Buhari ya bukaci 'yan sanda su zama 'yan ba ruwanmu a zaben 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Buhari zai tafi London domin a duba lafiyarsa

    Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kama hanyarsa zuwa London a yau dinnan domin a duba lafiyarsa.

    Kakakin shugaban, Femi Adesina a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ana saran Buhari zai koma gida a cikin mako na biyu na watan Nuwamba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Shugaban Najeriyan ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

    A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.

    Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

    A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.

  2. China ta gargadi Amurka da Australiya kan barazanar tsaronta

    China

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar China ta yi kira ga kasashen Amurka da Australiya da su yi duk mai yiyuwa wajen wanzar da zaman lafiyar yankin gabashin duniya.

    Kiran na zuwa ne bayan da rahotonni suka ce Amurka na shirin girke jiragen yaki shida masu harba muggan makamai a yankin arewacin kasar Australiya

    Kafar yada labaran Autraliya ta ABC ta ce za a tsugunar da jiragen a sansanin sojin sama na Tindall da ke arewacin Australiya.

    Ministan tsaron Australiya Matt Keogh, ya shaida wa manema labarai cewa ba ya tunanin samar da jiragen yakin Amurka a kasar zai iya kawo sabani tsakanin kasarsa da China.

    Kawo yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba game da lamarin.

    Samar da jiragen yakin masu harba makaman da za su ci dogon zango na akalla kilomita 14, zai kara wa Amurka karfi, a yayin da ake ci gaba da fargabar cewa China za ta yi amfani da karfin soji wajen kwace iko da Taiwan.

  3. 'Yan sanda sun kai samame masana'antar wayoyin iPhone na jabu

    iphone

    Asalin hoton, Elisio Francisco Gimo

    Hukumomin kasar Mozambique sun ce sun kwace wayoyin iphone na jabu kimanin 1,165, tare da kama wasu mutum biyu 'yan China bisa zargin gudanar da masana'antar, wadda ke Maputo babban birnin kasar.

    'Yan sanda sun ce ana zargin masu masana'antar da kera wayoyin iphone na jabu.

    Wadanda ake zargin dai sun musanta aikata ba daidai ba.

    Jami'an hukumar hana fasa kwauri ta kasar ta ce ta samu nasarar kama mutanen bayan da suka samu bayanan sirri.

    Babban daraktan hukumar mai kula da birnin Maputo Gino Jone, ya ce hukumarsa ta samu korafi game da zargin, inda suka kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba.

    Ya ce ''bayan binciken da muka gudananr na tsawon mako uku, sai muka gano masana'antar''.

    Ya kara da cewa ''Wani gini ne da ake gudanar da masana'antar, ana kera wayoyin tare kuma da sayar da su a wani shago da ke yankin Alto-Maè.

    iphone

    Asalin hoton, Elisio Francisco Gimo

  4. Akalla mutum 141 ne suka mutu sakamakon karyewar gada a Indiya

    Indiya

    Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo gawarwakin mutanen da suka nutse a kogi, sakamakon karyewar gada a gundumar Morbi da ke jihar Gujarata,

    Akalla mutum 141 ne suka mutu a karyewar tsohuwar gadar wadda aka gina tun zamanin mulkin mallaka.

    Indiya

    Akwai akalla jami'ai 500 daga hukumar kiyaye hadura da aukuwar bala'i ta kasar domin aikin ceton.

    Haka kuma jami'an sojin kasar na taimakawa wajen gudanar da aikin.

    Jami'an na amfani da kananan jiragen ruwa domin lalubo gawarwakin wadanda suka nutsen.

    Indiya
  5. AU ta umarci gaggauta tsagaita wuta a DR Congo

    DR KONGO

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarayyar Afirka ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a rikicin da ake gwabzawa a kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, inda 'yan tawaye ke kokarin kwace iko da wasu garuruwa a lardin gabashin kasar.

    Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, ta kori jakadan Rwanda a kasar, saboda zargin kasarsa da goyon bayan 'yan tawayen M23 wadanda suke barazana ga birnin Goma na DR Congo.

    Hakan ya biyo bayan sake kwace iko da wani gari a gabashin kasar da 'yan tawayen suka yi.

    Rwanda dai ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata na goyon bayan 'yan tawaye.

    Tarayyar Afirka ta umarci duka bangarorin da su zauna teburin sulhu, tana mai gayyatarsu zuwa taron sulhu a Kenya a watan gobe.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Jami'an tsaro sun kai samame gidajen karuwai tare da kubutar da 'yan mata 50

    Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Chief of Naval Staff

    Asalin hoton, Nig Navy

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta samu nasarar kubutar da 'yan mata 50, wadanda ta yi zargin cewa an tilasta musu shiga karuwanci a wasu gidajen karuwai biyu a birnin Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya.

    Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito jami'in hulda da jama'a na sansanin sojin ruwa da ke jihar Richard Iginla, na bayyana cewa a yayin samamen sun kama mutum uku da suke zargi da safarar 'yan matan -wadanda wasunsu shekarunsu ba su fi 14 ba - domin tilasta musu yin karuwanci.

    Ya ce Sun kaddamar da samamen ne tare da hadin gwiwwar hukumar yaki da safarar bil-adama ta kasar wato (NAPTIP) da kuma rundunar tsaro da Civil Defence.

    Ya ci gaba da cewa ''Mun samu bayanan sirri daga hukumar NAPTIP, wadda ta dade tana bibiyar gidajen karuwan da ake tilasta wa mata galibinsu 'yan mata yin karuwanci. Daga nan sai muka shirya rundunar hadin gwiwwa cikin gaggawa muka kuma samu nasarar kubutar da wadannan mata''.

  7. An kai hare-haren makamai masu linzami a wasu biranen Ukraine

    Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Ukraine sun Rasha ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami a sassan kasar, ciki har da Kyiv babban birnin kasar, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki da daukewar ruwa a wasu yankunan kasar.

    An bayar da rahoton tashin boma-bomai biyu a birnin Kyiv. Daya daga cikin mazauna birnin ya shaida wa BBC cewa wutar lantarki ta katse a gundumar da yake zaune.

    Hukumomin yankin arewa maso gabashin birnin Kharkiv, sun ce an lalata abubuwan more rayuwa da dama a yankin.

    Hare-haren na zuwa ne bayan da Rasha ta zargi Ukraine da kai hari da jirage marasa matuka kan tawagar jiragen ruwanta a cikin tekun Bahrul-Aswad da ke yankin Crimea.

    An kuma samu rahotonnin hare-haren makamai masu linzami a yau Litinin a tsakiyar yankunan Vinnytsia, da Zaporizhzhia a kudu maso gabashi, da kuma yankin Lviv da ke yammcin Ukraine.

  8. Ghana na fama da matsin tattalin arziki mafi muni - Nana Akufo Addo

    JOHN MACDOUGALL

    Asalin hoton, JOHN MACDOUGALL

    Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya bayyana cewa kasar na fama da matsin tattalin arziki mafi muni a tarhi.

    A wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin ɗin ƙasar a jiya Lahadi, Shugaba Addo ya bayyana cewa suna cikin matsala.

    Darajar kuɗin ƙasar ta ragu da kashi 50 cikin 100 a bana kuma an saka kuɗin kasar a jerin kuɗaɗen duniya da darajarsu ta fadi.

    Shugaban kasar ya ɗora alhakin faɗuwar darajar kuɗin na sidi kan yaɗa jita-jita, da kuma ƴan kasuwar canji na bayan fage inda ya ce babban bankin ƙasar a shirye yake ya yi dirar mikiya kan waɗanda ke da hannu a wannan lamari.

    Farashin mai na ci gaba da tashi a ƙasar kuma an samu hauhawar farashi da kashi 37 cikin 100.

    Cikin matakan da shugaban zai ɗauka, har da rage kashi 30 cikin 100 na albashinsa da mataimakinsa da ministoci da wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati

  9. Assalamu alaikum

    Masu binmu a wannan shafi na kai-tseye barkan mu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Ku kasance tare da mu domin kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai jagoranci shafin a daidai wannan lokaci, dafatan za ku ji dadi kasancewa tare da mu.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.