Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta kai ɗalibi Aminu Muhammad, in ji lauyansa

Wannan shafi na kawo maku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Da gaske ne gwamnoni na danne kuɗin ƙananan hukumomi - ALGON

    Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya, Hakeem Ambali ya ce kalaman shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan cewa gwamnoni na danne wa ƙananan hukumomi gaskiya ne.

    Jaridar Punch ta ruwaito Ambali na cewa “ana facaka da kuma danne kuɗaɗen ƙananan hukumomi.” Muna son shugaba Buhari ya yi ta-maza ya magance wannan matsala.

    Ya ƙara da cewa “idan ana so a magance matsalolin talauci da rashin tsaro, to dole ne a bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kansu.”

    Daga nan sai ya buƙaci shugaban ƙasar da ya tursasa gwamnoni su sanya hannu kan dokar cin gashin-kai na ƙananan hukumomi.

  2. Koriya ta kudu ta sanya wa Koriya ta arewa sabbin takunkumai

    ...

    Asalin hoton, Pool

    Bayanan hoto, ...

    Koriya ta Kudu ta sanya sabbin takunkumai a kan wasu daidaikun mutane, da hukumomi da ke da alaka da shirin makamai na Koriya ta Arewa, sakamakon kaddamar da manyan makamai masu linzamin da makwabciyar tata ke yi akai-akai.

    Ma'aikatar harkokin waje ta Koriya ta Kudun ta ce mutane takwas da hukumomi bakwai da abin ya shafa, sun hada da jami'ai a cibiyoyin kudi da ke da alaka da shirin nukiliya da kuma na makamai masu linzami na kasar ta Koriya ta Arewa.

    Wasu kuma su ne wadanda ke da hannu wajen haramtacciyar safara ta jiragen ruwa ta kayan Koriya ta Arewa da aka sanya wa takunkumi.

    Tun da farko Amurka ma ta sanya wa wasu manyan jami'ai na Koriya ta Arewar uku takunkumi, wadanda ta ce suna da hannu kai tsaye a kera makamai.

  3. Cuba ta tsaurara dokoki saboda masu zanga-zanga

    An fara amfani da wani sabon kundin dokoki hukunta laifuka a Cuba sakamakon karuwar zanga-zanga da jama'a kan yi a tsibirin.

    Kundin ya kara yawan hukuncin da za a yi a kan laifukan da suka shafi tsaron kasar da kuma yawan laifukan da za a iya yanke hukuncin kisa a kansu.

    Tuni kungiyoyin kare hakkin dan'adam suka fara suka kan abubuwan da sabon kundin dokokin zai iya haifarwa na danne 'yanci.

    Kundin ya kunshi wani sashe da aka haramta samar da kudi daga waje, ga 'yan jarida masu zaman kansu.

    Haka nan ya kara yawan laifukan da za a iya yanke hukuncin kisa a kansu zuwa ashirin da hudu (24), ciki har da duk wani yunkuri na durkusar da tsarin kwaminisanci da kasar ke bi.

  4. Barka da warhaka

    Masu bibiyan mu barka da shigowa wannan shafi namu na kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.

    Ni Haruna Ibrahim Kakangi zan rika kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma fadin duniya.

    Ku je shafukanmu na sada zumunta a facebook, da tuwita da kuma instagram domin tofa albarkacin baki kan labaran da muka kawo maku.