An kama mutumin da ya so ta da hargitsi a wajen raka gawar Sarauniya

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Sani Aliyu

  1. Brazil ta haramta sayar da wayoyin iPhone marasa caja

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ..

    Gwamnatin Brazil ta ce ta hana sayar da wayoyin iPhone wadanda ba su da caja a kasar.

    A wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar kasar ta fitar, ta ce ta ci tarar kamfanin wayoyin fam miliyan 2.04

    Hukumar kula da hakkin mai saye ta kasar ta ce matakin da kamfanin Apple - wanda ke kera wayoyin - ya dauka na rashin sayar da wayoyin tare da cajarsu ya ci karo da hakkin masu saya.

    To amma kamfanin na Apple ya ce zai daukaka kara game da wannan matakin.

  2. Sarki Charles lll da matarsa na gaisawa da dandanzon mutane a fadar Holyroodhouse

    .

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Sarkin ya fara ne da ziyartar majalisar dokokin Burtaniya a Landon

    Sarki Charles lll da matarsa sun isa fadar Holyroodhouse wajen da aka ajiye gawar Sarauniya.

    Ma'auratan sun gaisar da dimbin mutanen da suka taru a wajen fadar domin dakon isawarsu.

    .

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Dimbin mutanen da ke tarbar Sarki a wajen fadar Holyroodhouse
  3. Sarki Charles lll ya isa birnin Edinburgh

    .

    Asalin hoton, BBC.

    Bayanan hoto, Sarki Charles lll tare da matarsa sun taso ne gada birnin Landan

    Sarki Charles lll tare da matarsa Camilla sun sauka a filin jirgin saman birnin Edinburgh da ke yankin Scotland.

    A yanzu ma'auratan za su nufi fadar Holyroodhouse da ke birnin inda dubban jami'an tsaro sanye da kayan sarki ke kiran isowarsa.

  4. Za a dawo da harkokin wasanni a Ingila ranar Talata

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A karshen mako ne dai aka dakatar da harkokin wasannin saboda rasuwar Sarauniya

    A gobe Talata ne za a dawo da wasannin gasar kasar Ingila, bayan da aka dakatar da harkokin wasanni saboda alhinin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.

    To sai dai za a yi shiru na minti daya a cikin filin tare da karanta taken kasa, gabanin fara wasa domin nuna alhini ga rasuwar Sarauniya.

    Haka kuma 'yan wasa za su daura bakin kambu, tare da sauko da tuta kasa-kasa

    A karshen makon da ya kabata ne dai aka dakatar da harkokin wasanni a kasashen Ingila da Wales, da Scotland da kuma Ireland ta arewa, sakamakon rasuwar sarauniya Elizabeth II.

  5. Ma'aitakan filayen jiragen sama na yajin aiki a Najeriya

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, .

    Kungiyar Ma'aikatan filayen jiragen sama ta Najeriya sun rufe filin jirgin sama na Malam Aminua Kano da ke kano sakamakon yajin aikin da uwar kungiyar ta kasa ta fara gudanarwa a yau.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an soke tashin wasu jiragen da aka tsara tashinsu daga filin jirgin da safiyara yau Litinin

    Wani jami'in Filin jirgin ya ce an soke tashin jirgin AZMAN zuwa Abuja da na Max Air zuwa Legas, bayan da fasinjoji suka riga suka shiga jiragen.

    Yajin aikin na zuwa ne sakamakon sabani da aka samu tsakanin hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasar da hukumar kula da sararin samaniya ta kasar kan wasu batutuwa

  6. Tanzaniya ta gargadi masu goyon bayan 'yan luwadi da madigo

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, .

    Gwamnatin Tanzaniya ta gargadi mutanen da ke yada bidiyoyin masu nuna goyon bayan 'yan luwadi da madigo a shafukan sada zumunta.

    Haka kuma gwamnatin ta yi barazanar daukar matakai kan masu kula da shafukan da ke yada irin wadannan bidiyoyi

    Ministan yada labaran kasar Nape Nnauye ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen wani taron kafafen yada labaran kasar da aka gudanar a Dar es Salaam babban birnin kasar.

    Mista Nnauye ya ce mutanen na amfani da kayan wasan yara domin nuna goyon bayansu ga masu auren jinsi daya.

    Ya kuma kara da cewa gwamnati ba za ta lamunci wannan dabi'a da ta ci karo da al'adun mutanen Tanzaniya ba.

    Auren jinsi dai babban laifi ne a Tanzaniya, abin da ya tilasta wa 'yan luwadi da madigo da masu sauya jinsi boye kawunansu a kasar.

  7. Sarki Charles lll ya nufi Edinburgh daga Westminster

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Sarkin da matarsa za su hau jirgin samu zuwa Edinburgh

    Jim kadan bayan kammala jawabinsa a gaban majalisar dokokin Birtaniya, Sarki Charles lll tare da mai dakinsa Camilla, sun bar dakin taro na Westminster

    Ma'auratan za su hau jirgin samu zuwa Edinburgh, inda Sarkin zai yi wa gawar Sarauniya rakiya daga fadar Holyroodhouse zuwa majami'ar St Giles.

    Sarkin zai kuma gana da shugaban gwamnatin Scotland Nicola Sturgeon, sannan kuma zai kai ziyara majalisar dokokin kasar domin karbar gaisuwar ta;'aziiya daga 'yan majalisar.

  8. Sarki charles lll ya mayar da jawabi ga 'yan majalisar dokokin Birtaniya

    .
    Bayanan hoto, Sarki Charles lll ya ce ya yi matukar godiya game da jawaban da 'yan majalisar suka gabatar masa

    Sarki Charles lll ya mayar da jawabi game da ta'aziyyar da shugabannin majalisun dokokin Birtaniya suka yi masa kan rasuwar sarauniya Elizabeth ll

    Sarkin ya ce ya yi matukar godiya game da jawaban alhini da ta'aziyar da ya samu daga 'yan majalisar wanda ya ce masu sosa zuciya ne.

  9. Kakakin majalisar wakilai ya mika ta'aziyya ga Sarki Charles

    Shi ma Kakakin majalisar wakilan Birtaniya Sir Lindsay Hoyle, ya mika ta'aziyya a madadin sauran takwarorinsa 'yan majalisar wakilan ga Sarki Charles lll

    .
    Bayanan hoto, kakakin majalisar wakilan Birtaniya Sir Lindsay Hoyle
  10. Shugaban majalisar dattawa na gabatar da jawabi

    .
    Bayanan hoto, Shugaban majalisar dattawa Lord McFall yayin mika ta'aziyya ga sarki charles llll

    Shugaban majalisar dattawan Birtaniya Lord McFall na gabatar da jawabin ta'aziyya ga Sarki Charles lll a madadin sauran 'yan majalisar dattawan kasar.

  11. Sarki Charles lll ya hallara a dakin taro na Westminster

    Sarki Charles lll tare da matarsa Camilla sun hallara a harabar dakin taro na Westminster.

    Inda a nan ne 'yan majalisar dokokin za su mika sakon ta'aziyyarsu ga sabon sarkin kan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ll.

    Sarki charles
    Bayanan hoto, Sarki Charles lll tare da matarsa Camilla

    A gefe guda kuma sojoji sun shirya yi masa faretin ban girma

    .
    Bayanan hoto, Sojoji na dakon isowarsa domin yi masa faretin ban girma
    .
    Bayanan hoto, Sojoji na dakon isowar sabon sarki
    .
    Bayanan hoto, Sojoji sanye da kayan sarki na musamman
  12. An samu bullar cutur kyandar biri a jihohin Najeriya 30 a wannan shekara

    Hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce a wannan shekara an tabbatar da bullar cutar Kyandar biri a fadin jihohin kasar 30.

    A wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita, hukumar ta ce rahotonta game da cutar ya nuna cewa daga ranar daya ga watan Janairu zuwa 28 ga Agustan wannan shekara, an tabbatar da bullar cutar a kan mutum 277, tare da mutuwar mutum shida.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Majalisar dokokin Birtaniya na dakon isowar sabon Sarki Charles lll

    Daruruwan 'yan majalisun dokokin Birtaniya sun shirya tsaf, domin tarbar sabon Sarki wanda zai zo majalisar domin karbar gaisuwar ta'aziyya daga 'yan majalisar

    .
    Bayanan hoto, .
    .
    Bayanan hoto, .
    .
    Bayanan hoto, .
  14. Sarki Charles lll zai kai ziyararsa ta farko majalisar dokokin Birtaniya

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, .

    A yau ne Sarki Charles III, zai ziyarci dakin taro na Westminster Hall da ke majalisar dokokin Birtaniya a ziyararsa ta farko tun bayan zamansa sabon Sarkin Birtaniya.

    Sarkin tare da Matarsa Camilla, za su saurari jawaban ta'aziyya daga shugaban majalisar dattawa Lord McFall da kakakin majalisar wakilai Sir Lindsay Hoyle a madadin sauran 'yan majalisun, daga nan kuma sarkin zai yi nasa jawabin.

    A wannan dakin taro ne kuma za a ajiye gawar Sarauniyar domin bai wa mutane damar nuna girmamawa a gareta.

  15. Yadda Sarki Charles lll zai ci gaba da mutunta Musulunci

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, .

    Fiye da musulmai miliyan uku ne ke zaune a Birtaniya, akwai kuma wasu masu yawa a kasashen da ke karkashin mulkin Birtaniya.

    Duk da cewa a al’adance wanda ke mulkin Birtaniya shi ne shugaban Cocin Ingila, Sarauniya ta yi fice wajen shiga al’amuran da suka shafi al’umar musulman Birtaniya.

    Ita ce Basarakiya ta farko da ya taba zuwa Masallaci a Birtaniya a cewar Zara Mohammed babbar Sakatariyar kungiyar musulmin Birtaniya.

    Ta kuma shaida wa kafar yada labarai ta R4 Sunday cewa ‘’Mu al’umar musulman Birtaniya muna tuna yadda Sarauniya ta sadaukar da rayuwarta wajen hidimta wa al’uma tare da hada kan mutanen Birtaniya’’

    Wannan hali ne ke a ran Sabon sarki Charles III zai dora daga inda ta tsaya.

    Sarkin ya dade yana shiga tattaunawa tsakanin addinai daban-daban. A wani jawabi da ya gabatar a shekarar 1993 ya ce ya yi imanin cewa hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci duniya zai taimaka matuka wajen zaman lafiyar al’umar duniya.

    Babban masallacin Cambridge ya ce sarkin ya karanta harshen Larabci domin samun damar fahimtar Alqur’ani

    Ben Judah na kungiyar Atlantic Council, ya ce sarkin kan yi jawabi a duk shekara domin taya al’umar musulmai zagayowar bukukuwan salla haka kuma shi ne uba ga cibiyar Nazarin addinin Musulunci ta Oxford kuma yana yawan yin magana game da koyarwar musulunci.

  16. Maraba

    Masu bibiyarmu a wannan shifi barkanmu da Safiyar ranar Litinin, inda a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa game da rasuwar Sarauniya, da wasu abubuwan a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci

    Mun gode