Buhari ya tafi Daura domin yin hutun Babbar Sallah

Wannan shafi ne da zai rika kawo muku labarai kai-tseye daga Najeriya da filin Arfah a Saudiyya ma sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Ban fara komai ba wajen kai wa Ukraine hari – Putin

    Shugaba Putin

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya shaida wa shugabannin majalisar dokokinsa cewa bai fara komai ba wajen kai wa Ukraine hari.

    Da yake jawabi daga jihar Duma, Mr Putin ya yi wa kasashen yamma shagube da cewa idan har zasu iya to su yi nasara a kansa a fagen daga.

    Mr Putin ke nan ke cewa mun ji suna cewa suna son samun nasara akanmu a fagen daga, to ga fili ga mai doki nan sai su gwada mu gani.

    A Ukraine, dakarun Rasha na ci gaba da dannawa yankin gabashin Donetsk, bayan sun kwace birni na karshe a Luhansk.

    Rahotanni dai sun ce gwamnatin Ukraine tayi watsi da kalaman Putin tana mai cewa itama na ta dakarun na nasu kokarin.

  2. Boris Johnson na kara shan matsin lamba

    Boris Johnson

    Asalin hoton, ge

    Ana kara matsawa fira ministan Birtaniya Boris Johnson lamba a kan ya yi murabus, a inda manyan 'yan siyasar kasar ke cewa idan har aka ja kafa a kan hakan to komai na iya tsayawa.

    Bayan murabus mai yawa da aka samu daga gwamnatin Mr Johnson, a yanzu ya sauka daga shugabancin jam'iyyarsa, to amma ya ce zai ci gaba da kasancewa fira minista har sai an zabi wanda zai gaje shi.

    Sannan ya kuma yi alkawarin cewa ba zai yi amfani da sauran lokacin da ya rage masa ba wajen gudanar da manyan sauye sauye.

    Tsohon fira ministan Birtaniya, John Major, ya yi kira ga Mr Johnson da yi maza ya yi murabus, yana mai cewa bai kamata ya ci gaba da mulki a irin wannan yanayi ba.

  3. Maraba

    Masu bin mu a wannan shafi na BBCHausa barkanmu da safiya, ku biyo mu a yinin yau domin karanta labarai da rahotonni na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da filin Arfa na kasar Sadiyya da ma sauran sassan duniya.

    Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wannan shafi, haka kuma za ku iya ziyarta shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin bayyana ra'ayoyinku

    Mata na addu'a a filin Arfa

    Asalin hoton, Getty Images