Zelensky ya yaba wa Yariman Saudiyya saboda shiga tsakani a yakin Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Jabir Mustapha Sambo and Abdullahi Bello Diginza

  1. Macron na shiga tsakani a rikicin Rwanda da Congo

    Macron

    Asalin hoton, Rwanda Presidency

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da shugabannin Rwanda da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da samun tashin-tashina a kan iyakarsu kasashen biyu.

    Kasashen na Gabashin Afrika na samun rashin jituwa saboda ayyukan yan tawaye a kan iyaka.

    Ganawar na zuwa bayan shugaban Rwanda Paul Kagame ya fada a zauren Majalisar Dinkin Duniya cewa, ''nuna wa juna dan yatsa ba zai warware rikici ba''.

    Shi kuwa Shugaban Kongo Félix Tshisekedi ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, ya yadda ya yi aiki da yan tawayen M23, a kokarin ganin sun bar yankunan da suke rike da su, da kuma ganin al'umma sun koma gidajensu.

    Shugabannin uku sun yi kebabbar ganawa ce, a wani bangare na babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi yanzu haka a birnin New York.

    Kongo na zargin Rwanda da goyon bayan kungiyar yan tawayen ta M23, to amma gwamnatin ta shugaba Paul Kagame na musanta zargin.

  2. Ba ni da hurumin sanya Iyorchia Ayu yin murabus - Atiku

    Atiku

    Asalin hoton, AFP

    Dan takarar shugaban kasa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce ba shi da hurumin sanyawa ko hana shugaban jam'iyyarsu Iyorchia Ayu yin murabus.

    A sanarwar da ya fitar ya ce ''Ce- ce-ku-cen da ake yi kan neman shugaban jam'iyyarmu ya aiye aiki, ina so na nanata abin da na riga na fadi a baya cewa mataki ne da Dr Ayu kadai zai iya dauka, ni ko wani daban ba mu da hurumin yanke wannan hukunci''.

    Martanin na Atiku na zuwa ne jim kadan bayan bangaren Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya sanar da ficewa daga yakin neman zaben dan takarar a 2023, har sai Mr Ayu ya sauka daga kan mukaminsa kuma an nada sabon shugaba daga kudancin kasar.

    Nyesom Wike ya yi rashin nasara a zaben fid da gwani a hannun Atiku Abubakar, kuma tun daga lokacin ne ake ta kai ruwa rana da shi, a kokarin dinke barakar da ta kunno kai jam'iyyar.

    Daga cikin sharudan da Wike da 'yan korensa suka shimfida akwai bukatar shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu ya yi murabus.

    Sun ce ba zai yiwu a ce dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyya su fito daga yankin arewa ba.

  3. Adadin wadanda suka mutu a zanga-zangar Iran ya karu

    .

    Asalin hoton, Twitter

    Akalla mutum tara aka ruwaito sun mutu bayan zanga-zangar da ta barke a Iran sakamakon mutuwar wata mata a hannun jami'an tsaro.

    An tsare matar ne bisa zargin keta dokar saka hijabi a kasar.

    Daga cikin wadanda aka kashe akwai wani matashi mai shekaru 16, wanda jami'an tsaro suka harbe shi bayan sun buda wa masu boren wuta.

    Hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mata ke daga dankwali sama kafin su kona shi.

    An jiyo su suna cewa '' ba mu yadda da dankwali ba, ba mu yadda da rawani ba, mun yadda da yanci da daidaito''.

    A jawabinsa gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce suna bayan ''jajirtattun matan Iran da yanzu haka ke boren neman yancinsu''.

    Ya yi magana ne bayan martanin da Shugaban Iran din Ebrahim Raisi ya yi, na watsi da kiraye-kirayen kasashen Yamma na kira ga kasarsa ta martaba yancin mata.

  4. Budewa

    Barkanmu da wannan safiya ta Alhamis.

    Jabir Mustapha Sambo ke fatan kun tashi lafiya daga nan shafinmu na Kai-tsaye a bbchausa.com.

    Sai ku cigaba da kasancewa tare da mu don samun labarai da rahotanni da suka shafi rayuwarku.