Fiye da musulmai miliyan uku ne ke zaune a Birtaniya, akwai kuma wasu masu yawa a kasashen da ke karkashin mulkin Birtaniya.
Duk da cewa a al’adance wanda ke mulkin Birtaniya shi ne shugaban Cocin Ingila, Sarauniya ta yi fice wajen shiga al’amuran da suka shafi al’umar musulman Birtaniya.
Ita ce Basarakiya ta farko da ya taba zuwa Masallaci a Birtaniya a cewar Zara Mohammed babbar Sakatariyar kungiyar musulmin Birtaniya.
Ta kuma shaida wa kafar yada labarai ta R4 Sunday cewa ‘’Mu al’umar musulman Birtaniya muna tuna yadda Sarauniya ta sadaukar da rayuwarta wajen hidimta wa al’uma tare da hada kan mutanen Birtaniya’’
Wannan hali ne ke a ran Sabon sarki Charles III zai dora daga inda ta tsaya.
Sarkin ya dade yana shiga tattaunawa tsakanin addinai daban-daban. A wani jawabi da ya gabatar a shekarar 1993 ya ce ya yi imanin cewa hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci duniya zai taimaka matuka wajen zaman lafiyar al’umar duniya.
Babban masallacin Cambridge ya ce sarkin ya karanta harshen Larabci domin samun damar fahimtar Alqur’ani
Ben Judah na kungiyar Atlantic Council, ya ce sarkin kan yi jawabi a duk shekara domin taya al’umar musulmai zagayowar bukukuwan salla haka kuma shi ne uba ga cibiyar Nazarin addinin Musulunci ta Oxford kuma yana yawan yin magana game da koyarwar musulunci.