Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Raka gawar Sarauniya ya tuna min da mutuwar mahaifiyata Diana - Yarima William

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Bappa

  1. Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi hatsarin mota

    Wani Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a Kyiv babban birnin kasar.

    A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar ya ce wata motar fasinja ce ta daki tawagar motocin da shugaban ke ciki ranar Laraba a birnin na Kyiv.

    Shugaban dai bai samu munanan raunuka ba kamar yadda likitansa ya bayyana.

    Tuni dai aka yi wa diraban motar fasinjan magani, yayin da kuma daga bisani aka dauke shi a motar daukar masara lafiya

    Hadarin ya faru ne bayan da Mista Zelensky ya ziyarci birnin Izyum da ke arewa maso gabashin kasar, wanda dakarunsa suka kwace daga hannun sojojin Rasha.

  2. Har yanzu mutane na kan layin bankwana da gawar Sarauniya

    Dogon layin da ke bankwana da gawar Saruniya na ci gaba da jira domin nuna girmamawar karshe ga gawar.

    An dai yi shiru a dakin taron yayin da mutanen ke ci gaba da zuwa wajen gawar.

    Cikin kowanne minti ashirin akan yi shiru na dan wani lokaci, yayin da ake ci gaba da sauya jami'an tsaron da ke aiki a wajen.

    Tsohuwar Firaministar Burtaniya Theresa May tare da mijinta, sun je domin nuna girmamawa ga Basarakiyar da suka dauki lokaci suna aiki tare.

  3. Barkanmu da safiyar Laraba

    Abdullahi Bello Diginza ne ke muku fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Alhamis.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da ake ciki game da shirye-shiryen yin jana'izar Sarauniyar Ingila Elizabeth II da ma saran labaran Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a ko da yaushe a shafukanmu na sada zumunta da muhawara

  4. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa da muka wuni muna kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suka faru a duniya, musamman ma batun mutuwar Sarauniya ELizabeth II.

    Sai kuma gobe Laraba inda za mu ci gaba da kawo muku labaran da suka shafe ku.

    Sunana Aisha Shariff Baffa, nake cewa sai da safe.

  5. Shugaba Biden ya yi wa Sarki Charles ta'aziyya ta waya waya

    Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi magana da Sarki Charles III a yau, in da ya masa ta'aziyya da kuma shaida masa irin yadda Amurkawa ke matukar kaunar Sarauniya.

    A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Amurka ta fitar, ta ce shugaban ya tuna da irin kirki da kuma karramawar da Sarauniya ta yi musu shi da mai dakinsa a fadar Windsor Castle a watan Yunin da ya wuce.

    Sanarwar ta ce darajar Sarauniya da mutuncinta su suka sa kawancen kasashen biyu ya yi karko har ma ya zama sanadin samar da wata dangantaka ta musamman tsakanin Burtaniya da Amurka.

    Shugaban na Amurka zai halarci jana'izar Sarauniya da za ayi a Landan ranar Litinin mai zuwa.

  6. An biya wadanda 'yan sandan SARS suka ci zarafi ko azabtar da su diyya

    Hukumar kare hakkin dan adam a Najeriya, ta biya kusan dala dubu 700 diyya ga mutanen da 'yan sanda suka azabtar da kuma ci zarafinsu.

    Wasu da ga cikin mutane 58 da aka biya diyyar iyalai ko 'yan uwan wadanda aka zabtar ne ko kuma sune da kansu.

    Hakan ya biyo bayan bincike a kan korafe-korafen da iyalan wadanda aka azabtar suka yi in da suke zargin jami'an 'yan sanda da kisan da shari'a ba ta amince da shi ba da batar da mutane ba dalili, da kame ba bisa ka'ida ba da tsare mutane na lokaci mai tsawo da kuma kwace musu kadarorinsu, musamman wanda rundunar 'yan sandan nan da ta yi kaurin suna wato SARS ta yi.

    Shugaban hukumar ya ce diyyar da aka biya hanya ce ta neman afuwa ga wadanda aka azabtar kuma gwamnati ta amince an take musu hakkokinsu.

    Ya ce kada mutane su dauka cewa kudin diyyar da aka biya za su maye gurbin azabtarwa ko kuma laifukan da aka aikata na cin zarafin mutanen, ya kara da cewa hakkin hukumar ne ta kare 'yancin al'ummar Najeriya.

    A watan Oktobar 2020 ne, irin azabtarwa da cin zarafi da kuma take hakkin dan adam din da rundunar 'yan sandan ta SARS ke yi ne suka haifar da mummunar zanga-zangar gama gari a duka fadin kasar.

  7. Hotunan yadda ake tururuwar shiga Dakin Taron Westminster don ganin gawar Sarauniya

  8. Za a sake bibiyar dokokin kiyaye teɓa saboda tsadar rayuwa a Ingila

    Gwamnatin Ingila za ta sake yi wa dokokin kiyaye teba kwaskwarima ciki har da soke tallace-tallacen abincin da ke sanya teɓa a talbijin kafin karfe 9 na dare.

    An fahimci cewa ministocin kasar sun yi amanna cewa dole a kula da yanayin tsadar rayuwar da ake ciki a yanzu.

    To amma ƙwararru a bangaren lafiya sun ce sun damu matuka a kan rahotanni da ke cewa za a soke matakan.

    Gwamnatin dai ta ce za a tsawaita dokar har zuwa nan da shekara guda, saboda mutane su saba da matakan kare tebar.

    A baya dai an sanya dokoki a wuraren abinci a game da yawa da kuma irin abincin da za a rinka siya a wajensu.

    Rahotanni sun ce za kuma a sake waiwayar dokar harajin da aka sanya a kan lemunan da ke da zaki sosai wadda a ka yiwa garanbawul a 2018.

  9. An ci tarar shugaban masu hakar ma'adinai saboda mutuwar masu hako zinare

    An samu wani daraktan masu hakar ma'adinai a Burkina Faso da laifin kisan mutane, bayan wata ambaliya da ta hallaka masu hako ma'adinai takwas a watan Afrilu.

    An ci tarar Hein Frey, mai kamfanin hako ma'adinai na Trevali mallakin kasar Canada, kudi dala 3,000 da kuma hukuncin zaman gidan yari na watanni 24.

    Mutane sun harzuka a fadin kasar bayan faruwar lamarin.

    Mutanen Burkina Faso dai na ganin hukuncin ya yi kadan ganin yawan mutanen da suka mutu.

    An kuma samu Frey, wanda ya fito daga Afirka ta Kudu da laifin hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba da kin bin sharuda na kiyaye lafiya da jefa rayukan mutane cikin hadari da kuma kin taimaka wa mutanen da ke cikin hadari.

    An fara sauraron karar ce ranar 24 ga watan Augusta bayan shigar da korafi da iyalan masu hako ma'adinan da suka mutu suka yi.

  10. Philipines ta janye haramcin hana 'yan kasar zuwa Saudiyya neman aiki

    Hukumomi a Philiphines sun dauki matakin dage haramcin da suka sanya na tura ma'aikatansu zuwa Saudiyya, bayan da Riyadh ta amince ta kare hakkin ma'aikata 'yan cirani daga Philiphines.

    Manila ta hana 'yan kasar tafiya Saudiyya domin yin aiki a watan Nuwambar bara bayan rahotannin cin zarafi da rashin biyansu hakkokinsu.

    An kiyasta cewa sama da ma'aikata 500,000 ne 'yan Philiphine ke aiki a Saudiyya kafin sanya haramcin, inda yawanci suke aiki a matsayin 'yan aiki da kuma leburorin da ke aikin gini.

    Hukumomi a Saudiyya sun canja dokoki, inda a yanzu ma'aikata daga kasashen waje za su iya barin aikinsu ko da kwantiraginsu bata kare ba muddin suna fuskantar cin zarafi.

    An kuma basu lokacin hutu da kuma inshora domin taimaka wa wadanda ba a biya su albashi ba.

  11. Mutane sun fara shiga Westminster Hall don bankwana da gawar Sarauniya Elizabeth

    An fara barin mutane su shiga Westminster Hall don ganin gawar Sarauniya Elizabeth, bayan jira na sa'o'i kadan domin yi mata bankwana.

    Za a ajiye gawar Sarauniyar har zuwa 6:30 na ranar Litinin, inda daga bisani za a yi mata jana'izar ban girma ta kasa baki daya.

  12. Masar ta saki dan jaridar Al Jazeera da ta tsare

    Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta bayyana cewa hukumomi a Masar sun saki dan jaridar ta Ahmed El-Nagdy da suka tsare.

    Wannan na zuwa ne yayin da shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah al-Sisi ke ziyara a Qatar - wurin da kafar yada labaran ke yada shirye-shiryenta.

    Haka-zalika, wannan ne kuma karon farko kenan tun bayan da kasashen biyu suka dawo da huldar dangantaka a shekara da ta wuce bayan rashin jituwa ta diflomasiyya.

    An tsare El-Nagdy tsawon shekara biyu, inda har yanzu ake ci gaba da tsare abokanan aikinsa biyu.

    Gwamnatin Masar karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Sisi ta sha kama 'yan jaridan Al Jazeera kan abin da ta kira na yada labaran da basu dace ba da take yi.

  13. Mozambique ta tsare matasa 29 saboda zarginsu da shiga kungiyoyin masu ikirarin jihadi

    'Yan sanda a Mozambique sun tsare matasa 29 saboda zarginsu da yin tafiya domin shiga kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yankin Cabo Delgado da ke arewacin kasar mai albarkatun iskar gas.

    Hukumomi sunce, matasan wadanda suka fito daga lardunan Memba da Nacala-Porto da ke makwabtaka da yankin Nampula, sun ce sun je lardin Cabo Delgado ne don kamun kifi.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Nampula, Zacarias Nacute, ya soki matasan, inda ya ce an yaudaresu da niyyar sama musu ayyuka.

    Ya ce za a mika su ga ofishin babban mai yanke hukunci na kasar domin dakar mataki na gaba.

    Mozambique na fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi a arewacin kasar tun 2017.

  14. Gawar Sarauniya ta isa zauren Westminster

    Gawar Sarauniya Elizabeth ta II ta bar fadar Buckingham zuwa babban zauren Westminster, tare da rakiyar Sarki Charles na III, da Yariman Wales, da kuma Duke na Sussex da sauran manyan 'yan gidan sarauta.

    Akwatin gawar ya isa Fadar Westminster, kuma a hankali, cikin natsuwa, masu daukar gawa sun shiga da akwatin fadar.

    Mutum takwas ne aka bai wa wannan aiki, wanda suka shafe lokaci suna gwajin yadda za su gudanar da shi.

    Akwai dandazon jama'a a harabar, da suka shafe awanni suna jiran ganin yadda za a shiga da akwatin gawar.

  15. Rikici na kara kazanta tsakanin Armenia da Azerbaijan

    Mataimakin ministan harkokin wajen Armenia Paruyr Hovhannisyan, ya ce a bayyane ta ke karara taho mu gama tsakanin sojin kasarsa da na Azerbaijan na dada muni, wanda hakan ka iya maida su filin yaki gadan gadan.

    Ma'aikatar tsaron Armenia ta ce sojojin Azerbaijan sun cigaba da luguden wuta tun da sanyin safiyar yau Laraba tsakanin iyakokin kasashen biyu.

    Tun da fari Armenia ta zargi Azerbaijan da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma shekaru biyu da suka gabata.

    Yaki ya barke tsakanin makwabtan biyu a shekarar 2020, lokacin da Azerbaijan ta mamaye kaso biyu cikin uku na yankin Nagorno-Karabakh, wanda 'yan awaren Armenia ke iko da shi tun shekarun 1990.

    A ranar Litinin rahotanni suka ce an kashe sojoji sama da 100 tsakanin kasashen biyu.

    A cewar Firanministan Armenia Nikol Pashinyan an kashe sojojinsa 49 a dare guda, yayin da ma'aikatar tsaron Azerbaijan ta ce itama ta rasa sojoji 50.

    To amma a ranar Talata Rasha ta ce ta shiga tsakani kuma an tsagaita wuta a rikicin na baya bayan nan.

  16. Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan jihar Yobe

    Kauyuka da dama, da hanyoyi da gonaki, har ma gadoji ne ambaliyar ruwa ta yi awon-gaba da su a wasu yankunan jihar Yobe da ke maso maso gabashin Najeriya.

    Wani babban jami'i a kananan bankunan bayar da rance na Jihar, Sheriff Almuhajir ne ya wallafa hotunan irin barnar da ambaliyar ta yi a shafinsa na Facebook ranar Laraba.

    Ya yi zargin cewa bala'in da suke ciki a Yobe na faruwa ne saboda ambaliya a dam din Tiga da ya fito daga Kano ya bi Hadejiya a jihar Jigawa, daga nan ya dangana da Nguru da Gashua a jihar ta Yobe.

    A cewarsa ya kamata a ce masu zuba jari a harkar noma su yi amfani da damar isasshen ruwan da ke yankin don jama'a su amfana a kuma kawar da bala'in ambaliyar.

    Yobe ta shiga sahun sauran jihohin Arewacin Najeriya da suka hada da Jigawa, da Kano, da Bauchi, da Adamawa, da ambaliya ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, da kuma rusa dubban gidaje.

  17. Kante da Mendy ba za su buga wa Chelsea gasar Zakarun Turai ba

    Golan Chelsea Edouard Mendy da dan wasan tsakiyarta N'Golo Kante ba za su buga wasan Zakarun Turai da kungiyar za ta buga da RB Salzburg ba a birnin London.

    Chelsea za ta karbi bakuncin Salsburg a Stamford Bridge, bayan rashin nasara a hannun Dynamo Zagreb, a wasan farko na rukunin E, wanda hakan ya yi sanadin sallamar tsohon kocin kungiyar Thomas Tuchel.

    Kante na fama da ciwo a cinyarsa, yayin da Mendy ke fama da ciwo a gwuiwarsa.

    Sai dai Chelsea na da isassun yan wasa da za su maye gurbin masu raunin.

    Shi ne wasa na farko da sabon kocin kungiyar Graham Potter zai jagoranta tun bayan nada shi makon da ya wuce.

    An dage wasannin gasar Premier League na makon da ya wuce saboda jimamin mutuwar Sarauniya Elizabeth ta II, wanda hakan ya kawo jinkirin ganin kamun ludayin Potter a Chelsea.

  18. Gwamnonin Arewacin Najeriya na so a kafa rundunar 'yan sandan jihohi

    Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 da sarakunan gargajiya a yankin sun yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulki na 1999, don samar da yan sandan jihohi.

    A cewarsu wannan ne kadai zai sa a shawo kan matsalar tsaro da yankin ke fama da ita dama kasa baki daya.

    Yankin Arewacin na Najeriya ya jima yana fama da matsalar yan fashin daji, da satar mutane don neman kudin fansa, da sauran nau'o'in ayyukan ta'addanci.

    Kungiyar gwamnonin arewa ta NGF, da ta sarakunan gargajiya (NTRC) sun aminta da hakan ne bayan kammala wani taro ranar Litinin a Abuja.

    Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu suka cimma matsayar samar da yan sandan jihohi a taron hadin gwuiwa.

    Sai dai akwai masu fargabar cewa wasu gwamnonin jihohin kan iya amfani da yan sandan da za a samar a karkashin ikonsu, don cin zarafin abokan adawa ko kuma cimma burinsu na siyasa.

    An dade ana kiraye-kirayen samar da yan sandan jihohi, inda masu bukatar a yi hakan ke kafa hujjar cewa rundunar yan sanda ta kasa ta yi kadan, idan aka yi la'akari da girman matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

  19. Angola da Libya sun shiga gaban Najeriya wurin samar da danyen mai – OPEC

    Adadin danyen man fetur da Najeriya ke samarwa ya yi kasa zuwa ganga 972,000 a duk rana a cikin watan Agusta, wanda hakan yasa kasashen Angola da Libya suka shiga gabanta wurin samar da danyen man a watan.

    Hakan na kunshe ne a rahoton da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) ta fitar a cikin watan Satumba.

    Wannan ne karon farko a cikin shekaru da dama, da Najeriya ta samar da ganga kasa da miliyan daya ta danyen man fetur a rana.

    Kazalika rahoton na OPEC ya ce lamarin ya sa kasashen Angola da Libya sun sauko da Najeriya wurin samar da danyen man fetur a dan tsakanin.

    Rahoton ya ce '' fitar da danyen mai ya karu a kasashen Libya da Saudi Arabia, yayin da ya ragu a Najeriya.''

  20. Sarki Charles na III ya isa Fadar Buckingham

    Sarki Charles na III ya isa Fadar Buckingham, inda ya daga hannu ga dandazon mutanen da suka jeru domin yin tozali da akwatin gawar Sarauniya.

    An wuce da Sarkin a cikin mota, kuma dan anjima zai sake fitowa inda zai yi wa akwatin gawar Sarauniya Elizabeth rakiya.

    Gawar za ta bar fadar Buckingham zuwa babban dakin taro na majalisar dokokin kasar watau Westminster, domin bai wa jama'a damar ganin akwatin gawar.