Motocin daukar marasa lafiya sun taimaka wa mutanen da ke kan layin ganin gawar Sarauniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa kan shirye-shiryen jana'izar Sarauniya Elizabeth ll da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Bappa

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi a nan muka kawo muku karshen labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da suka faru a yau a fadin duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, sunana Aisha Shariff Baffa, nake cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Ya'yan Sarauniya sun je coci don yi wa mahaifiyarsu addu'oin dare

    'Ya 'yan Sarauniya hudu na yi mata addu'a

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, 'Ya 'yan Sarauniya hudu na yi mata addu'a

    'Ya 'yan Sarauniya Elizebeth sun fara zama don yi wa mahaifiyarsu Addu'a a dakin taron na Westminister.

    Sarki Charles da Gimbiya Anne da Yarima Andrew da kuma Yarima Edward, kowa ya kama wajen tsaiwarsa a kusa da akwatin gawar Sarauniya, don gudanar da abin da ake kira addu'a ga Sarauniyar.

    Za a shafe mintuna 15 ana addu'ar.

    A yammacin gobe ne su ma jikokin Sarauniyar za su gudanar da irin wannan addu'a.

    • An soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a PDP a Zamfara

      PDP
      Bayanan hoto, PDP

      An yanka ta tashi dangane da zaben dan takarar gwamna a jam`iyyar PDP, a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, bayan wata babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwanin da jam`iyyar PDP ta yi, in da Lawal Dare, ya samu nasarar zama dan takararta na gwamna.

      Kotun ta ce ta gamsu cewa ba a bi ka`ida ba wajen gudanar da zaben.

      Kotun tarayyar, wadda mai sharia Aminu Bappa, ya jagoranci zamanta a Gusau, babban birnin jihar, ta saurari karar da wasu mutum uku da suka nemi takarar gwamna a tutar jam`yyar PDP a jihar suka kai gaban ta, wanda suka hada da da Ibrahim Shehu Gusau da Malam Wadatau Madawaki da kuma Hafiz Muhammad Nahuce, wadanda suka kalubalanci zaben fidda gwanin na takarar gwamnan suna cewa an tabka kura-kurai tare da taka ka`idojin da kundin tsarin mulkin jam`iyyar ya tanadar, bayan Dr Dauda Lawal Dare ya samu nasara.

      Kotun ta ce ta gamsu da hujjojin da lauyan bangaren masu karar, wato Barrsiter Ibrahim Ali ya gabatar, kana ta soke zaben.

      Hukuncin da Lauyan ya ce ya musu dadi:

      To sai dai kuma lauyan dan takarar gwamnan da kotu ta soke zaben nasa, Dauda Lawal Dare, wato Barrsiter Masama ya ce akwai bukatar sai bayan sun yi nazarin hukuncin, kana za su san abin yi.

    • Matashiya ta mutu a yayin da ake tsare da ita a Iran

      Hukumomi a Iran, sun tabbatar da mutuwar, matashiyar nan da ta fara rashin lafiya lokacin da ta ke tsare a hannun jami'an tsaro.

      An garzaya da matashiyar Mahsa Amini, zuwa asibiti, sa'a guda bayan 'yan sandan tabbatar da tarbiyya sun kamata lokacin da suke tafiya tare da iyayenta a birnin Tehran, kan laifin sanya tufafin da bai dace ba.

      Mahaifiyarta ta shaida wa BBC cewa 'yan sanda ''sun kashe ma ta abar kaunarta''.

      'Yan sandan sun ce Mis Amini, ta gamu da ajalinta ne sakamakon bugun zuciyar lokaci guda, lokacin da aka kaita ofishinsu din yi mata nasiha da wa'azi.

      Wasu rahotanni sun ambato kawunta na cewa dukan tsiyar da su kai mata ne ya janyo rasuwarta, amma 'yan sandan sun musanta haka.

      Wannan lamarin ya janyo mummunar suka da tofin ala tsine ga rundunar 'yan sandan kasar, kuma tuni shugaba Ibrahim Ra'eesi, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar matashiyar.

    • Motocin daukar marasa lafiya sun taimaka wa daruruwan mutanen da ke kan layin ganin gawar Sarauniya

      Mutane a dogon layi

      Asalin hoton, EPA

      Bayanan hoto, Mutane a dogon layi

      Wasu mutane 435 sun kamu da rashin lafiya a yayin da suke kan layi ko kuma kusa da dogon layin ganin gawar Sarauniya in da motocin daukar marasa lafiya da jami'an lafiya a Landan suka rika yi taimaka musu.

      Yawancin mutanen dai suma suke ko kuma su yanke jiki su fadi har wasu daga ciki na jin rauni aka.

      Haka kuma akwai marasa lafiya 40 da aka garzaya da su asibiti a cewar hukumar lafiya ta Burtaniya.

      Hukumar lafiyar ta kuma gargadi wadanda ke da wata rashin lafiya da su tabbatar suna tafiya da duk maganin da suke amfani da shi saboda gudun shiga wata matsala.

      Sannan an umarci masu bin dogon layin ganin gawar Sarauniyar da su rinka shan ruwa sosai da kuma cin abinci a kan kari.

    • Yarima Edward da matarsa sun kai ziyarar bazata fadar Windsor

      Yarima Edward da matarsa Sophie

      Asalin hoton, Reuters

      Bayanan hoto, Yarima Edward da matarsa Sophie

      Dan autan Sarauniya Elizebeth da matarsa sun gaisa da masu zaman makoki a fadar Windsor Castle.

      Yarima Erdward da matarsa Sophie, sun yi magana da cuncurundon mutanen da ke wajen tare da karbar furannin da suka ba su.

      Yariman da mai dakinsa, sun kuma tattauna da masu raba abinci da ke aiki a fadar, sannan sun karanta sakonnin ta'aziyyar da aka ajiye a wajen kofar shiga wajen.

      Mutane a fadar sun rinka ihu bayan da suka ga Yariman da matarsa sun isa wajen.

    • Ghana ta ayyana cewa a yanzu ba bu cutar Marburg a kasar

      Kwayar cutar Marburgh

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Kwayar cutar Marburgh

      Ghana ta ayyana cewa cutar Marburg da ta bulla kasar a baya bayannan a yanzu ba bu ita bayan an shafe kwanaki 42 ba a samu wanda ya kamu da ita ba.

      Tun da farko mahukunta a kasar sun an karar da mutane cewa cutar wadda ta bulla a kasar na da matukar hadari in da ake danganta ta da Ebola, bayan da a watan Yuli aka samu mutum biyu da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

      Mutum ukun da suka kamu da cutar uba da da da kuma mahaifiyar jaririn dan watanni 14 da haihuwa, biyu sun mutu yayin da mahaifiyar kuma ta warke daga baya kuma aka sake gwada ta aka ga ta kamu da cutar.

      An rinka gwada mutane 200 da suka yi mu'amala da mutum ukun akai-akai amma daga bisani aka tabbatar ba su kamu da cutar ba.

      Wani babban jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar Dr Patrick Kuma-Aboagye, ya shaida wa manema labari cewa a yanzu ba bu cutar a Ghana.

      Daga nan ya gode wa Hukumar Lafiya ta Duniya da ma sauran kungiyoyin da suka taimaka wajen kawar da cutar a kasar.

      Wannan ne dai karon farko da aka gano cutar ta Marburg a yammacin Afurka.

      A bara an samu mutum guda da ya kamu da cutar a Guinea, to amma daga bisani aka tabbatar da cewa ba bu cutar a kasar.

    • Za a rufe bankuna tsawon kwana uku a Lebanon

      Bankuna a kasar Lebanon za su kasance a rufe tsawon Kwanaki uku a mako mai zuwa, bayan 'yan matsaloli da aka fuskanta a lokacin da kwastomomi suka yi kokarin kwashe dukannin kudinsu na ajiya.

      A ranar Juma'a an fuskanci takaddama lokacin da wasu dauke da bindigogin roba suka dira bankunan domin kwashe kudinsu na ajiya.

      Sakamakon tabarbarewar tattalin arziki na tsawon shekaru uku, bankuna a Lebanon sun saka tsauraran dokoki game da yadda kwastomomi za su cire kudinsu na ajiya.

      Irin dan barwar da ke ta faruwa a Lebanon wajen cire kudi ta samo asali ne daga ranar laraba -- lokacin da wata mata rike bindigar roba da kuma fetur ta bukaci a bata damar ta cire kudinta a banki saboda ta biya kudin maganin cutar kansa da kanwarta ke fama da ita.

    • Al'umar arewacin Najeriya sun mika sakon ta'aziyyar Sarauniya Elizabeth ll

      Sarkin Fulanin Legas
      Bayanan hoto, Sarkin Fulanin Legas

      A kokarin kyautata dadaddiyar alaka tsakanin shugabanni da Sarakunan arewacin Najeriya da tsarin sarautar Burtaniya, a yau wasu daga cikin sarakunan arewacin Najeriya mazauna jihar Legas sun kai ziyara ta musamman a karamin ofishin jakadancin Burtaniya da ke Legas.

      Ziyarar ta zo da mika sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Burtaniya ta hannun ofishin jakadancinta game da rasuwar Sarauniyar Elizabeth ll.

      Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Muhammadu Abubakar Bambado, wanda ya wakilci al’ummar arewacin Najeriya mazauna birnin na Legas ya shaida wa BBC cewa sun je karamin ofishin jakandancin ne domin yin ta'aziyyar saboda akwai kayakkaywar alaka tsakanin Burtaniya da al'umar arewacin Najeriya

      Ya kara da cewa ''Mun sa hannu kan rijistar ta'aziyyar, sannan na mika takardar gaisuwa a madadin al'umar arewa mazauna yankin kudu maso yammacin Najeriya."

    • Sarki Charles lll ya gana da shugaban gwamnatin yankin Wales

      .

      Asalin hoton, PA Media

      Bayanan hoto, Sarkin Charles da Mark Drakeford

      Sarki Charles lll ya gana da Shugaban gwamnatin yankin Wales Mark Drakeford a fadarsa da ke birnin Cardiff.

      Mutane da dama ne dai suka shafe sa'o'i masu yawa suna jiran isowar sarkin domin yi masa tarba, to amma duk da wannan sarkin ya hadu da wasu rukunin masu zanga-zangar adawa da mulkin Sarauta da suka taru a wajen fadar.

    • An yi wa Sarki Charles III ihun 'Ba ma yi' a Masarautarsa da ke Cardiff

      .
      Bayanan hoto, Masu zanga-zangar adawa da mulkin Sarauta a birnin Cardiff

      A yayin da sabon Sarkin Ingila Charles lll ya isa fadarsa da ke birnin Cardiff, mutanen wajen sun yi ta yi masa ihu tare da wakokin 'ba ma yi'.

      A yayin da daruruwan masu zanga-zanga suka taru a kusa da kofar fadar, a daya tsallaken kuma wasu mutane ne rike da allunan da ke dauke da sakonni da ke cewa 'A soke mulkin Sarauta' 'Ba ma son Charles' 'Mu dimokradiyya muke so'

    • David Beckham na kan dogon layin ganin gawar Sarauniya

      b
      Bayanan hoto, David Beckham

      An hango tsohon shararren dan kwallon Ingila da Manchester United David Beckham, cikin dogon layin ganin gawar Sarauniya Elizabeth ll.

      Da aka tambaye shi kan yawan lokacin da ya shafe a kan layin, tsohon dan kwallon ya ce ya shafe tsawon sa'a 12 a kan layin.

      Game da yadda alaka ta kasance tsakaninsa da mutanen da ke kan layin, Beckham ya ce sun yi alaka mai kyau, domin kuwa sukan raba wa junansu abinci da lemuka.

      Mutanen da ke kan layin dai sun yi ta daukar hotuna tare da fitaccen tsohon dan kwallon.

    • Najeriya da Morocco sun sanya hannu kan yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas

      Aikin mai nisan kilomita 7,000 zai ratsa sahara zuwa kasar Morocco

      Asalin hoton, NNPC

      Bayanan hoto, Aikin mai nisan kilomita 7,000 zai ratsa sahara zuwa kasar Morocco

      Kasashen Morocco da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta bayar da damar shimfida bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco.

      Aikin na tsawon kilomita 7,000 zai hade da bututun arewacin Afirka da ke tura gas zuwa kasashen Turai wanda ke arewacin Morocco.

      Shugaban kamfanin mai na Najeriya Mele Kyari ya shaida wa maharta taron sanya hannun wanda aka yi a birnin Rabat na kasar Morocco cewa aikin zai inganta walwalar jama'a tare da magance matsalar hamada da ake fuskanta a wasu yankunan yammacin Afirka.

      A watan da ya gabata ne kasar Algeriya ta daina amfani da bututun da ke bi ta Morocco zuwa Spain, abin da ya janyo wa Moroccon koma-baya ta fuskar man gas da kudin fito da kasar ke karba.

      A sanarwar da kamfanin na NNPC ya fitar ya ce aikin zai samar wa kasashen yammcin Afirka kudaden shiga ta hanyar karbar kudin fito na gas din da ke bi ta kasashensu.

      Kawo yanzu dai ba a san yaushe aikin zai kammala ba, wanda ake sa ran fitar da gas mai tarin yawa a kowacce rana.

    • Mali ta gargadi ECOWAS kan tsoma baki game da batun sojojin Ivory Coast da ke hannuta

      Gwamnatin mulkin soji a Mali ta soki batun neman taimakon ECOWAS domin sakin sojojin kasar 49 da aka kama a Mali tun cikin watan Yuli.

      A wata kakkausar suka da Malin ta yi ta ce batun sojojin abu ne da ta yi cikin doka, kuma batu ne da ya shafi kasashen biyu, dan haka ne gargadi ECOWAS da cewa ka da ta tsoma bakinta.

      sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Mali ba za ta lamunci bata suna da tursasawa ba.

      Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar tsaron Ivory Coast ta yanke shawarar kai batun gaban kungiyar ECOWAS saboda ta shiga tsakani ta hanyar shirya zaman tattaunwa tsakanin shugabannin kasashen biyu.

    • Sarki Charles lll tare da matarsa sun isa birnin Cardiff a yankin Wales

      .

      Asalin hoton, PA Media

      Bayanan hoto, Sarki Charles lll na Birtaniya

      Sarki Charles tare da matarsa Camilla sun isa birnin Cardiff da ke yankin Wales domin halartar taron addu'o'in tunawa da rayuwar Sarauniya Elizabeth a majami'ar Llandaff da ke birnin.

      Haka kuma ana sa ran sarkin zai gana da shugaban gwamnatin yankin na Wales Mark Drakeford tare da Sakataren gwamnatin yankin Sir Robert Buckland, tare da wasu man'yan 'yan Siyasar yankin.

    • Gommai sun mutu a wata arangama tsakanin ISWAP da Boko Haram a Borno

      .

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, kungiyoyin sun yi arangamar ne tsakanin Dikwa da Bama

      An yi wata arangama tsakanin kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da tsagen kungiyar karkashin ISWAP, a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mai suna Kundu.

      Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno.

      Wata majiyar tsaro ta ce Kwamanda Kundu tare da tawagarsa na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan babura shida, kowanne dauke da mutum uku suka far musu.

      A baya-bayan nan dai ana yawan samun arangama da juna tsakanin kungiyoyin da a baya suka addabi al'umar kasar,

    • Shugaban Somaliya da Sakataren tsaron Amurka sun tattauna batun al-Shabab

      Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya gana da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a birnin Washington DC domin tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar ciki har da batun kungiyar 'yan tawaye ta al-Shabab da ke ayyukanta a yankin kusurwar Afirka

      A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita Hassan Sheikh Mohamud ya ce ''Na gana da Sakataren tsaron Amurka a Pentagon, a wani bangare na ziyarata zuwa Amurka. mun tattauna batun hada hannu da kokarinmu wajen ganin mun kubutar da kawunanmu daga ayyukan 'yan ta'adda da ke damun duniya, Amurka babbar kwar somaliya ce ta fannin tsaro''.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

      Ganawar na zuwa ne yayin da dakarun Somaliya da kawayensu ke kara kaimi wajen kai wa kungiyar al-Sahab hare-hare a kudanci da yankin tsakiyar kasar a kokarinsu na kwato yankunan da ke hannun kungiyar.

    • Yakin Ukraine: An gano wani babban kabarin da aka binne mutane da dama a birnin Izyum

      .

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Kabarin na birnin Izyum wanda dakarun Ukraine suka kwato daga hannun sojojin Rasha

      Ukraine ta ce tana da shaidar gano katon kabarin da ka binne mutane da dama a birnin Izyum da ke arewa maso gabshin kasar, wanda ta kwato kwanan nan daga hannun dakarun Rasha

      Shugaban 'Yan sandan yankin Volodymyr Tymoshko ya shaida wa BBC cewa ana tsammanin an binne gawarwaki fiye da 400 a cikin kabarin.

      Kawo yanzu dai ba a san dalilin mutuwar mutanen da ke cikin kabarin ba, to amma wasu na zargin cewa sun mutu ne sakamakon hare-haren bom da rashin samun magunguna.

      Ukraine da kawayenta sun sha zargin dakarun Rasha da aikata laifukan yaki, zargin da Rasha ta sha musantawa.

    • An gayyaci Sarkin Ashanti na Ghana zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth ll

      Sarkin Ashanti

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Sarkin Ashanti

      Sarkin Ashanti da ke kasar Ghana Otumfuo Osei Tutu II, ya samu gayyata zuwa jana'izar kasa da za a yi wa Sarauniyar Ingila Elizabeth ll a Westminster Abbey da ke birnin Landan ranar Litinin mai zuwa.

      Wani gidan radiyo a kasar ne ya wallafa wasikar gayyatar a shafinsa na Tuwita inda ya ce ''Mai martaba Otumfuo Osei Tutu II sarkin Ashanti, ya karbi wasikar gayyatar jana'iza daga mai martaba Sarki Charles lll, domin halartar jana'izar kasa da za a yi wa mai martaba Sarauniya Elizabeth ll''

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

      Sarki Otumfuo Osei Tutu II, dai ya hau karagar Sarauta a shekarar 1999 a matsayin sarkin Ashanti na 16.

      A shekarar 2018 Sarkin ya karbi bakuncin Sarki Charles lll a fadarsa da ke Manhiya

      .

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Sarki Charles lll a fadar Sarkin Ashanti
    • PDP ta nada Tambuwal a matsayin daraktan yakin zaben Atiku

      .

      Asalin hoton, PDP/Twitter

      Bayanan hoto, Gwamna Tambuwal

      Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar, inda ta nada gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a matsayin babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasar

      A wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce kwamitin wanda gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ke shugabanta ya kunshi wasu gwamnonin da suka hada da gwamnan Ribas Nyesom Wike wanda ke ta kiraye-kirayen shugaban jam'iyyyar na kasa ya sauka daga mukaminsa.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

      Jam'iyyar dai ta fada rikicin cikin gida ne tun bayan zaben fitar da gwani na jam'iyyar, zaben da ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar nasara, matakin da bai yi wa gwamnan jihar Ribas Nyensom Wike dadi ba.

      A makon da ya gabata ne dai Tambuwal, wanda ke shugabantar kungiyar gwamnonin jam'iyyar, da shugaban kwamitin amintatu na jam'iyyar Sanata Walid Jibrin, suka ajiye mukamansu, matakin da suka ce sun dauka domin samun masalaha a jam'iyyar.