Motocin daukar marasa lafiya sun taimaka wa mutanen da ke kan layin ganin gawar Sarauniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa kan shirye-shiryen jana'izar Sarauniya Elizabeth ll da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Bappa

  1. Dubban mutane sun taru domin tarbar Sarki Charles lll a birnin Cardiff

    .
    Bayanan hoto, Mutane na jiran isowar sarki Charles

    A nan gaba kadan ne a yau Sarki Charles lll zai ziyarci yankin Wales, inda dubban mutane suka taru domin yi masa maraba.

    A ziyararsa ta farko a matsayin Sarkin Birtaniya, Sarkin tare da matarsa za su halarci taron addu'o'in da za a yi wa Sarauniya a majami'ar Llandaff

    Jude daga birnin Cardiff na daga cikin dubban mutane da suka taru domin ganin sarkin, ta kuma ce ''Ina son mika sakon ta'aziyyar Sarauniya, domin kuwa shi ne babban abin da ya dace da ni."

    .
    Bayanan hoto, Anne Gainger

    Anne Gainger, mai shekara 58, wadda ta je Landan domin mika sakon ta'aziyyarta ga rasuwar Sarauniya, yanzu haka tana birnin Cardiff domin tarbar sabon sarkin.

    Ta ce ''ina son kasancewa a nan yau ne domin taya shi murnar zama sabon Sarki."

  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na bbchausa.com barkanmu da safiyar Juma’a.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke maraba da sake haduwa da ku a wannan shafi na kai-tsaye, inda a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Haka kuma za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.