Mutum uku sun mutu a fada tsakanin kungiyoyin asiri a Kwara

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Asuba ta gari

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi kai-tsaye da muka dauki tsawon yinin yau muna kawo muku.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu dawo da sabbin labarai.

    Kafin nan, Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Ukraine za ta kwashe mutum dubu 70 a yankin kogin Dnipro da Rasha ta mamaye

    Kherson

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban yankin Kherson da Rasha ta mamaye ya ce za su kwashe kusan mutum dubu 70 daga yankin kogin Dnipro.

    Hakan na zuwa yayin da dakarun Ukraine ke ci gaba da kai hare hare da nufin sake kwato birnin Kherson.

    Vladimir Saldo ya ce suna fargaba za a samu ambaliya a yankin. Kazalika ya zargi Ukraine da shirin tarwatsa dam din na Dnipro.

    Sai dai a martani da tayi Ukraine ta zargi Rasha da raba mutane da gidajensu da karfi da yaji don ta mamaye su.

  3. Faduwar darajar naira: EFCC ta kama 'yan canji a Abuja

    EFCC

    Asalin hoton, OTHER

    A yau Talata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi wa kasuwar musayar kudaden ketare ta bayan fage dake Zone 4 a Abuja ƙawanya, inda suka tafi da wasu daga cikin ‘yan chanjin.

    Wasu da lamarin ya faru akan idon su sun ce jami'an EFCCn sun isa wajen ne da misalin 2:00 na rana, inda suka datse dukkan wata hanya da zata kai layin da ‘yan chanjin suke harkokinsu, wanda hakan ya kawo tsaikon harkoki a kasuwar da ke Zone 4 na tsawon kusan sa'a 2.

    Sai dai har yanzu, hukumar ta EFCC bata kai ga cewa uffan ba kan wannan batu.

    Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tashin farashin dala a kasuwanin bayan fage a Najeriya, wanda masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arzikin kasar ke alakanta shi da matakin da babban bankin kasar ya dauka na sauya fasalin takardun kudin kasar nan da watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa ta 2023.

    Faruwar wannan lamari dai ya dauki hankalin al’umma musamman masu harkokin musayar kudade a Najeriya na fargabar rashin sanin yadda lamarin ka iya fadada zuwa wasu jihohin kasar.

  4. Alkalai a Brazil sun ki ganawa da Bolsanaro har sai ya amsa shan kaye

    Brazil

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkalai a kotun kolin Brazil sun ki yadda su gana da Shugaba Jair Bolsonaro har sai ya amsa shan kaye a bainar jama'a.

    Mista Bolsonaro ya sha kaye hannun Lula Inacio da Silva da tazara yar kadan, a zaben da aka yi ranar Lahadi.

    Kafafen cikin gidan sun ruwaito cewa Shugaban ya nemi yayi taron gaggawa da alkalan a fadarsa, amma suka ki amsa gayyatar.

    Dama a baya Bolsonaro ya sha sukar kotuna cewa suna nuna masa bambanci ta fuskar siyasa.

    Yanzu haka ana bata kashi tsakanin yan sanda da direbobin manyan motoci, da ke ci gaba da toshe hanyoyi a Brazil.

    Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa duk da haka kawo yanzu babu wani sauyi don hanyoyi na ci gaba da zama a toshe, yayin da al'umma ke shafe awanni kafin su isa inda zasu.

  5. Kudin da aka ware don yaki da labaran ƙarya sun yi kadan - Lai Mohammed

    Mnistan ƴada labaru da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kudaden da ake ware wa ma'aikatarsa sun yi kadan wanda kuma ke kawo cikas wajen ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.

    Ministan ya bayyana hakan ne yau Talata a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma'aikatarsa a 2023.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Ya ce ma'aikatarsa na bukatar kudade da ya kamata domin ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.

    “Idan akwai ma'aikatar da ya kamata a ware wa kudade da yawa, to ita ce ma'aikatar ƴada labaru,'' in ji Lai.

    Ya ce duk da cewa an yi watsi da gargadin da Amurka ta bai wa 'yan kasarta a Najeriya kan batun rashin tsaro a Abuja, amma ba a yi hakan ba yadda ya kamata na ganin hankalin 'yan Najeriya ya kwanta.

    Ya kuma ce abin damuwa shi ne duk da cewa a ware wa ma'aikatar naira biliyan 2.5 a matsayin kudaden kashewa a 2022, kashi daya bisa uku na kudin shi aka sak ware mata na shekarar 2023 wanda kuma ya kai naira miliyan 869.

  6. Kwankwaso ya ƙaddamar da manufofinsa na takarar shugaban Najeriya

    Kwankwaso

    Asalin hoton, Twitter/Kwankwaso

    A Najeriya, a yau ne dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar NNPP, Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya kaddamar kundin manufofinsa, wanda ya kunshi kudurce-kudurce da hanyoyin da zai bi wajen aiwatar da su idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya.

    Cikin manufofin har da aniyar inganta tsaro ta hanyar kara yawan jami`na tsaron, da kula da lafiyar mata masu juna biyu kyauta da kuma tsawaita amfani da sakamakon jarrabawar shiga jami'a, wato Jamb.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Gambia na ci gaba da bincike don gano maganin tari da ya kashe yara 70 a ƙasar

    Cough Syrup

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin kasar Gambia sun ce har yanzu ba su hakikance cewa magungunan nan da suka gurbata guda 4 ne musabbabin mutuwar akalla yara 70 a kasar ba.

    Da farko dai hukumar lafiyar ta duniya WHO ta danganta mutuwar yaran ga shan daya daga cikin magungunan 4 da aka shigo da su daga Indiya har ma ta fitar da gargadi ga sauran kasashen duniya.

    Hukumomin lafiyar na kasar Gambiya sun ce ba dukkan yaran 70 da suka rasu ba ne suka sha magungunan da suka gurbata.

    Suka ce duk da yake magungunan sune aka fi tuhuma da haddasa mace-macen, ana kuma samun matsalar kodar da yaran suka samu saboda wasu dalilan; amma suna ci gaba da bincike domin tabbatar da abin da ya yi sanadin mutuwarsu a hukumance.

    Kimanin yara 82 ne suka samu wannan matsalar tun daga watan Yulin bana amma 12 ne kawai suka kai labari.

    Hukumar WHO da kuma, binciken farko da ‘yansanda suka yi sun ta’allaka mace-macen da shan magunguna hudu da aka yi a kasar Indiya.

    Magungunan sun gurbata ne da sanadaran ake yin man da ke hana injinan mota toshewa saboda tsananin sanyi da kuma ruwan birki.

    Hukumomin kasar dai sun samu janye fiye da kwalabe dubu 40 na wadannan magungunan daga kasuwa tare da kwace lasisin fiton kaya na kamfanin da ya shigo da su.

    Kwamitin lafiya na Majalisar Dokokin Gambiya na gudanar da bincike kan lamarin kuma Shugaba Adama Barrow ya kafa wata hukumar binciken da ake sa ran ta bayar da shawarwarin hana afkuwar hakan a gaba.

  8. Mata da ƙananan yara ne aka fi cin zarafinsu a Afirka ta Kudu - Ramaphosa

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce mata da ƙananan yara ne aka fi ciwa zarafi a ƙasar.

    Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taro da fadarsa ta shirya kan nemo hanyar mafita kan cin zarafin da ake yi wa mata.

    Ya ce a baya-bayan nan, ana samun ƙaruwar aikata fyade da kuma kashe manyan mata, inda ya ce kamata ya yi a mutunta su a matsayinsu na uwaye ba wai kashe su ba.

    A cewar shugaban, alkaluman 'yan sandan ƙasar sun nuna cewa cin zarafin mata ya ƙaru da kashi 13 tsakanin shekarar 2017/2018 zuwa 2021/2022.

    ''Tsakanin zangon farko na shekarar 2021 da kuma zangon farko na 2022, an samu ƙaruwar kashe mata da kashi 52 da kuma kashi 46 na yaran da ake kashewa.'' in ji shugaban.

    A don haka, Ramaphosa ya yi kira ga maza da su kawo karshen aikata wadannan laifuka.

    Labaran cin zarafin mata ko ƙananan yara dai ba sabon abu bane a Afirka ta Kudu.

  9. Mutum uku sun mutu a fada tsakanin kungiyoyin asiri a Kwara

    Cult

    Mutum akalla uku sun rasa rayukansu bayan kazamar fada tsakanin kungoyiyin asiri a garin Kankatu da ke yankin Okelele na jihar Kwara.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an kashe daya daga cikin mutanen ne mai suna Abdulganiy a daren Litinin.

    Sai dai, wasu da ake kyautata zaton cewa suna kungiya daya da Abdulganiyun, nan take suka yi dirar mikiya zuwa wani wajen inda suka kashe wani Adebayo Yitta.

    Wani shaida ya bayyana cewa da isar su wurin, nan take suka harbe mutumin da kuma barinsa jina-jina, inda daga baya rai ya yi halinsa.

    Ganau din ya kuma ce mutane da ke zaune a wajen da lamarin ya rafu sun fara tserewa saboda fargabar kawo harin ramuwar gayya.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce ba shi da masaniyar faruwar lamarin amma za su gudanar da bincike.

    Shugaban al'ummar yankin ta Ibagun, Malam Sakariyau Ilufemiloye, ya yi Alla-wadai da kisan da mambobin kungiyoyin asirin suka yi.

  10. Kotu a Amurka za ta gurfanar da mutumin da ake zargi da kai wa mijin Nancy Pelosi hari

    Pelosi

    Asalin hoton, Reuters

    Kotu a Amurka za ta gurfanar da mutumin da ake zargi da kai wa mijin Nancy Pelosi, shugabar majalisar dokokin ƙasar hari.

    Ana zargin mutumin mai suna David DePape da yunkurin kisan kai, inda kuma ake tuhumarsa da yin dirar mikiya zuwa gidan ma'auratan a ranar Juma'a da ta gabata.

    Miss Pelosi ita ce dai mai girman mukami na biyu bayan shugaban kasa, ta yi balaguro lokacin da abin ya faru.

    A yanzu dai Paul Pelosi mai shekara 82 na murmurewa daga raunukan da ya samu bayan kai masa harin.

  11. Kotu a Bauchi ta yanke wa wani saurayi da ya kashe abokinsa hukuncin kisa

    Court

    Asalin hoton, Court

    Wata babbar kotu a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kama shi da laifinsa kashe abokinsa.

    Jaridar Punch ta ruwaito a yau cewa alkalin da ya yanke hukuncin Mai Shari'a Faruq Sarki, ya samu mutumin da laifin kashe abokin nasa ne ta hanyar yanka wuyansa da ƙwaƙule masa ido ya saka su a cikin kwalba kafin daga bisani ya binne shi a wani wajen daban.

    Lauyoyin da suka shigar da ƙarar daga Ma'aikatar Shari'a ta jihar Bauchi, Mohammed Ibrahim da Salihu Haruna da Ali Yusuf sun zargi saurayin da kisan kai inda suka kafa hujja da cewa shi ma hukuncinsa kisa ne idan aka yi la'akari da sashe 221 na kundin dokar Penal Code.

    Masu shigar da ƙarar sun shaida wa kotu cewa wanda ake zargin mai suna Musa Hamza ɗan ƙaramar hukumar Alkaleri, ya yaudari abokin nasa Adamu Ibarhim mai shekara 17, ya dake shi a ido da wani sanda sannan ya cire kansa da idanuwansa biyu, daga bisani kuma ya binne shi.

    Da farko dai matashin ya yi watsi da zargin da ake yi masa ɗin a gaban kotun, amma daga baya ya amsa laifin.

    Masu shigar da ƙarar sun gabatar da shaidu shida a yayin shari'ar yayin da mai kare wanda ake ƙarar ya gabatar da shaida ɗaya kawai.

    Shaidun sun ce mahaifin yaron da aka kashe ɗin ya kai ƙorafin cewa ɗansa bai koma gida ba, amma ya samu bayani cewa an gan shi da wan ake zargin a tare da daddare.

    Daga baya an tsannanta bincike inda aka gano wayar marigayin a hannun wanda ake zargi da kashe shin.

  12. Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ba da hakuri "kan sakacinta" a mutuwar mutum 156

    Ministan harkokin cikin gida a Koriya ta Kudu ya bayar da hakuri, inda ya amsa cewa akwai sakaci daga bangaren gwamnati, a turmutsutsin da ya faru ranar Asabar.

    Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 156, da ke halartar bikin kalankuwa na Halloween a Itayawan.

    Lee Sang-Min ya yi amai ya lashe, bayan tun da farko ya kare rundunar 'yan sandan kasar daga zargi.

    Wakiliyar BBC ta ce shi ma Sifeta Janar na ƴan sandan ya amsa cewa rundunarsa ta gaza yin abin da ya kamata ta yi, duk da samun kiraye-kiraye ta waya cewa bala'in na iya faruwa saboda tsananin cikar da aka yi.

  13. Sarauniyar Giwayen Kenya ta mutu tana da shekara 65

    Twitter/ KWS

    Asalin hoton, Twitter/ KWS

    Masu kula da gandun daji a kasar Kenya na makokin mutuwar fitacciyar giwar kasar da aka fi sani da 'Sarauniyar' giwayen kasar tana da shekara 65 a gandun dajin Tsavo da ke gabashin kasar.

    Hukumar kula da namun dajin kasar ta ce giwar ta mutu ne sakamakon yawan shekaru.

    Tsohuwar giwar - mai suna Dida wadda kuma aka fi sani da 'Sarauniyar giwaye' - ta sha tsallake kalubale da dama a kasar kamar farin da kasar ke fuskanta.

    A wasu jerin sakonni da ma'aikatan gandun dajin kasar suka yi ta wallafawa a shafukansu na Tuwita, sun bayyana kaduwa da alhininsu bayan mutuwar 'sarauniyar Giwayen'.

    Gandun dajin ya bayyana Dida a matsayin giwar da gandun dajin ba zai taba mantawa da ita ba.

    Haka kuma an bayar da rahoton mutuwar wasu giwayen biyu a gandun dajin Imenti na kasar.

    A 'yan watannin baya-bayan nan dai ana samun karuwar yawan mace-macen dabbobin dawa, lamarin da ya haddasa mutuwar giwaye sama da 100 a gandun dazukan kasar da daban-daban, kamar yadda gidauniyar kula da namun daji ta Afirka ta bayyana.

    Masu kula da gandun dajin na ganin hakan a matsayin wani koma baya ga fannin tattalin arzikin kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. NDLEA na neman kasurgumin mai fataucin miyagun kwayoyi ruwa a jallo

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ayyana neman - fitaccen mamallakin Otal din Adekaz, Ademola Kazeem - ruwa a jallo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da halasta kudin haram.

    Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, ya ce matakin bayyana nemansa ruwa a jallon ya biyo bayan rashin amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.

    Mista Femi ya ce hukumar na zargin mista Ademola da daukar nauyin wasu masu safarar kwayoyin da hukumar ta kama suna yunkurin fitar da kwayoyin zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen duniya.

    Ya kara da cewa “Bayan da muka kama wani direba wanda yaronsa ne mai suna Bolujoko Muyiwa Babalola, a watan Yuni ranar 27 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da Legas, sai Alhaji Ademola Kazeem wanda shi ne shugaban kamfanin Adekaz Global Integrated Services ya yi batan dabo''.

  15. Sojojin Mali da na Rasha sun kashe mutum 13 a wani samame

    Sojoji

    Asalin hoton, AFP

    Akalla mutum 13 ne suka mutu bayan wani samame da sojojin Mali da wasu - wadanda da 'yan kasar suka kira - 'sojojin hayar Rasha' karkashin kungiyar Wagner..

    Sun ce dakarun Malin da sojojin hayar, sun kaddamar da samamen ne kan al'umar Fulani.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito mazauna garin na cewa an kashe wata mata tare da danta a lokacin samamen da aka kaddamar a kauyen Guelledje na garin Tenenkou da ke yankin Mopti.

    An kuma kama wasu mutanen da ake zargi da 'yan jihadi ne a lokacin samamen.

    Kungiyar ci gaban al'umar Fulani ta kasar ta ce fiye da fafaren hula 20 ne aka kashe a yankin, ikirarin da sojojin Malin suka musanta.

    An dade dai ana zargin sosjojin Mali da cin zarafin fararen hula, ciki har da dakarun Majalisar Dinkin Duniya na (Minusma) wadda ta yi zargin cewa Malin ta dauki hayar sojojin Rasha ta hanyar kungiyar Wagner mai aiki a wasu kasashen Afirka.

    Zargin da Malin ta sha musantawa tana mai cewa kasar tana aiki da sojojin Rasha ne saboda kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu.

    A baya dai kasar Rasha ta musanta hannu a kungiyar dakarun Wagner.

    Kasar Mali dai na fuskantar rikice-rikicen tsaro da na siyasa da ke da alaka da ayyukan masu ikirarin jihadi tun shekarar 2012.

  16. Magoya bayan Bolsonaro sun rufe tituna bayan shan kaye a zaben Brazil

    Direbobi

    Asalin hoton, Getty Images

    Direbobin manyan motoci wadanda ke mara wa shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro baya, sun toshe tituna a fadin kasar, bayan da shugaban kasar ya sha kaye a zaben zagaye na biyu da aka gudanar a karshen mako.

    Rahotonni sun ce an toshe tituna a a duka jihohin kasar in banda guda biyu, lamarin da ya haddasa cunkoso tare da shafar jigilar kayan abinci a fadin kasar.

    Sakamakon zaben ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Luiz Inácio Lula da Silva ne ya yi nasara da dan karamin rinjaye kan abokin karawarsa, kuma shugaban kasar Jair Bolsonaro.

    Mista Bolsonaro dai bai kalubalanci sakamakon zaben ba, duk kuwa da cewa bai bayyana amincewa da shan kayen ba.

    Akwai fargabar cewa shugaban kasar zai haifar da rudani a kasar cikin watanni biyu da suka rage kafin ya mika mulki ga sabon shugaban kasar.

    Za dai a rantsar da zababben shugaban kasar ranar daya ga watan Janairun 2023.

    Brazil

    Asalin hoton, Reuters

    Brazil

    Asalin hoton, Reuters

  17. Wani gini ya kama da wuta bayan fashewar wani abu a Legas

    wuta

    Asalin hoton, others

    Wani gini da ke kan titin Adeola Odeku a yankin Victoria Island na jihar Legas ya kama da wuta.

    Gobarar ta tashi ne sakamakon wani injin janareto da ya kama da wuta da safiyar ranar Talata.

    Wani shaida ya fada wa Jaridar The Cable a Najeriya cewa wata motar fasinja dauke da mutum uku ta kama da wutar bayan da ta tsaya a gefen ginin da ke ci da wutar.

    Wutar ta shafi ababen hawa da wasu gine-ginen da ke kusa da inda lamarin ya faru.

    Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA Nosa Okunbor, ya ce jami'an su na wajen da wutar ta kama domin kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.

  18. Kotu ta tsare wasu matasa kan sata a gidan Patience Jonathan

    Patience Jonathan

    Asalin hoton, others

    Wata babbar kotun jihar Ribas da ke zamanta a birnin Fatakwal ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari saboda da zargin fashi da makami a gidan matar tsohon shugaban Najeriya Patience Jonathan.

    Ana tuhumar matasan da laifuka biyar da suka hadar da hadin baki, da sata, da fashi da makami, da kuma yunkurin kisan kai.

    Ana dai zargi mutanen hudu da kutsawa gidan matar tsohon shugaban kasar wanda ke unguwar GRA a birnin Fatakwal inda suka saci kayayyaki na miliyoyin nairori.

    Zargin da matasan hudu duka suka musanta bayan karonto musu tuhumar a gaban gotu.

  19. Hukumomin Abuja sun shawarci mazauna birnin su sanya kyamarorin tsaro a gidajensu

    Muhammad Musa Bello

    Asalin hoton, FACEBOOK/Muhammad Musa Bello

    Hukumomin Abuja babban birnin Najeriya sun shawarci mazauna birnin da su saka kyamarorin tsaro a gidajensu domin sama wa gwamnati saukin magance matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

    A wata sanarwa da babban daraktan hukumar fasaha da sadarwa na birnin Muhammad Sule ya fitar, ya ce hukumomin birnin sun bayar da shawarar ne a yayin zaman majalisar zartarwar birnin da aka gudanar a gundumar Gwarimpa.

    Sanarwar ta ce "sanyan kyamarorin tsaron zai taimaka wa hukumomi wurin tabbatar da tsaro a birnin'.

    Taron - karkashin jagorancin babban sakataren birnin tarayya Mr Olusade Adesola, wanda ya wakilci ministan tarayya Malam Muhammad Bello - ya samu halartar manyan sakatarorin hukumomin birnin daban-daban.

  20. Ana ci gaba da bayyana alhinin rasuwar Ifeanyi dan gidan Davido

    Ifeanyi

    Asalin hoton, Chioma

    Ana ci gaba da bayyana alhinin mutuwar dan gidan shahararren mawakin nan na Najeriya Davido wato Efeanyi.

    Tun da asubahin ranar Talata ne rahotanni ke cewa yaron mai shekara uku ya rasu ne bayan ya faɗa wurin ninƙayan da ke cikin gidan Mahaifin nasa, kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar.

    Daga cikin wadanda suka bayyana alhinin har da dan takarar shugaban Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubukar, wanda ya ce ''Ina mika sakon jaje da addu'a ga Davido da Chioma da daukacin iyalan Adeleke a wannan lokaci. Ina addu'a ga Allah da ya karfafe su tare da ba su hakurin jure wa rashin''

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Shi ma shararren mai wasan barkwancin nan na kasar AY ya bayyanar rasuwar yaron da cewa mutuwa ce da ba a saba gani ba, kuma abin takaici

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

    Ita ma fitacciyar mawakiya Waje ta yi kira ga al'uma da su sanya iyalan Davido cikin addu'o'insu domin nuna alhini a gare su.

    Ta ce ''babu abin da iyalan ke bukata a yanzu sai addu'o'i, da nuna soyayya da goyon bayanmu garesu''

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Shi ma mawakin nan mai suna The Guy, ya ce wannan rana ce ta bakin ciki ''Ina mika sakon ta'aziyya ta zuwa ga Davido da matarsa Chioma''

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3