Mu kwana lafiya
Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai-tsaye, a nan muka zo karshen rahotanni da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai-tsaye, a nan muka zo karshen rahotanni da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.

Asalin hoton, UKRAINE GOVERNMENT
Firaministan Ukraine ya ce sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da Rasha ta kai sun yi mummunar illa ga ababen more rayuwa a ƙasar.
Denys Shmyhal ya ce wutar lantarki ta lalace a bakwai daga cikin yankuna goma da hare-haren suka shafa, inda lamarin ya shafi ɗaruruwan garuruwa.
Ruwan famfo ya dawo a babban birnin ƙasar Kyiv, bayan da wutar lantarki ta ɗauke a cibiyoyin da ake tura ruwan, amma magajin garin birnin Vitali Klitchko ya ce, babu ruwa a kusan kashi 40 cikin 100 na gidaje.
Ya ce injiniyoyi suna aiki tuƙuru don ganin an gyara wutar da ƙarfe tara ko goma na daren yau agogon ƙasar.
Shugaban yankin ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai matukar wahala amma ana shawo kan al'amura.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan bindiga na ci gaba da kai jerin hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina, inda suka kashe mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu jama’a domin karbar kudin fansa da kuma dabbobi masu yawa.
Rahotanni na cewa gomman mutane sun rasa ransu a cikin hare-haren da 'yan bindigan suka kai.
Sun kuma sace shanu a yankin gwadawaba da kauyen Kiri na yankin gada a jahar Sokoto, inda suka kashe a kalla mutane 5.
Hukumar yan sandar Najeriya a jihar ta Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin.
A jihar zamfara ma mai makwabtaka da Sokoto, 'yan fashin dajin sun kai hari yankin nasarawar burkullu.
Wani mazaunin garin Yan Kaba na Kauran Namoda ya shaidawa BBC cewa 'yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane.
Rundunar 'yan sandan jihar ta Zamafar ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce tuni aka kara daukar matakan tsaro da kuma dakile kai wasu hare-hare a yankin.
A yankin funtuwa ma na jahar Katsina yan bindigar sun tafi da akalla mutum 33 baya ga kashe wasu.
Yankin arewa maso yammacin dai Najeriya na fuskantar hare-haren 'yan bindiga a daidai lokacin da aka soma yakin neman zaben 2023.

Asalin hoton, Reuters
Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke Hague ta buƙaci babban mai shigar da ƙararta ya fara gudanar da jerin bincike kan zarge-zargen miyagun ayyukan da aka aikata a Afghanistan.
Sama da shekara biyu ke nan, aka dakatar da binciken bayan hamɓararriyar gwamnatin Afghanistan ta nemi Kotun Manyan Laifuka ta ba ta lokaci don yin nata binciken.
Kotun ta umarci gudanar da wani bincike ba kawai a kan laifukan yaƙin ƙungiyar Taliban ba, har ma da zarge-zargen da ake yi wa dakarun sojin Amurka.
Sai dai babban mai shigar da ƙaran, Karim Khan, a bara ya ce ba zai dubi aikace-aikacen dakarun Amurka ba a cikin binciken saboda 'yan Taliban da ƙungiyar IS ne suka aikata laifuka mafi muni a ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun soki lamirin shawarar ƙin haɗawa da dakarun Amurka a cikin binciken.

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Paul Pogba, ba zai buga wa ƙasarsa ta Faransa wasa ba a gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci saboda rauni da ya samu a gwuiwarsa, inda a yanzu yake ci gaba da murmurewa.
Pogba mai shekara 29, bai buga wa Juventus wasa ba tun fara fara kakar gasar Serie A ta bana bayan da ya sake komawa kungiyar daga Manchester United.
Dan wasan ya samu rauni a gwuiwarsa a watan Yuli, inda da farko yaki amincewa da a yi masa aiki a kafar tasa domin kada ya kasa zuwa gasar ta cin kofin duniya.
Faransa za ta fara kare kofinta a ranar 22 ga watan Nuwamba, inda za ta barje gumi da ƙasar Australiya.
Donald Trump ya miƙa buƙatar gaggawa ga Kotun Ƙolin Amurka da ke neman ta hana kwamitin Majalisar Dokokin ƙasar mai rinjayen 'yan Dimokrat, samun bayanan dukiyar da ya kamata ya biya wa haraji.
A makon jiya, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukunce-hukunce guda biyu na ƙaramar kotu da ke umartar tsohon shugaban ƙasar ya ba su bayanan dukiyar tasa.
Lauyoyin Mista Trump sun ce gaskiyar dalilan da suka sa ake neman bayanan harajinsa ita ce neman ɓata shi a siyasance, daidai lokacin da yake neman sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Kwamitin Majalisar Dokokin mai ƙarfin faɗa-a-ji na neman bin diddigin kuɗaɗen harajinsa tun bayan da ya zama shugaban ƙasa na farko a cikin shekara 40 da ya ƙi fitar da irin waɗannan bayanai bainar jama'a.

Asalin hoton, OTHER
Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Dosso, Djermakoye Maidanda Hamadou Seydou rasuwa.
Sarkin ya rasu ne yau Litinin yana da shekaru 99 a birnin Dosso da ke jamhuriyar Nijar.
Djermakoy Maidanda Hamadou Seydou shi ne Sultan na farko a masarautar ta Dosso .
Shi ne zarmakoye na 24 da ya hau karagar mulki a ranar 13 ga watan oktoba na shekara ta 2000.
An haife shi a ranar 8 ga watan Maris na 1923 a garin Dosso. Ya shiga makarantar Faramari a 1931, inda ya karanci sashen hada magunguna.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jami'an 'yan sandan ƙasar da su zama 'yan ba ruwana tare da da bijiro da shirye-shirye da za su taimakawa waje ganin an samu sahihin sakamako a zabukan 2023 da ke tafe a fadin ƙasar.
Buhari ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin wani bikin ƙarawa juna sani na kwana uku da aka shiryawa manyan jami'an 'yan sandan ƙasar domin duba matsalolin barazanar tsaro da ake fuskanta wadanda kuma ake ganin za su kawo cikas a zabukan.
Da yake tabbatar musu da cikakkiyar goyon bayansa gabanin zabukan na 2023, Buhari ya nuna jin dadinsa kan irin sauye-sauye da aka samu a karkashinsa wadanda kuma ke kawo ci gaba musaman ta yadda 'yan sanda ke gudanar da ayyukansu cikin korewa yanda doka ta tanada.
''A don haka therefore, na hori sufeto janar na 'yan sanda da ya tabbatar da cewa an bai wa kowane dan kasa dama da kuma hakkinsa na zabar wanda yake so kamar yanda tsarin mulki ya tanada, domin kuma ganin cewa sakamakon zabe ya kasance zabin mutane,'' in ji Buhari.
Shugaban ya kuma kara nanata zimmar sa na ganin an gudanar da zabuka masu tsafta cike kuma da gaskiya a shekara ta 2023.
Shi ma da yake magana, gwamnan jihar ta Imo, Hope Uzodinma, ya yi kira ga 'yan sandan ƙasar da su kawo tsare-tsare na wajabtawa 'yan ƙasar shan rantsuwar cewa ba za su tayar da tarzoma ba lokacin gudanar da zabe.
Da yake mayar da martani, Sufeton yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya tabbatar wa shugaban da 'yan Najeriya cewa rundunar za ta yi aiki wajen ganin zabukan na 2023 sun tafi yadda ya kamata ta hanyar bijiro da tsare-tsare kan sha'anin tsaro da kuma kyautata yanayin siyasa a ƙasar.

Asalin hoton, AFP
Dubban masu zanga-zanga ne suka fito maci a birnin Goma da ke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda suke zargin Rwanda da marawa 'yan tawayen M23 baya, abu kuma da ya sa Kongon ta dakatar da jakadan Rwanda da ke ƙasarta.
Sai dai ƙasar Rwanda ta musanta zargin.
Gabashin Kongo dai na fuskantar ƙaruwar hare-hare a wannan watan n Okotoba yayin da 'yan tawayen na M23 ke ci gaba da kokarin dannawa zuwa birin Goma.
Jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na cikin shirin ko-ta-kwana.
'Yan tawayen na M23 wadanda yawanci suka fito daga kabilar Tutsi, sun dawo kai hare-hare a shekarar da ta gabata bayan tsagaita wa na shekaru da dama.
'Yan tawayen sun zargi Kinshasa da gaza aiwatar da yarjejeniya da suka cimma na daukar mambobin zuwa cikin rundunar sojin ƙasar.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, OTHER
Matasa a birnin Bauchi sun fito zanga-zanga a yau Litinin tare da toshe babbar hanyar zuwa jihar bayan kisan wani mutum mai shekara 67 mai suna Adamu Babanta da ke zaune a yankin Yelwa Labura na jihar.
Tun da sanyin safiya da misalin 7, matasan suka yi dirar mikiya a kan babbar hanyar Bauchi -Tafawa Balewa a gaban kwalejin aikin gona, inda suka toshe hanyar tare da kawo cikas wajen wucewar ababen hawa, wanda hakan ya sanya da yawa komawa amfani da wata hanya.
Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa makwabcin mutumin ne mai suna Mohammed Damina Galadiman Dass ya buge shi da motarsa wanda kuma ya kai ga mutuwarsa.
Wani dan uwan mamacin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ana zargin wanda ya kashe dan uwan na sa da yunkurin yin lalata da wata yarinya mai shekara 18 mai suna Khadija da kuma ta kasance 'ya ga marigayin.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce an shawo kan matasan da suka fito zanga-zanga tare da girke jami'an tsaro domin samar da zama lafiya a yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Akalla fasinjoji 13 ne suka kone kurmus a hadarin mota a jihar Enugu.
Hadarin ya auku ne a jiya Lahadi a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal kusa da asibitin koyarwa na Jami'ar Najeriya Nsukka a Itulu-Ozalla.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa motar bas ce mai daukar mutum 14 da ta fito daga Imo zuwa Adamawa ne ta yi taho mu gama da wata tirela, inda nan take suka kama da wuta.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen Enugu, Mista Joseph Toby, ya nuna takaicinsa, inda ya ce har ya zuwa yanzu ba a gama tantance wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Asalin hoton, AFP
Wata kotu ta musamman a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ta yanke hukuncin farko a zaman da take yi na mutanen da suka aikata laifukan yaki a kasar, inda ta daure mayaka uku saboda hannu a laifukan ƴaki a 2019 a arewa maso yammacin kasar.
Hukuncin kotun da aka kafa a Bangui shekaru hudu da suka gabata ta yanke kan wadanda suka aikata laifukan ƴaki ya kasance irin sa na farko kuma mai cike da tarihi a kasar.
Kotun ta yanke wa Issa Sallet da Ousman Yaouba daurin shekara 20 a gida yari, yayin da Tahir Mahamat kuma aka yanke masa hukuncin kisa saboda kashe gomman fararen hula a arewa maso yammacin ƙasar a 2019.
Har ila yau, wata babbar kotun sauraron manyan laifuka a Hague, na zargin wasu jagororin kungiyoyin mayaka da dama da aikata laifukan ƴaki a ƴakin basasar ƙasar.
'Yan tawaye ne dai ke rike da kashi biyu bisa uku na ƙasar, wacce take farfadowa daga ƴakin basasa.

Asalin hoton, AFP

A yau ne al’ummar jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya suka wayi gari da matsalolin rashin motocin haya, tun bayan da masu motocin bas suka shiga yajin aikin gargadi na tsawon kwana bakwai a fadin jihar.
Direbobin motocin haya dai na zargin ma’aikatan karbar haraji na motocin haya da aka fi kira Agbero, da karbar kudi fiye da ƙima da sunan haraji daga direbobin.
Sun yi barazanar shafe tsawon kwana biyar zuwa bakwai suna yajin aiki, idan har gwamnatin jihar ba ta kakkaɓe hannun Agbero daga kan tituna da sunan karbar haraji daga motocin bas a jihar ba.
Da yawa daga titunan jihar sun kasance fayau babu alamar motocin bas na haya, sa’ilin da fasinjoji suka zama abin tausayi, inda masu motocin ne kadai ke kaiwa da komowa.

Dubban fasinjoji ne suka cika a kan manya da ƙananan titunan birni da kewayen jihar Legas.
Tuni al’ummar jihar suka fara ji a jikinsu sakamakon wannan yajin aiki da direbobin motocin hayar suka fara daga yau Litinin.
Wasu daga cikin fasinjoji sun yi amfani da duk wata kafa da ta rage mu su domin zuwa wuraren aiki ko kasuwanci, inda wasu suka hau motocin titiri wasu kuma suka samu tallafi daga motocin da ba na haya ba zuwa guraban harkokinsu. Wasu kuwa sun hakura sun koma gida.

Direbobin dai sun alakanta mambobin Agbero da zargin tursasawa da karbar wadannan kudade cewa akwai hannun kungiyar masu daukar ma’aikatan motocin haya ta (RTEAN) da kuma kungiyar NURTW da hannu a ciki.
Wasu daga cikin direbobin dai sun bayyana rashin jin dadinsu da matakan mambobin kungiyoyin kula da tashoshin.
Ukraine ta ce Rasha ta kaddamar da hare-haren makami mai linzami a fadin ƙasar har da Kyiv babban birnin ƙasar, inda ake ta jin karar ababen fashewa.
Jami'ai a Kyiv sun ce makaman kariya ne suka hana fadowar makamai masu linzami a birnin, amma sun ce hare-haren sun shafi bangaren wuta da kuma ruwan sha.

Hounan tauraron dan adam sun nuna wuta na ci gaba da ƴaduwa kan tsaunin nan mafi girma a Afirka Kilimanjaro duk da irin kokari da jami'ai ke yi wajen shawo kan ta tun da ta soma a ranar 21 ga watan Oktoba.
An sake samun barkewar wuta a bangaren gabashin tsaunin kusa da wajen shakatawa na Mawenzi, inda babu abin da ake iya hangowa sai tashin hayaki zuwa sama.
Mutane da ke zaune kusa da tsaunin sun ce suna ganin wutar na ci kusa da kauyensu da dare kamar yadda wani da ya wallafa hotuna da kuma bidiyo a shafinsa na Tuwita ya bayyana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
sama da mutu 500 da suka kunshi masu kashe gobara da jami'an gandun daji da masu yawon bude ido da kuma fararen hula ne ke ta kokarin ganin sun shawo kan wutar.
Sai dai gwamnatin Tanzania ta ce abubuwan da suka janyo wutar ke ci gada da bazuwa shi ne saboda fari na tsawon lokaci da kuma iska mai karfi, amma ta ce ba a san hakikanin abin da ya haddasa wutar ba.
A shekaru biyu da suka gabata, wutar daji da ta dauki tsawon mako daya tana ci, ta lalata dubban eka na filaye a kan tsaunin na Kilimanjaro.

Asalin hoton, others
Gwamnatin Najeriya ta bayyana gargadin baya-bayan nan da kasashen yamma suka yi na yiyuwar kai harin ta'addanci a Abuja da wasu sassan kasar da cewa abu ne da bai ''dace'' ba kuma bai ''kamata'' ba.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkoki tsaro Babagana Monguno ya shaida wa manema labarai cewa ''batun barazanar kai harin'' ba shi da wani tushe balle makama.
Manguno na jawabi ne bayan taron gaggawa na majalisar tsaron tsaron kasar wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Litinin.
Taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasar ya samu halartar manyan hafsoshin tsaron kasar.
Mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaron ya ce, an shawo kan matsalar tsaron birnin Abuja, dan haka a yanzu birnin ba ya cikin wata barazanar tsaro.
Mista Monguno ya ce ‘’bai kamata a saka 'yan Najeriya cikin fargaba da tashin hankali ba'' ya kara da cewa ''batun barazanar karya ce, kuma bai kamata wani ya rika tsorata mutane ba'.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Geofrey Onyeama ya ce gwamnatin kasar na aiki da takwarorinta na kasashen waje domin ingantuwar alaka tsakanin 'yan kasashen wajen da na Najeriya, ba tare da wani firgici ko tsoro ba.
A makon da ya gabata ne dai kasashen yamma irinsu Amurka da Birtaniya da Canada da Australiya suka fitar da jerin gargadin cewar akwai yiyuwar kai harin ta'addanci a birnin Abuja da wasu sassa na kasar, tare da umartar 'yan kasashensu da su tsayar da tafiye-tafiye zuwa birnin.
Har ma Amurka ta tabbatar da kwashe wasu 'yan kasarta tare da kananan ma'aikatan ofishin jakadancin kasar a Abuja.
Gargadin dai ya sanya 'yan kasar da dama cikin fargaba da tsoro.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro ciki har da ayyukan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da ayyukan 'yan fashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa, da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Asalin hoton, Xaume Olleros/Bloomberg
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen taya sabon zababben shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva murnar lashe zaben da aka gudanar a kasar.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce yana fatan sabon shugaban kasar zai karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
''Ina fatan yin aiki da sabon zababben shugaban kasar domin ci gaba da karfafa dankon zumuncin da alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashenmu'', in ji sanarawa.
Lula ya yi nasara da karamin jinjaye kan abokin hammayarsa Jair Bolsonaro wanda har yanzu bai amince da shan kaye ba.

Asalin hoton, Getty Images
Sabon mamallakin kamfanin Tuwita Elon Musk ya ce za a sake duba hanyar da ake bi wajen tantance masu amfani da shafin.
Hakan na zuwa ne yayin da rahotonni ke cewa kamfanin zai fara cazar kwastomomin - da aka tantance shafinsu - dala 20 a wata.
Kwanaki bayan da ya sayi kamfanin Elon Musk ya wallafa a shafin nasa cewa za a sauya hanyar tantance masu amfani da shafin.
A halin yanzu dai tantance masu amfani da shafin - wanda ake saka wa shudiyar alama domin tabbatar da sahihancin shafin - kyauta ne.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai Mista Must ya kammala sayen kamfanin kan kudi dala biliyan 44.
Shugabannin Afirka sun bi sahun takwarorinsu na fadin duniya wajen taya sabon zababben shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva, wanda ya lashe zaben zagaye na biyu na shugaban kasar da aka gudanar karshen mako.
Shugaban Kasar Mozambique Filipe Nyusi ya ce Lula ya samu nasarar ne ta hanyar jajircewa da kaskantar da kai da kuma adalcinsa.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce kasarsa a shirye take wajen gina kyakkyawar alaka da kasar Brazil, wani abu da shi ma takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi ma Shugaban Senegal kuma shugaban Tarayar Afirka Macky Sall, ya mika sakon taya murnarsa ga sabon zababben shugaban na Brazil.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Hukumomin kasar Somaliya sun tabbatar da mutuwar mutum 120 a tagwayen hare-haren bom da aka kai Mogadishu babban birnin kasar ranar Asabar.
Ministan lafiyar kasar Haji Ali Aden ne ya tabbatar da wannan adadi ga manema labarai ranar Litinin a birnin Mogadishu.
An dai kai hare-haren biyu kan ginin ma'aikatar ilimin kasar, kuma 'yan bindigar sun buɗe wuta kan mai tsautsayi bayan tashin bama-baman a cikin ginin.