Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kama mutumin da ya so ta da hargitsi a wajen raka gawar Sarauniya

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Sani Aliyu

  1. Tammat!

    A madadin sauran abokan aikina da suka kasance tare da ku a wannan shafin, ni Sani Aliyu ke muku fatan alheri. SAboda haka zan mika ku ga abokan aikina wadanda za su ci gaba da aikin sanar da ku dukkan muhimman abubuwan da ke aukuwa a fadin duniya.

    Sai dai kafin in tafi, ga wannan:

    Ko kun san cewa Sarauniya Elizabeth ba ta bukatar fasfo domin ta ziyarci duk kasar da ta ke so?

    Ganin cewa Sarki Charles III ne ke kan karagar sarautar Birtaniya, shi ma ba zai bukaci fasfo ba kamar mahaifiyarsa ke nan.

    Idan ya isa kasar da yake so, sai kawai ya bayyana sunansa da sauran bayanai kamar adireshinsa da shekaruns ana haihuwa ga jami'an shige da fice na kasar da ya ziyarta.

  2. Daga birnin Edinburgh ina kuma aka dosa?

    Bayan zaman da Sarki Charles III da 'yan uwansa uku suka yi a cocin St Giles da ke Edinburgh, akwai sauran abu guda da ya rage da za a yi ranar Talata.

    Da misaloin karfe 5 na yammacin Talatar, za a dauki gawar Sarauniyar daga cocin zuwa filin jirgin saman Edinburgh, wurin da za a saka ta cikin wani jirgin sama wanda zai kai gawar zuwa filin jirgin sam na sojojin sama mai suna RAF Northolt da ke yamma da birnin Landan da karfe 6 na yamma.

    'Yar Sarauniyar wato Gimbiya Anne ce za ta raka gawar - kamar yadda ta rika yi tun da aka dauko ta daga Fadar Balmoral da ke Scotland.

    Ana sa ran gawar ta isa cikin birnin Landan da karfe 7 na dare, kuma daga nan za a wuce da ita kai tsaye zuwa Fadar Buckingham, wurin da da Sarki Charles III da matarsa Camila za su tarbi gawar.

    Ana kuma sa ran Sarkin da matarsa za su ci gaba da kai ziyara zuwa yankunan Birtaniya, inda za su tafi Belfast, wurin da Sarkin zai gana da sakataren arewacin Ireland da sauran shugabannin jam'iyyun siyasar yankin.

    Bayan ya gana da jagororin addinai, Sarkin da matarsa za su halarci wani taron yin addu'o'i a cocin St Anne kafin daga baya ya koma birnin Landan.

  3. Kasar da ta fi yawan 'yan majalisa mata a Afirka ta Yamma

    A kasar Senegal, a yanzu, mata ne ke rike da kashi 44 na kujerun sabbin 'yan majalisar dokoki da aka zaba.

    Bayan zabuka da aka gudanar a watan Yuli, mata ne ke rike da kujerun 'yan majalisa 73 cikin kujeru 165, wanda shi ne kaso mafi yawa a dukkan kasashe da ke yankin.

    A fadin Afirka ta yamma, alkaluma mata 'yan majalisa ya bambanta; alal misali a Najeriya, mata na da kashi 4 na kujeru a majalisar kasar, yayin da makwabtanta Niger kuma ke da kashi 26 na mata a majalisar dokokin kasar.

    Senegal na mataki na hudu a Afirka sannan na 18 a duniya na 'yan majalisa mata, inda take gaban Switzerland da Faransa da Birtaniya da Amurka, a cewar hukumar 'yan majalisar dokoki na kasashe da ke Geneva.

    Wani doka da aka kafa a 2010 da ke son kawo ''daidaiton jinsi'' a dukkan hukumomi, shi ne ya sanya kasar baiwa mata yawan kaso na mukamai a ofisoshi.

    A cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, bayan Senegal, 'yan majalisa 15 ne kadai mata cikin 111 da aka baiwa mukamai ko kujerun ministoci a Afirka ta Yamma da yankin sahel tsakanin watan Disamba zuwa Yuni.

    Ga kaso na mata 'yan majalisa da mata ke rike da shi a majalisun dokokin kasashen Afirka ta Yamma

    • Benin kashi 8
    • Burkina Faso kashi 20
    • Cape Verde kashi 39
    • Côte D'Ivoire kashi 14
    • Gambia kashi 9
    • Ghana kashi 15
    • Guinea kashi 30
    • Guinea-Bissau kashi 14
    • Liberia kashi 11
    • Mali kashi 27
    • Mauritania kashi 20
    • Niger kashi 26
    • Nigeria kashi 4
    • Senegal kashi 44
    • Sierra Leone kashi 12
    • Togo kashi 19
  4. Duka 'ya'yan Sarauniya sun isa wurin da aka ajiye akwatin gawarta

    Kamar yadda mua shaida muku dazu, 'ya'yan Sarauniya Elizabeth su hudu sun isa cocin St Giles domin yi ma mahaifiyar tasu addu'o'i.

    Sarkin Charles III da kanwarsa Gimbiya Anne da kaninsa Yarima Andrea da kaninsa Yarima Edward sun tsaya kusa da akwatin na wani takaitaccen lokaci.

    Wannan ne karon farko da mace ta taba halartar irin wannan hidimar ibadar, yayin da Gimbiya Anne ta isa wurin tare da Ssabon Sarki Charles III da sauran 'yan uwan nata biyu.

  5. Kalli hotunan yadda 'yan Edinburgh ke shiga kallon akwatin gawar Sarauniya

    Al'ummar birnin Edinburgh na ci gaba da turuwa zuwa cocin St Giles da aka ajiye gawar Sarauniya Elizabeth II.

    An rika raba wa jama'ar da ke kan dogon layi wasu robobin da za su daura a hannayensu a matsayin alamar wadanda aka tantance, gabanin a bar su su kafa layin da ya bi ta cikin Jami'ar Edinburgh kafin su kai ga cocin na St Giles.

  6. Mutum miliyan bakwai ke rayuwa cikin bautar zamani a Afirka, Daga Grace Kuria BBC News, She Word, Nairobi

    An yi ƙiyasin cewa akwai a ƙalla ƴan Afirka miliyan bakwai da ke rayuwa cikin bautar zamani, inda ta zama nahiya ta biyu bayan Asiya da Pacific, kamar yadda wani sabon rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya gano.

    Matsin tattalin arziki da annobar cutar korona ta jawo, da rikice-rikicen masu tayar da ƙayar baya da sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da suka jawo hakan.

    A shekarar 2016, mutum miliyan 40 ne a faɗin duniya ke rayuwa cikin bautar zamani inda lamarin ya fi shafar mata da yara.

    MDD ta ce a yanzu yawan mutanen ya kai miliyan 50.

    Rahoton ya bayar da shawarwari kamar haka:

    • A kara tare da ƙaƙaba dokoki na sa ido a kan harkar ƙwadago
    • A kawo ƙarshen tursasa yin ƙadago da ƙasashe ke yi
    • A ƙarfafa bayar da kariya a shari’ance
  7. An fara ba jama'a damar ganin akwatin gawar Sarauniya

    Wannan ne lokacin da wasu mazauna birnin Edinburgh suka shafe wannan yinin suna jira - wato damar ganin akwatin gawar Sarauniya domin su bayyana ta'aziyyarsu.

    Masu nakasar kafa da ke amdfani da kujerun guragu aka fara ba damar shiga cocin da aka ajiye gawar, wadda aka lullube da tutar masarautar BIrtaniya.

    Tun karfe 7 na safe wasu mutanen ke bisa layi domin su sami damar zama na farko-farkon wadanda za su shiga inda aka ajiye akwatin gawar.

    Wasu sojojin da ke bayar da tsaro ga Sarkin Ingila ne ke kula da akwatin gawar - kuma ana sa ran da yammacin yau sabon Sarki Charles III zai isa cocin domin yi ma ta addu'a.

  8. Sarki Charles III ya isa majalisar Scotland a karon farko

    Ayyukan da ke gaban Sarki Charles III sai karuwa suke yi, inda a halin yanzu ya isa majalisar kasar Scotland, wurin da majalaisar za ta gabatar da wani kuduri na ta'aziyyar mutuwar Sarauniyar Elizabeth II.

    Sarkin ya isa majalisar ne tare da matarsa Camilla.

    Wannan kudurin zai ba 'yan majalisar damar bayyana yadda suke kallon rayuwar da Sarauniyar ta gudana, da sadaukarwar da ta yi da kuma yadda ta shaku da al'ummar Scotland ana tsawon zamani.

    Ana sa ran Sarki zai yi jawabin godiya bayan 'yan majalisar sun kammala jawabin nasu.

  9. 'Mazauna ƙauyuka za su ci ga da fuskantar bala'in ambaliya'

    Jami'ai a Pakistan sun yi gargadin ƙarin mazauna kauyuka za su ci gaba da fuskantar matsala sakamakon tumbatsar babbar madatsar ruwan kasar ke kara yi.

    Tuni hukumomin suka samar da wata hanyar da ruwan zai dinga bi da ta ratsa ta tafkin Manchar.

    Wakilin BBC ya ce ana fargabar ka da ambaliyar ta shiga cibiyar wutar lantarkin da ke rabawa gundumomi shida wuta, ciki har da Dadu, wadda miliyoyin mutane suka dogara da ita.

    Mamakon ruwan saman da ake fuskanta ya janyo mummunar ambaliyar ruwa a Pakistan, kusan mutane 1400 ne suka mutu, yayin da gonaki da gidaje har da asibitoci musamman na yankunan karkara suka ruguje.

  10. An kama mutumin da ya so ta da hargitsi a wajen tattakin raka gawar Sarauniya

    An kama wani mutum a yayin da ake tattakin yi wa gawar Sarauniyar Ingila rakiya a kan titin Royal Mile, a yau da rana, kamar yadda ƴan sanda suka sanar.

    Wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar ta ce: "An kama wani mutum mai shekara 22 da hannu a son tayar da hargitsi a titin Royal Mile da misalin ƙarfe 2.50 na rana."

  11. Iyalan Sarauniya sun bar Majami'a bayan kammala taron addu'o'i

    An kawo karshen taron addu'o'in da aka yi wa gawar Sarauniya a majami'ar St Giles’ da ke birnin Edinburgh.

    Gawar Sarauniyar za ta kasance a majami'ar zuwa gobe inda za a wuce da ita zuwa birnin Landan.

    Sarki Charles lll tare da sauran iyalan gidan Sarauniyar sun bar majami'ar.

  12. An kama gungun masu halasta kuɗin haram na $1bn a Saudiyya

    Mai shigar da ƙara a Saudiyya ya gano makudan kudin da suka kai sama da dala biliyan daya daga wasu gungu da ake zargi da halasta kudin haram.

    Wani jami'i a ofishin mai shigar da ƙara, ya ce za a yankewa duk ɗan kasar da aka samu cikin mutanen ɗaurin shekara 10 a gidan kaso.

    Su kuma sauran mutum biyar ɗin da ba a fadi kasar da suka fito daga Gabas ta Tsakiya ba, aka haramta musu shiga Saudiyya da kuma daurin shekaru.

    Laifin da suka aikata sun haɗa da tura kuɗaɗen da aka yi safararsu, da zuba jari a harkar gidaje da kudaden da akai damfararsu.

  13. Ana karanta wa gawar Sarauniya taken kasa

    Bayan kwashe kusan sa'a daya ana yi wa gawar sarauniya addu'o'i a majami'ar St Giles.

    An kammala taron da yi wa gawar taken kasa domin girmamawa

  14. An dora Kambin sarautar Scotland kan gawar Sarauniya

    An dora Kambin sarautar scotlan kan gawar Sarauniyar a majami'ar St Giles' da ke Edinburgh.

    A tarihi akan yi amfani da kambin wajen nuna mulki da iko a wuraren bukukuwan al'ada a kasar.

    Duke na Hamilton ne ya dora kambin kan gawar, kuma zai ci gaba da kasancewa a kan gawar har lokacin da mutane za su kammala zuwa domin nuna girmamawa ga gawar.

    Ana tsammanin tarin mutane za su halarci majami'ar domin nuna alhinisu ga mutawarta.

  15. Gawar Sarauniya ta isa Majami'ar St Giles

    Gawar Sarauniya ta isa waje na karshe a yankin Scotland wato Majami'ar St Giles, za ta kasance a nan zuwa gobe inda za a wuce da ita zuwa birnin Landan.

    Kafin nan ana sa ran yi mata addu'o'i na tsawon sa'a daya, sannan a bai wa mutane damar shiga domin yin bankwanan karshe da gawar.

  16. Hotunan 'ya'yan Sarauniya da ke yi gawarta rakiya

  17. Al'umar Edinburgh na yi wa Sarauniya bankwana bayan shekara 70

    Lokaci na farko da Sarauniyar ta ziyarci yankin Scotland a matsayin Sarki shi ne a shekarar 1953, lokacin da al'umar birnin Edinburgh suka fito kwansu da kwarkwata domin taryen Sarauniyar.

    To sai dai shekara 70 bayan fitowa taryen Sarauniyar, a ma al'umar birnin sun fito kan titunan birnin domin yi mata bankwana ta karshe, a yayin da ake wucewa da gawarta zuwa majami'ar St' Giles

  18. An fito da gawar Sarauniya zuwa majami'a

    An fara tafiya da gawar Elizabeth ll zuwa majami'ar St Giles, yayin da Sarki Charles lll ke yi wa gawar mahaifiyar tasa rakiya zuwa majami'ar.

    Duka 'yay'an sarauniyar hudu na cikin tawagar domin yi wa gawar mahaifiyar tasu rakiya.

    Idan suka isa majami'ar za a shigar da gawar domin yi mata addu'o'i na tsawon sa'a daya

    Daga nan za a bai wa mutane damar shiga domin nuna alhini da girmamawa gareta

  19. Dandazon mutane a Edinburgh na jiran fitowar gawar Sarauniya zuwa majami'ar St Giles

    Dandazon mutane a titin Royal Mile na Edinburgh na jiran fitowar gawar Sarauniya zuwa majami'ar St Giles

  20. Waɗannan ne firaiministoci 15 da Sarauniya Elizabeth II ta yi zamani da su