Na amince da takarar Atiku Abubakar - Wike

Asalin hoton, OTHER
Gwamnan Rivers da ke kudancin Najeriya Nyesom Wike ya tabbatar da mubaya’arsa ga Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Sai dai Wike ya ce yana nan a kan bakarsa cewar dole shugaban jam’iyyar ta Peoples Democratic Party Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Wike ya tabbatar da haka ne a wani taro da ya yi da ƴan takarar jam’iyyar na jihar Rivers a mataki daban-daban, a garin Port Harcourt, a daren Alhamis.
Wike ya ce ana iyakar bakin ƙoƙari wajen ganin an warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar sai dai wasu ƴan-ba-ni na-iya ne suke kawo cikas.
Ya ce “An gama zaɓen fitar da gwani. Na ce a cire ɗan takarar shugaban ƙasa ne?
Ko na ce a cire ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa? To mene ne kuma ake ba ni haƙuri a kai?
“Abin da nake cewa shi ne tunda kun samu ɗan takarar shugaban ƙasa to ku ba mu muƙamin shugaban jam’iyya.”
