Mutum uku sun mutu a fada tsakanin kungiyoyin asiri a Kwara

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Yawan al'umar Tanzaniya ya karu da kusan kashi 40 a shekarar 10

    Sakamakon kidayar yawan al'ummar Tanzaniya da aka fitar ranar Litinin ya nuna cewa yawan al'umar kasar ya karu da daga miliyan 44.9 a shekarar 2012, zuwa sama da mutum miliyan 66.

    Karuwar yawan al'umar ya tilasta wa shugabar kasar Samia Suluhu fitar da gargadi ga 'yan kasar game da kalubalen da kasar za ta fuskanta sakamakon karuwar yawan jama'ar kasar.

    Ta kara da cewa ''karuwar yawan al'umma ba zai zama matsala ga babbar kasar kamar tamu ba, to amma hakan zai shafi kudin shigar da kasarmu ke samu da ababen more more rayuwa''.

    Sakamakon kidayar ya nuna kashi 51 cikin 100 na al'umar kasar mata ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Ba za a fuskanci karancin abinci a Najeriya ba - Gwamnatin tarayya

    Ministan noma

    Asalin hoton, Ministry of Agricultu

    Ministan noma da raya karkara na Najeriya Mohammed Abubakar ya yi watsi da fargabar da ake yi a kasar na fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

    Yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin kasar, ministan ya ce ba za su bari hakan ta faru ba.

    Wasu daga cikin 'yan majalisar dai sun bayyana cewa matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.

    Sun kara da cewa an yi hasashen cewar kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.

    To Amma ministan ya ce ''ba za mu bari matsalar karancin abinci ta yi tasiri a Najeriya ba, ina mai tabbatar muku da cewa da yardar Allah hakan ba za ta faru ba, saboda akwai matakai da dama da muka dauka domin magance wannan matsalar''.

    Ya ci gaba da cewa ''daya daga cikin matakan da muka dauka shi ne noman rani, wanda muka ware masa kudi, muna aiki da ma'aikatar kudi, muna kuma samun tallafi daga cibiyoyin kudi, kamar bankin raya kasashen Afirka, dan haka za mu fadada noman ranin''.

    Ministan ya kuma ce gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa. kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya ruwaito.

  3. Najeriya na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola

    Ebola

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Najeriya sun ce kasar na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola, da ake tunanin shigo da ita daga kasar Uganda.

    Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta ce an samu karuwar baranazar barkewar cutar ne sakamakon yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cudanyar fasinjoji, musamman a filayen jiragen sama na Nairobi, da na Addis Ababa, da kuma filin jirgin sama na Kigali.

    Hukumomin lafiyar kasar sun ce suna cikin shirin ko ta kwana, yayin da suka dauki matakan da suka dace domin yakar cutar idan ta barke.

    Matakan sun hada da sanya ido kan fasinjoji tare da tantance su a filayen jiragen saman kasar.

    Hukumar ta shawarci 'yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda idan ba ta zama dole ba, daga yanzu zuwa wasu lokuta.

    NCDC ta ce fasinjojin da suka zo kasar daga Uganda za a sanya ido a kansu na tsawon mako uku, domin tabbatar da halin da suke ciki.

    An samu bullar cutar a kan mutum 100 tare da mutuwar mutum 30 a Uganda, tun bayan barkewarta a watan Satumba, ana kuma fargabar cewa cutar ka iya yaduwa zuwa makwabtan kasashe.

  4. Cutar amai da gudawa ta kashe mutum 180 a Malawi

    Cholera

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya ta kasar Malawi ta ce adadin wadanda cutar amai da gudawa ta kashe a kasar ya kai 183 zuwa karshe watan Octoba.

    Haka kuma hukumar ta ce wadanda ke kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa, inda yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar tun watan Maris ya kai 6,056, kamar yadda sanarwar da ma'aikatar lafiyar ta nuna.

    Ma'aikatar lafiyar kasar ta danganta yawan mace-macen da rashin tsaftataccen abinci, da ruwan sha da rashin amfani da ban dakuna kamar yadda ya dace.

    Haka kuma ministan lafiyar kasar ya ce wasu marasa lafiyar ba sa zuwa asibiti saboda wasu dalilai na addini, inda wasu kuma ke zuwa asibitin bayan da cutar ta gama yi musu illa.

    Ya yi kira ga jagororin addini a kasar da su rika karfafa wa al'uma gwiwwa wajen zuwa asibiti, domin kaucewa yawan mace-macen.

    Cutar - wadda galibi ake kamuwa da ita sakamakon cin gurbataccen abinci da ruwan sha - ana alakanta ta da rashin tsaftar muhalli.

  5. Ma'aikata sun rufe filin jirgin sama na Legas

    Filaye

    Asalin hoton, Getty Images

    An soke tashin jiragen da aka shirya tashinsu yau da safe a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, sakamakon zanga-zangar ma'aikatan filayen jiragen sama.

    Lamarin ya sanya fasinjojin da suka yi sammako domin yin tafiye-tafiye cikin kunci.

    Su dai ma'aikatan filayen jiragen sama na zanga-zangar ne saboda korar wasu daga cikin mambobin kungiyarsu 34 daga aiki, da kamfanin Bi-Courtney Aviation Services Limited (BASL) ya yi.

    Kungiyar ma'aikatan sun yi zargin korar wasu daga cikin ma'aikatan nata da kamfanin ya yi ba ya bisa tsarin doka.

    A wata sanarwa da kamfanin jirgin sama na Ibom Air, ya aikewa fasinjojinsa ya ce wannan zanga-zanga ta shafi zirga-zirgasa na yau a ciki da wajen Legas.

  6. Elon Musk zai zama sabon shugaban Twitter

    Ilon Musk

    Asalin hoton, Reuters

    Elon Musk ya bayyana cewa shi ne zai zama sabon shugaban kamfanin sada zumunta na Tuwita wanda ya saya kan zunzurutun kuɗi dala biliyan arba'in da huɗu.

    Ɗaya daga cikin matakan farko da ya ɗauka bayan kammala cinikin kamfanin, shi ne korar shugaban kamfanin wato Parag Agrawal.

    Sai dai masu sharhi na ganin da wuya zai mayar da hankali domin kula da kamfanin na Tuwita sakamakon irin ayyukan da suka sha masa kai a kamfanoninsa na Tesla da Space - X.

    Haka kuma Mista Musk ya rushe daraktocin kamfanin duk da cewa ya ce matakin na wucin gadi ne.

    Ana ganin zai kawo tsare-tsare masu yawa kan yadda ake gudanar da kamfanin ciki har da sauyi kan shafukan da aka tantance da shuɗin maki.

  7. Assalamu alaikum

    Masu binmu a wannan shafi na kai-tseye barkan mu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Ku kasance tare da mu domin kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai jagoranci shafin a daidai wannan lokaci, dafatan za ku ji dadi kasancewa tare da mu.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.