Mahaifiyar Ummita ta ba da shaida a gaban kotu kan zargin Ɗan China da kisan ƴarta

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Mata za su sami kashi ɗaya bisa uku na kujerun majalisar dokoki a saliyo

    Sierra leone

    Asalin hoton, others

    Majalisar dokokin Saliyo ta amince da murya ɗaya, wata doka da za ta tabbatar wa mata kashi ɗaya bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar, tare kuma da samar wa matan kashi ɗaya bisa uku na kujerun kansiloli a fadin ƙananan hukumomin ƙasar.

    A yanzu za a miƙa ƙudurin dokar ga shugaban ƙasar Julius Bio domin ya sanya hannu ya zama doka.

    Duk da cewa ƙudurin na daga cikin manyan alƙawuran yaƙin neman zaɓe a 2018. Majalisar ta ɗauki shekara uku kafin ta amince da ita.

    A yanzu haka dai mata 19 ne kawai a majalisar dokokin mai mambobi 146.

  2. Maraba

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance tare da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhara kan labaran da muke wallafawa.