Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Raka gawar Sarauniya ya tuna min da mutuwar mahaifiyata Diana - Yarima William

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Bappa

  1. An dage bude makarantu a Sudan saboda ambaliya

    Gwamnatin Sudan ta sanar da dage bude makarantu a fadin kasar, saboda ambaliya da ta daidaita yankuna da dama a kasar.

    Da ma a wannan watan ya kamata a fara sabon zangon karatu a kasar, to amma yanzu an dage batun komawar har sai ranar 2 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridun cikin gida suka ambato Ministan Ilimi Sir al-Khatim al-Huri yana fada.

    Akalla makarantu 623 ne ambaliyar ta shafa, kuma an dauki matakin ne da nufin gyara su kafin a cigaba da karatu.

    Ruwan sama mai karfi da ambaliya sun kashe sama da mutum 100, tare da lalata dubban gidaje a gwamman jihohin Sudan a makonnin da suka wuce.

  2. Hotuna: Dogayen layuka domin kallon akwatin gawar Sarauniya

    Bisa al'ada irin ta 'yan Birtaniya, dubban mutane sun kwana a kan layi domin su kalli akwatin gawar Sarauniya Elizabeth II.

    Da misalin karfe biyar agogon Birtaniya na yau za a bude ginin majalisar dokokin kasar domin bai wa mutane damar kallon akwatin.

    Haka lamarin zai ci gaba zuwa ranar Litinin da misalin karfe shida da rabi na asuba lokacin da za a birne Sarauniyar.

  3. Sabon shugaban Kenya na shirin cire tallafin man fetur

    A rana ta farko da ya shiga ofis, Shugaban Kenya William Ruto ya soke wasu shirye-shiryen gwamnatin wanda ya gada, wato Uhuru Kenyatta.

    Shugaba Ruto ya kuma nada alkalai shida da Hukumar kula da Ayyukan Shari'a ta tantance shekaru uku da suka wuce, wadanda Mr Kenyatta ya ki nadawa bisa zargin cewa gurbatattu ne.

    Za a rantsar da da alkalan a ranar Laraba.

    Sabon shugaban ya kuma yi kalaman da ke nuna cewa zai iya soke tallafin abinci da na man fetur.

    A cewarsa ana kashe makudan kudi kansu kuma ba a moriyarsu yadda ya kamata.

    Mr Ruto kazalika ya ce daga yanzu ba za a kara tantance kwantenoni idan ba a tashar Mombasa ba, wanda a gwamnatin baya ana aikin tantancewar a tashar Naivasha.

    Da ma matakan da Mr Ruto ya fara dauka na daga cikin alkawuran da ya dauka lokacin kamfe.

  4. Ganawa da gawar Sarauniya - abubuwan da suka kamata ku sani

    Ana sa ran dubbai za su yi dogayen layuka a London don yin ido-da-ido da gawar Sarauniya.

    Za a shimfide gawar da karfe 5:00 na Yamma a zauren Westminster ranar Laraba 14 ga watan Satumba, kuma za ta ci gaba da kasancewa a nan, har sai karfe 06:30 na safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, wato ranar da za a gudanar da jana'izar kenan.

    Ga abubuwan da suka kamata ku sani kafin fara ganawa da gawar.

    Tikiti?

    Babu tikiti, amma kuma dole ka bi layi. Kuma za a iya daukar tsawon lokaci, saboda haka sai a shirya wa hakan.

    Daga ina layin zai fara?

    A Albert Embankment, da ke bayan London Eye. Za a bai wa mutane abin daurawa a hannu da zarar sun hau layi shaidar suna kan layi. Dogon layin zai iya kai wa anguwar South Bank, watakila ma har Southwark Park.

    Bandaki?

    An samar da bandaki na wucin-gadi a wurare da dama na wadannan unguwanni.

    Kazalika wasu shaguna da dama kamar Southbank Center da Shakespeare's Globe za su kasance a bude tsawon lokacin ga masu bukata.

  5. Na yi namijin kokari a mulkina - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari, idan aka yi la'akari da dan abin da take samu wurin tafiyar da lamuran kasar.

    Shugaban ya yi kalaman ne yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke birnin Owerri ranar Talata, bayan bude wasu manyan ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma ya yi.

    Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin gudanar da ayyuka da dama duk da kudaden da take samu ba basu isa.

    ''Wannan gwamnati ta yi kokari sosai. Dole na fada saboda wadanda alhakin fadar hakan ya rataya a wuyansu ba sa yin haka. Ban san me ya sa ba,'' in ji Shugaba Buhari.

    Ya kuma jinjina wa gwamnatinsa bisa nasarar da ta samu na gurgunta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a Kudu maso Gabas, a rikicin da ya ce ya gada daga gwamnatin PDP a 2015.

    Shugaban ya kuma yi jinjina ga gwamnan jihar ta Imo kan gayyatar shi a karo na biyu cikin shekara daya don ya bude ayyukan da ya aiwatar.

  6. Masu ganin gawar Sarauniya Elizabeth II za su shafe awa 30 kan layi

    Ministar Al'adu a Birtaniya Michelle Donelan ta yi gargadin cewa za a iya samun dogayen layuka fiye da yadda aka yi tsammani don ganawa da gawar Sarauniya Elizabeth II a babban zauren Westminster.

    Ta ce akwai yiwuwar samun dogayen layuka na dubban masu ta'aziyya, da ka iya shafe awa 30 a kan layi.

    A kan haka ta gargadi al'umma da su shirya jure wa tsayuwa ta tsawon awanni a kullum, su kuma shirya jure wa yanayi.

    Sai dai ta ce ''Gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa ta tabbatar jama'ar da za su yi balaguro zuwa London ba su samu matsala ba.''

    Ms Donelan ta ce sama da mutum 1,000 ne a kullum za su kasance a inda jama'a suka yi layi don su taimaka masu.

    Ta kara da cewa kamfanonin Tate Modern da Shakespeare Globe za su haska ofisoshinsu da ke London da hoton Sarauniya Elizabeth, sannan shaguna za su raba abin sha ga jama'a.

    Bugu da kari an tanadi ban-daki guda 500 a kan hanyar da ke sa zauren na Westminster don biyan bukatar jama'a.

  7. Barkanmu da safiyar Laraba

    Jabir Mustafa Sambo ne yake muku fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Laraba, wadda Hausawa kan yi wa kirari ta bawa ranar samu.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da ake ciki game da shirye-shiryen yin jana'izar Sarauniyar Ingila Elizabeth II da ma saran labaran Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a ko da yaushe a shafukanmu na sada zumunta da muhawara a BBC Hausa.