannin saurin fusata da rana, amma shekaru 6 bayan nan, adadin ya karu da kashi 6.

    Matan Cambodia su ke jan ragamar yawan masu fushi da rashin farin ciki da kashi 17, yayin da Indiya, da Pakistan, da Moroco suke da kashi 12.

  4. Shugaban China na ziyara a Saudiyya

    Xi Jinping da yarima Mohammed bn Salman

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban China Xi Jinping zai fara wata ziyara a Saudiyya, irin ta ta farko da ya taɓa kai wa masarautar cikin shekaru shida.

    Ana sa ran shugaba Xi zai gana da Sarki Salman bin Abdul'Aziz al-Sa'ud, da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman, za kuma su halarci taron koli na yankin gulf.

    China babbar aminiya ce ga Saudiyya ta fuskar kasuwanci, tana kuma neman ƙara faɗaɗa hakan a ƙasar.

    Ziyarar na zuwa ne, daidai lokacin da a hukumance dangantaka tsakanin Saudiyya da Amurka ta yi tsami, yayin da ita ma China da Amurkar alakar ta ƙara dagulewa fiye da shekarun baya.

  5. Barka da warhaka

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Haruna Ibrahim Kakangi ke maku barka da safiyar Laraba.

    Za mu rinƙa kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya ta wannan shafi a tsawon wannan yini da yardar Allah.

    Da fatan za ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinku kan waɗannan labarai da ma wasu ƙari a facebook, da tuwita, da instagram @bbcnewshausa.

    Za ku iya kallon shirye-shiryenmu na bidiyo a shafinmu na BBC Hausa youtube.