Gwamnatin jihar Benue ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran da ke faruwa a Najeriya da yammacin Afirka har ma da sauran sassan duniya baki daya.

Rahoto kai-tsaye

Bello Habeeb Galadanchi

  1. An yi gargadi kan zaman dar-dar a Taiwan

    Taiwan map

    Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar Asia da Pacific sun yi gargadin cewar zaman dar-dar da ke ruruwa game da Taiwan ka iya haifar da tashin hankali na zahiri a yankin.

    Wata sanarwa da kungiyar kasashen yankin ta fitar ta bukaci da a yi taka-tsan-tsan tare da guje ma duk wani abu da zai haifar da tayar da jijiyar wuya.

    Ta kara da cewa abubuwan da ke faruwa yanzu haka ka iya haifar da kura-kurai, da fito-na-fiton da zai iya gwara kan manyan kasashen duniya.

  2. China ta soma atisayin soji bayan ziyarar Pelosi Taiwan

    China military

    Asalin hoton, Getty Images

    China ta fara wani gagarumin atisayen soji, ta ruwa da ta sama a tekun da ke zagayen Taiwan a matsayin martani kan ziyarar da shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai a tsibirin.

    Atisayen dai zai wakana ne a kan wasu daga cikin hanyoyin jiragen ruwa mafi hada-hada a duniya, kuma zai kunshi yin amfani da makaman yaki na ainihi.

    Akwai rahotanni daga ma'aikatar tsaro ta Taiwan da ke cewar sun tsinkayi jirage marasa matuka cikin dare a kusa da tsibirin, wani abu da dama ake sa ran zai faru.

    Bayanan da kasar ta China ta fitar sun nuna cewa wasu jerin atisayen za su gudana ne a kimanin mil 12 daga bakin gabar tsibirin na Taiwan.

    China dai ta nuna matukar bacin ranta kan ziyarar da Ms Pelosi ta kai domin nuna goyon baya ga mulkin gashin-kai na tsibirin wanda China ke dauka a matsayin mallakinta.

  3. Barka da asuba

    Buredi da gasashen nama

    Masu bin mu a wannan shafin na BBC Hausa da fatan kun tashi lafiya.

    Yaya aka ji da ruwan sama?

    Ku biyo mu a wannan shafin kai tsaye domin karanta labarai daga lungu lungu da saƙo na duk fadin duniya.

    Tambayar farko ita ce da me kuka yi karin kumallo?

    Bello Habeeb Galadanchi ne zai ja ragamar shafin.